← Book details Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 205

Sashe 38

Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

banda fuska da tafukanta. Kinga babu afata a cikin al aura ko?. In ji? Wasu malaman sun ce hatta muryarki ma al aura ce. Ke fa ki ka ce min akwai wanda ya ce a bashi number ki saboda afarki ta yi masa, hakan ba zunubi ba ne ba kasancewar ki ta matar aure?. Nayla tayi shiru bata ce komai ba. Didi ta ce, Ko bai hana ba daman ina da niyar yi miki magana, ina sane ban yi maganar ba so nake ya magantu kamar yanzu kuma ya yi magana. Abu aya nake so ki sani, babu wanda ya zauna da Omar ya san halin Omar kamar ni, zaki fi ni sanin halayensa amma ba yanzu ba sai nan gaba, kafin ki zo karatun nake ora ki a kai yadda kafin ya riske ki kin haddace. Nayla inda Omar bai damu dake ba hankalin sa bazai tashi haka ba, sai ya ji abu a cikin zuciyarsa yake hargitsewa haka, abinda bai kai ya kawo ba baya damunsa har kiga fushinsa kamar wannan. Amma da zarar abin ya ratsa zuciyarsa nan take zai bayyana akan fuskarsa, baya ta a tayar da hankali akan abinda bai shiga zuciyarsa ba. In zaki tuna azu da na fara tambyarsa cewa ya yi bai sani ba arshe ya ta e baki ya bar maganar, amma da ya ji ke ce fa?. Nayla tana sauraren Didi amma bata ce komai ba tana tunanin kalaman da Didi ta fa a mata. Didi ta mi e da kanta ta kwashe tray in da ya fashe tana cewa, Wannan tray ya tashi aiki dole sai dai a zubar. Nayla ta mi e ta araso ta ce, Didi ki bari zan kwashe. Ajjiyewa tayi akan dining Nayla ta ce, Didi mu je ciki. Tare suka shiga ciki har bedroom in Nayla. Disi kalli Nayla ganin gaba aya ta canja sai ta ce, ki saki ranki don Allah, bana son wannan yanayin na ki. Ajiyar zuciya tayi aka kira wayar Didi ta auka ta fita falo. Ita kuwa bata bari kalaman Didi sun yi tasiri a zuciyarta ba ta cire kaya ta shiga wanka. Lokacin da ta fito sanye da bathrobe tana zaune a kan stool na madubi tana amsa waya. Didi ce ta shigo ta zauna a gefen gadon tana kallon Nayla. Nayla tana da kyau sosai, tana da madaidaicin jiki mai kyau da kuma kyakykyawar sura mai aukar hankali lokaci aya. Ta fi arfin Omar ta ko wacce fuska, tazarar su kamar nisan sama da asa ne, ita matar manyan mutane ce ba mitstsa irin su Omar ba. Dan Omar bai kai a ce masa aramin mutum bama sai dai a ce an mitsitsi. Alqalamin addara ne ya zana mata rayuwa dashi, in ba dan haka ba da matar minister ce ko sanata. Kashe wayar Nayla ta yi ta kalli Didi ta ce, Wai anin Salma ne zai yi graduation a London, shine Mama ta kira ni wai ko zan je. Didi tayi murmushi jin abinda ta ce sai ta ce, to zaki je in?. Nayla ta girgiza kai ta ce, na yi ya da aikina? Bazan je ba. Didi tayi murmushi a lokacin Nayla take shafa turare a jikinta sannan ta warware gashin kanta tana fesa turare. Didi ta ce, Nayla akwai ki da son hamshi, harda turaren gashi?. Nayla ta yi murmushi ta ce, Khamshi duniya ne Didi. Didi ta murmusa ta ce, Gaskiya ne. Wai kuwa Didi har yanzu kina abincin order?. Ina yi mana Nayla, Ina yi sosai dan yanzu har na biki na fara yi. Nayla ta wara idanu ta ce, waye yake taya ki?. Wacce take yi min aiki mana. amma kina ari, da nima na so nayi irin abincin nan wallahi. Didi ta ce, Aikin ai ba na ajebo bane irin ku, aikin da wahala baza ki jure ba. Nayla tayi dariya ta ce, wai ajebo. Ki tura min hotunan spices in da naga kin fara, ina da masu siya sosai. Didi ta ce, to Nayla zan tura miki, Na gode. Nayla ta ce, ke da kike aunata kenan, dana ce zan yi miki har kin yarda kin kuma gode, aninki kuwa da baya aunata, iris yake jira na shiga sabgarsa ya zane ni. Didi tayi dariya sosai ta ce, Hajiya Nayla amaryar Omar. Murmushi tayi bata ce komai ba ta cigaba da abinda take yi. Didi ta lura so take ta tashi ta saka kaya amma nauyinta take ji hakan ya saka ta ce, Bara na watsa ruwa na kwanta. To na dafa miki ruwan zafi?. a garin da zafi ai, haka zan yi ta fa a tana shiga ban aki. Ganin shigar ta ya saka Nayla ta tashi ta auko kayan bacci riga da wando masu kyau da tsantsi ta saka, ta fitowa da Didi doguwar riga ta ajjiye mata sai ta fita dan in ta fito ta shirya. Didi da ta fito ta ga kayan tayi murmushi ta shirya amma ba rigar ta saka ba ta saka wacce tazo da itaa. A lokacin Nayla ta dawo Didi ta bita da kallo kayan sun yi masifar yi mata kyau, kasancewar kayan jajaye sun haska fatarta sosai, ga gashinta a kwance ya sauka har kafa arta sai ta yi irin kamar wacce ta shirya zata je turakar mijinta. Didi kallon ta take tana tunanin da me Narma ta fita ne har ya furta yana sonta bai ce yana son Nayla ba? In surar jikin Narma ce ta ru e shi tabbas Nayla ta fita ira mai kyau da aukar hankali, kawai ita a oye surar take baka gani sai ka zauna da ita, sa anin Narma da take a bayyane ga kowa da kowa. Didi ta ce, Nayla kin yi kyau sosai, amma ki tattare gashin nan ki rufe kan ki dare ya yi. Nayla ta ce, To Didi, amma baki saka kayan da na ajjiye miki ba. Ai na taho da nawa shiyasa. Amma da kin sani kin saka, zan ji da i in kika saka ta fa a tana aure kanta ta saka hular kayan ta auki turare ta mi awa Didi. ar turaren tayi ta ce, Amma yana da i sosai Nayla. Murmushi ta yi bata ce komai ba ta zauna tare da aukar laptop inta ta ora laptop in akan table in da yake akin ta zauna akan cushion tana dammawa. Didi dai kallon ta take yi tana fatan Allah ya mallaka mata Omar kamar yadda take aunarsa, Allah ya saka zaman su ya ore har aljanna. Shiru suka yi baka jin sautin komai sai na keyboard in laptop da take dannawa, cike da warewa dan da sauri take dannawa. Ajiyar zuciya tayi ta an ture laptop in ta ce, na gama, wani aikin Ogan mu ya bani sai da na gama hankalina ya kwanta, yanzu bacci zanyi ta fa a tana kallon agogo a lokacin arfe goma na dare. Didi ta ce, da wuri haka? Na san bakya baccin wuri. Yanzu yi nake yi Didi saboda aiki, har na saba ma da yi Gaskiya dai, dole ki saba. Didi ta ce, To ni kam zan kwanta. Nayla ta mi e tsaye ta ce, nima na gaji, kwanciyar zan yi. Didi ta ce, in zaki fita ki kashe min hasken, sai da safe. Nayla da mamaki ta ce, Ina zan je?. akin mijinki mana. Nayla ta an tafi tunani waye ma mijinta dan maganar Didi ta ru ata. Didi ganin ta yi shiru sai ta ce, akin Omar zaki tafi. Nayla ta wara idanu tare da dafe irji ta ce, Innalillahi wa inna ilahir raji un! Didi har kin saka gabana ya fa i wallahi. Didi ta ce, Meye na fa uwar gaban?. Nayla ta ce, akinsa fa ki ka ce?. Eh nan na ce, kuma can in zaki je ba. Nayla ta girgiza kai ta ce, in kin ganni a lahira ai kaini aka yi Didi, iya fa ar da ki ka yi ma gabana fa uwa yake yi balle na aikata ta arasa fa a tana dariya. Didi ta lura ta auka wasa take yi hakan ya saka ta ce, Ba fa wasa nake miki ba Nayla, Yau a akin mijinki Omar zaki kwana. Nayla ta kalli Didi a firgice ta ce, Wai Didi da gaske ki ke?. Da gaske nake mana, ki wuce ki tafi. Da kina wanka ya dawo na tabbatar ya kwanta shima. Nayla ta zubawa Didi idanu a tsorace ta ce, Didi zan iya kwana a falo in bakya so na kwana tare dake, amma zuwa akinsa kamar barazana ne ga numfashina. Didi a tausashe ta ce, Haba Nayla! Me zai hana ni kwana tare da ke? Kawai baza ki kwanta nan in bane saboda mijinki yana nan, kuma akinsa akwai space ya ishe ku ku kwanta. Nayla ta sauke ajiyar zuciya ta ce, Didi don Allah ki bar fa a, bazan iya ba. Zaki iya Nayla, kuma zaki yi yanzu. Bazan iya ba Didi. Daman kin yi masa laifi ai, sai ki je ki bashi ha uri daga nan sai ki kwanta. Gobe da safe zan bashi ha uri amma ban da yanzu Didi, don Allah ta fa a a raunane tana kallon ta. Didi ta kalle ta cikin bada umarni ta ce, Nayla wacece ni a wajan ki?. Nayla a sanyaye ta ce, Yayata. To ki bi umarnina ki tafi akin mijinki ki kwana. Nayla kamar zata yi kuka ta ce, Didi ki yi ha uri bazan iya ba, shima kuma bazai bari ba. Tsawa zai yi min ko ya wula antani, bana son hakan bana jin da ta fa a ido na cikowa da hawaye. Didi ta ce, zai bari, na tabbatar miki bazai miki tsawa ba kuma bazai wula anta ki ba. In kuma kin je ya yi miki tsawa ko ya wula anta ki ki dawo mu kwanta tare, amma yanzu ki wuce ki tafi. Nayla ta dawo kusa da Didi ta ce, Didi ta ya zan iya zuwa? Ni fa ban da azu ban ta a shiga akin ba wallahi, yanzu ma in ki ka ce min ya tsarin akin yake bazan iya fa a ba tunda azun ma a ru Didi ta dafata ta ce, bazan yi abinda zai cuce ki ba Nayla
Chapter 38 · 0% Book details