← Book details Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 199 OF 205

Sashe 199

Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ya ce, "shine kuma zaki yi musu wannan tsawar? Haba Jidda, tun kafin na shigo na ji tsawar da ki ka yi musu, ai sai ki tsorata su, har nawa suke da za a yi musu wannan tsawar?. Nayla ta kalle sa da kallon mamaki baki bu e, dan ta lura sam baya so ayi musu fa a komai sai abinda suke ga dama suke yi, musamman Marmerh da take babba kuma mai iriniya, baya so ya ga Marmerh tana kuka ko ka an yanzu sai ya damu kansa kamar wani babban abun ne ya same ta. Nayla ta kawar xa kai gefe ta ce, " an nawa haihuwar kwana ukun zan bawa wa annan yaran? In suka yar min dashi fa? Haihuwarsa na yi fa, ba bacci nayi na farka na gansa a gefena ba. Kawai dan kar su yi kuka sai na basu shi? Sun da e basu yi ba. Omar ya an yi murmushi ya ce, "Eh na san haihuwarsa ki ka yi ba ajjiye miki aka yi ba, amma ki daina yi musu irin fa a haka, ki duba har kuka suke yi fa. In kika yi musu magana a nutse ai zasu fahimta, tsawar nan tsorata su ki ke yi wallahi. Nayla bata sake magana ba ta auke kai ta cigaba kallon anta da yake kwance a jikinta. Omar ya kalle su da suke kwance a jikinsa ya ce, "Kar ku daina kuka kun ji, ku kar a ku jr ku yi wasan ku ya fa a yana basu kayan za in da ya shigo musu dashi, suka kar a suka fita zuwa inda aka tanadar musu domin wasa. Ya bisu fa kallo har suka fita, ya kalli Nayla da ba shi take kallo ba tare da yin ajiyar zuciya ya ce, "Ban samu mun yi magana ba sai yanzu, bana samun zama sai ta kama. Ta kalle sa fuska babu walwala ta ce, "ka yi busy ai, ni in ma ba ganin ka nake yi ba" ta fa a tana auke kanta daga kansa. Ya an shafa kansa zuwa gashin fuskarsa ya ce, "Abubuwa sun yi min yawa ne wallahi, kwana biyu kuma bakya rage min aikin ne shiyasa. Na saba wani abun ke ki ke yi shiyasa abubuwan suka tarar min sosai. e baki ta yi bata ce komai ba. Ya nutsu yana kallon yanayin ta dan sai ya ga kamar fushi take yi ya ce, "wai fushin me ki ke yi ne haka? Ina magana kina kawar da kai kina aure fuska. Bata kalle sa ba ta ce, "ni ba fushi nake yi ba." "Amma meyasa ki ke aure fuska? Maganar ma kamar bakya so ki ke yi, da farko na auka saboda yanayin jikin ki, ne amma yanzu na lura kamar akwai wani abun a ranki. Nayla ta ce, "Gaba aya yanzu ka zama baka da lokacina, ko yaushe kana office baka dawowa sai dare, kuma da ka dawo zaka cemin bacci ka ke ji ka gaji. Abinci ma ba ko yaushe ka ke ci ba, in na ce a aiko maka dashi office ka ce a'a. A haka ka ke so ka ganni kamar daaa?. Kaima ai ba kamar da in ka ke ba yanzu. Tunda ta fara magana yake kallon ta har ta gama, ya girgiza kai cike da mamakin rigima irin ta ta ya ce, "Jidda aiki ne yake yi min yawa kin fi kowa sani, ke da kan ki kina taimaka min wajan rage min wani abun. Kuma ina sane nake cewa kar ki aiko da abinci saboda yanayin da ki ke ciki, yanzu kuma kin haihu, in ki ka huta sosai zuwa gaba zan ce a kawo ai. Ta ya zaki ce bani da lokacinki? Ina da wanda zan bawa lokacina in ba ke ba?. Ajiyar zuciya ta yi tana an ta e baki alamun bata yarda ba ta ce, "Haka ne." Ya yi murmushi yana kallon ta ya ce, "baki yarda ba kenan ko? Baki yarda da abinda nace ba?. "Hmm ni ban ce ban yarda ba, tunda ka fa a ai dole na yarda ko bana so. Amma batun canji ka canja fa, a daa in na auki wayarka baka damuwa, har fita ka ke yi ka barta a hannuna, wani lokacin ni ce ma nake aiko maka da ita saboda kar a neme ka. Amma yanzu da na auka sai ka ce na baka zaka yi amfani da ita, ko da kaga zan yi amfani da ita sai ka riga ni auka kamar wacce take yi maka bincike a ciki. Kafi kowa sanin ba bincike nake yi maka ba, inda bincike nake yi maka a wayar da ka sani. Babban abinda yake tsaya min a rai meyasa baka so na ri e? Meyasa baka so na auka bayan daa baka damuwa?. "Saboda bana so ki ga abinda zai ata miki rai ne." Da mamaki ta kalle sa ta ce, "Meye a wayar da zai ata min rai? Yaushe aka samu abinda zai ata min rai a cikin wayar?. "Ba wani abun bane a, amma wayar tana hannunki message zai iya shigowa wanda baza ki ji da i ba in kika gansa, ta ko wacce kafa messages da hotuna nake samu, ko nayi blocking wani zai zo. Duk da ba amsa nake bayarwa, ba amma in kika gani ranki bazai yi da i ba, na san halin ki. Saboda haka nake kiyaye acin ranki, shiyasa bana so wayar ta jima a tare da ke. Ta zuba masa ido tana kallonsa, kafin ta janye idanunta ta kalli gefe bata cr komai ba. Omar ya mi a mata wayarsa ya ce, "kar i." Bata kar a ba ta cigaba da kallon anta tana shafa kansa. Ya an yi shiru na wani lokaci, kana ya ce, "Jidda kina zargin ina da an mata a waje ne ko kina zargin na fara bin matan banza?." Da sauri ta kalle sa ganin so serious ya yi maganar, ta langwa ar da kai a raunane ta ce, "A'a,ni ban ce ba." "To meyasa ki ka damu dan ina kar ar wayataa hannunki? In akwai abinda nake aikatawa wanda bana so ki gani ai bazan ma bari ki auki wayar ba ko da wasa. Da rufe ta zanyi na saka mata security wanda baki san sa ba. Na san kuma ba bincike ki ke yi min ba, sai amfanin ki auka in ya zo ki ke aukar waya. Amma saboda gujewa acin ranki da jin babu da i a zuciyarki ya saka nake kar a. Amma ke naga zargina ki ke yi, zargi ki ke yi ina aikata wani abun mara kyau shiyasa. Da sauri ta tare shi ta ce, "A'a wallahi, ni ba zarginka nake yi ba, har abada bazan ta a zargin ka ba ta fa a a raunane tana kallonsa. Ya zuba mata ido yana kallon ta kana ya ce, "To me yasa kika damu kan ki har ki ke fushi?." Nayla ta ce, "Kawai zuciyata ta kasa aminta da hakan ne, na riga da na saba da yadda muka fara tun farko, ganin wannan canjin zai saka min shakku a zuciyata. Shakku, a kaina Jidda?. A kan wayar ba kai ba ta fa a tana rausayar da kanta. To waye mai wayar in ba ni ba?. Allah ba haka nake nufi ba. an yi murmushi ya ce, "Ni dai ina fa a miki, babu abinda zan oye miki a cikin rayuwata da wajenta. Jidda ko budurwa na gani ina so zan aura you're the first person da zan fara fa awa, ko ya yi miki da i, ko kar ya yi miki da i, ni dai na fa a miki saboda kece komai nawa, dan bani da wata bayan ke. Daman ke da Didi ne, to ita bata duniya sai ke ka ai, dole ki jure abubuwan da zan dinga zuwar miki dashi dan wani bazai yi miki da in ji ba. Ina so ki ri e wannan, bisa kuskure na aikata wani abun mara kyau wallahi sai na fa a miki Jidda, ko mai muninsa sai kin sani. Ta yi ajiyar zuciya a raunane ta ce, "balle ma baza ka ga budurwar har ka fara so ba, kuma baza ka aikata wani abun ba." an murmushi ya yi ka an yana lumshe idanunsa akan fuskarsa kana ya ce, "ki kwantar da hankalinki, wannan Omar in na ki ne ke ka ai in sha Allah, babu wata mace da zata yi miki over taking a wajena. Dan na san duk akan kar ki je ina da wata a waje ki ke wannan abun, to babu Jidda, har gobe da jibi kece ka ai. Abu aya nake so a gare ki...." ta ago ta kalle sa kamar yadda yake kallon idonta ya ce, "Yarda! Ki yarda dani kawai Jidda, bazan ta a cin amanarki ba in sha Allah. Yadda kika ri e min amanar kan ki nima bazan ci amanar ki ba, zan ri e miki kaina da zuciyata, babu wacce zata shiga zuciyata domin fadar ki ce. Murmushi jin da i da walwala tayi, ya shafa kumatunta yana ja ka an ya ce, keda kishi aminan juna ne. Ta kwantar da kanta a kafa arsa ta ce, kai kuma fa?. Bai bata amsa ba ya kalli Babyn da yake jikinta ya ce, "da Abiy zamu dinga kiran sa?." Da mamaki ta ce, "Sunan Abiy in ne? Na auka sunanka ne." "Sunan sa ne, in Allah ya kawo wani sai a saka sunan nawa." Ta yi murmushin jin da in karar da ya yi mata ta ce, "Na gode YaMar." Ya aga gira sama yana binta da kallo ya ce, "da aka yi me?." Murmushi ta yi bata bashi amsa ba, ta shafa kan yaron ta ce, "Allah ya raya mana Mufty." Ya bita da harara ya ce, "kin cika iyayi, daga Musliha an samo Mufty. Ko da yake ar gayu ce ke, dole ki saka sunayen an gayu. Ta yi dariya ta ce, "kuma dole ka fa a ba, haka lokacin Musliha ka ce baza ka fa a ba, sai gashi yanzu shi ka ke cewa har ka sana." Ya yi murmushi ya ce, "zan fita, ki yi lisaafin abinda za a siyo da abinda ki ke
Chapter 199 · 0% Book details