← Book details Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 127 OF 205

Sashe 127

Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

da batun Tk, kamata ya yi ka sake ri e shi hannu biyu ba ka daina kula shi ba. Shi ne ya ceci Ashiq inka, ka daina jin haushinsa don Allah." Ya sauke numfashi yan kallonta, ta yi murmushi ta ce, "duk da fushi ka ke yi dani a cikin kwanakin, baka iya barina da yunwa, sai ka tabbatar naci abinci, in baka siyo ba sai ka dafa min. In na ci abincin sai ka tabbatar na sha magani ka ke bari nayi bacci. Ina jinka in ina bacci kana ta ani dan ka tabbatar lafiya nake. Iya wannan ya isa ya tabbatar min da mahimmacina a rayuwarka." Ya yi murmushi ya ce, "ni ba fushi nake dake ba, kece ki ke fushi dani har ki ke jin tsorona, shiyasa na baki lokaci ki dawo nutsuwarki ba dan kin yi laifi ba. Ta ya zan yi fushi dake bayan ni ne mai laifi? Ina da son ayi min adalci a rayuwata, shiyasa nake yiwa kowa adalci, in nayi fushi dake ban yi miki adalci ba." Ta zuba masa ido bata ce komai ba, shima kallon ta yake yi kamar zai ha iye ta saboda aunarta da tausayinta da yake ji. Muryarsa ya kai can asa yana shafa fuskarta ya ce, "na saka ki kuka ko, Ashiq ina?." Ta shagwa e fuska cikin muryar shagwa a ta ce, "shiyasa na ce ni bana so kana komawa Tiger, nafi son Rouhiina" ta fa a tana karya murya. Yayi murmushin da yake kashe mata jiki ya ce, "Tiger ya tafi, amma zai dawo wani lokaci. Kafin ya dawo ga Rouhinki ki yi abinda ki ke so, Jiddana!" Ya fa a yana lumshe ido kamar mai jin bacci." Kafin ta yi magana ya ce, "Na yi kewarki Jidda!" Ya fa a a kunnenta cikin kasalalliyar murya. Ta kalle shi ta ce, "Nima nayi kewar ka Rouhii." Ya antar da ido ya ce, "Ki nuna min, ki saka aljanun wannan dare su tashi" ya fa a da salon da ya bata dariya har ta fara kissing insa cikin kewa da soyayya. an zame kansa ya yi ya ce, "baki da lafiya Jidda, kar na wahalar dake." "Ni haka na ce maka bani da lafiya?." "Ni na san babu." Ta kalli idanunsa ta ce, "Ni lafiyata alau" ta arasa fa a cikin salon da ya saka shi lumshe ido yana bu ewa akan fuskarta. Ya matso da fuskarsa kusa da ta ta ya ce, "ciwon ki fa, babu matsala?." Bata ce komai ba saboda yadda yake bin wuyanta da hancinsa yana sauke mata numfashi mai zafi hannunta yana cikin gashin kansa. Kissing wuyanta ya yi ba tare da ya ago ba ya ce, "Ashiq!." Nayla da yar ta iya bu e baki ta ce, "Uhum." "Bani da kuzari mai yawa, zaki taimaka min?." Ta bu e idanunta ya kalle ta da ido ya aga mata gira tare da ha e bakinsa da nata cikin tsananin kewa da soyayya. KRB3P076 Nana haleema #Thebeginingofsuccess! Haka suka cigaba da zama cikin soyayya da aunar juna, abinda ya faru ya saka Omar ya ara ninka kulawar da yake bata. Ko fita ya yi baya jimawa zai dawo, in kuma ya kira wayarta aka yi rashin sa a bata auka ba lokaci aya sai hankalinsa ya tashi ya dawo gidan. Baya iya bari ta fita ita ka ai, duk inda zata je sai ta jira ya kaita in ba haka ba sai dai a fasa. Ya shiga damuwa akan abinda ya faru, shiyasa yake kiyaye duk wata hanya da za a sake cutar da ita. Da yake abin bai baza duniya kamar wancan lokacin ba ba kowa ne ya san ya faru ba. Cikin ikon Allah babu abinda ya sake faruwa, tun yana jin fargaba har ya daina ya sake suka cigaba da rayuwarsu. Wannan sabuwar kulawar da yake bata sai ta sake zama ar gata a wajansa, kulawa yake nuna mata zalla wacce babu sirki a ciki. Ko sau aya ka je gidan zaka tabbatar da irin aunar da Omar yake nunawa Nayla, baya iya oyewa ko ka an, ko yaushe cikin fa a mata sirrin zuciyarsa yake baya iya yin shiru. angaren kasuwancinsa sai dai ace alhamdulillah, ku i ne suke shigo masa ta ko ina kuma suna fita. Harka ta bu e ta ko ina, dan zuwa lokacin ya siyi bus da machine na kai kaya, sannan yaransa uku duk ya siya musu machine na hawa. Babu wanda yake aiki a ashinsa baya jin da in zama dashi, sai dai yana da fa a wanda duk yaransa sun saba da fa ansa, in yana yi ma wani lokacin basu cika damuwa ba saboda sabo, amma kyautatawa kam yana yi sosai. Naira biyar in ta shiga account insa sai Nayla ta sani, baya iya oye mata samunsa haka in asara aka yi itama zata sani. Duk ribar da za a samu da abinda zai siyawa Didi da Marmerh, ya canjawa Didi waya da sauran kayan amfani musamman a angaren sana'arta. Marmerh kuwa ko shi ya haife ta sai haka, duk abinda zai samu sai ya siyawa Marmher wani abu, kayan wasa kuwa kamar banza haka yake siya ya kai. Nayla kuwa abin ba a cewa komai, siyayyar kayan sakawa da tarkace kayan kwaliyya haka zai kawo Nayla. Wani lokacin ya kan rasa me zai siya mata saboda sai ya ga komai tana dashi, shiyasa ya fi mayar da hankali a siya mata kayan ado tunda ya ga tana so. Omar ya sake yin haske saboda zaman da ku i suke a hannunsa, ya sake zama mai class na arshe, magana ma sai ka zama mai sa a za a yi maka. Dan yanzu harkar kasuwancin sai in ta ku i masu yawa ne ake maganar dashi, amma komai da Bashir ake yi. Kamar ko yaushe yana zaune a falo tana kusa dashi yana ri e da hannunta saboda ciwon kan da take fama dashi, yana bin tabon ciwon da aka ji mata da yatsansa a hankali ya ce, "Kin san me?." Nayla ta ce, "sai ka fa "Akwai abubuwa da yawa da nake son siya, Akwai machines da kayan ado da za a dinga amfani dashi amma ance sai an je China ake samu." Nayla ta ce, "to ya za ayi yanzu kenan?." Ya yi ajiyar zuciya ya ce, "Ina tunanin zan je China Jidda, amma ance samun visa China yana da wahala sosai, shiyasa kaina ya kulle na rasa ya zan yi. Kuma bana so na tafi na barki, bana son yin nisa da inda ki ke kar a sake cutar min da ke. Nayla ta aure fuska ta ce, ana zancen arzu i zaka kawo wannan maganar, don Allah ka daina fa ar haka komai ya wuce. Ya sauke numfashi ya ce, to na daina, ina jin ki. Nayla ta yi murmushin ta ce, "Indai ta visa ne baka da case, akwai wanda Abiy zai yiwa magana a cikin sati aya za a iya buga maka visa China." Ya ce, "Da gaske?." "Da gaske wallahi, Indai har zaka je in kayi passport da komai, zan yiwa Abiy magana." an yin murmushi ya ce, "Shikenan, Gobe zaki raka ni passport office in sai ayi." Nayla ta rungume shi ta ce, "Allah ya kaimu Rouhii, Allah ya cigaba da saka maka albarka a duk abinda ka saka a gaba." Ya yi murmushi yana shafa fuskarta ya ce, "Amin, ki cigaba da taya ni addu'a." "Addu'a ko yaushe cikin yi maka mu ke yi." Ya kalle ta ya ce, "Daman ke ar baiwa ce ai, addu'arki da wuri kar uwa." Tayi dariya kafin ta yi magana ya ce, "da gaske nake. Tun daga ranar ashirin da bakwai ga watan ramadan na tsorata da lamarinki, kina kuka kina fa awa Allah abinda yake zuciyarki, a lokacin na ji a zuciyata Allah ya sa ba arata ki ke kaiwa ba." Ta kwanta a jikinsa tana dariya ta ce, "kuma na kai masa arar ka, a lokacin da ka ke hararata, nace Allah kana ganin bawan ka, ina jin tsoron idanunsa yana hararata. Ya yi dariya mai sauti bai ce komai ba. Nayla ta ce, Kukana nake kai masa, kuma wallahi Allah ya bani, babu abinda na ro o wanda Allah bai cika min shi ba a wancan lokacin." Ya yi murmushi ya ce, "shiyasa na ce ke ar baiwa ce ai. Ko zaki raka ni China? Kin ga dai ban ta a zuwa ba." Nayla ta ce, "ai da yawa wanda suke fara zuwa China duk basu ta a zuwa ba, a hankali suke gogewa su dawo an gari. Kuma da aka kashe min ku i a tafi dani gwara ai siyi wani abun da ku in, kar ka manta ginin gida ake yi." Ya ta e baki yana kallon ta ya ce, "wai ke irin mai tausayin nan ko?." Tayi dariya sosai ta ce, "eh mu je a haka." Dariyar shima ya yi ta kalle shi ta ce, "zuwa nan da yaushe ka ke saka ran tafiya?." "In aka samu visa nan da sati biyu ma zan tafi." Nayla ta ce, "lokacin bikinsu Ya J." Ya aga girarsa ya ce, "Uhum sai ki yi abinda ki ke so ko? Shiyasa ki ke murna." Nayla ta langwa ar da kai ta ce, "ya za a yi na yi murna bayan Rouhiina zai yi tafiya ya bar ni?." "Hmmm kya ji da shi dai" ya fa a yana murmushi ba tare da ya kalle ta ba. Itama murmushin ta yi kafin ya sake kallon ta su ha a ido ya ce, "Ya ciwon kan na ki?." Nayla tayi murmushi ta ce, "tunda ka zauna ka ke tambayata, na ce maka na ji sau i." Ya an yi shiru yana kallon ta kafin ya ce, " azu Didi ta ce min ina ki ke, sai na ce baki da lafiya, shine ta ce min ko ciki ne dake." Nayla ta auke ido daga kallonsa sai ya ja tsaki ya ce, "yanzu sai ki ce na baki kunya ko?." Nayla tayi dariya ta ago ta ce, "ni bani da komai." "Ya aka yi ki ka sani?." "Ka manta ina on period ne yanzu haka? Shine ma ya saka min ciwon kan." Ya an yi ajiyar
Chapter 127 · 0% Book details