Sashe 99
Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ido ta zuba mata domin ganin iya gudun ruwan ta, daga ranar da ta gaya mata har zuwa daren washe gari..amma Husnah bata nuna mata komai ba sai dai ta lura tafi bawa wayar ta muhimmanci a cikin lokutan.
Zaune suke tare a parlour bayan Sallar maghrib, amma idanun Husnah na kan wayar ta tana dubawa, daga jiya zuwa yau 'din ta tura masa text kusan thirteen times, amma ga dukkan alamu ko guda 'daya bai gani ba, ko yanzun ma text 'din take rubutawa karo na goma sha hu'du inda bayan ta kira dukkan layukan sa basu shiga ba kamar yadda ta saba ji shine ta shiga rubuta" Please Mu'een ka 'kira ne idan ka kunna wayar ka, hankali na ya tashi sosai, gashi ina cikin damuwa we need to talk".
Ji take kamar ta fasa ihu dan ba'kin cikin da take ji tana dannan "send"
sai taji muryar Mummyn tana cewa da ita" Husnah ko dai dama wannan batun auren naki shine abinda kike tambaya ta kwanaki akan wai ko naji wani abu kuma kika 6oye baki bayyana min ba?"
" a a Mummy"
Ta bata amsa cikin sauri tare girgiza kan ta side by side.
Mummyn Husnah kam sam bata yadda ba dan yanayin Husnah ya nuna mata akwai wani abinda take 6oyewa, dan haka cike da 6acin rai ta cigaba da fa'din" Ashe Husnah dan bani da matsayi a wurin ki shine har zaki iya bawa namiji damar turowa gidan ku batare da kinyi shawara da ni ba?"
" Ba haka bane wallahi mummy, nima fa bansan da maganar ba Allah..wanda na sani a can Shuwarin 'din kuma na ta 'kira layin sa bai tafiya bansani ba ko shine ya turo ko ba shi bane...Mummy in har auren zanyi ai kisan kece mutum ta farko da zata fara sani tun ma kafin aje ga Abbah".
Jin haka yasa Mummyn ta 'dan sakko sai tace
" A ina dama kika sanshi?"
" Makarantar mu ne 'daya da shi".
" Amma bai ta6a sanar dake cewa zai turo gun mahaifin ki ba?"
"A a wallahi Mummy ni bai ta6a sanar da ni ba ko da wasa ma".
" Ikon Allah!"
Mummyn ta fa'di cike da mamaki sannan ta cigaba da fa'din..." To ki ta gwada layin nasa duk sanda kika same shi kukayi magana, zan miki wata tambaya".
" To Mummy".
Tace cikin sanyin murya tana mai sake maida fuskar ta kan wayar ta dake ri'ke a hannun ta.
*Hmmm....Allah Ubangiji ka raba mu da sharrin social media* 🙏
_Comment_
_Vote_
_Share_
*Salmerh ce* 😍
💕 *NOORUL* 💕
(Haske nah)
By
*Salmerh MD*
*Wattpad @*
*Serlmerh-md*
💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*
_*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_
*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*
🅿 *48*
Ita kanta ta matsu ta jishi su gana, musamman ma da ta tuno jiya da dare bayan dawowar Abbah da ta gaida shi yanda ya kar6i gaisuwar ta cikin nuna halin ko'in kula, yana gyara zaman sa zuwa kishingi'da yace da ita" Wato mahaifiyar ki ce ta gayyato ki musamman domin ki zo ki gaya min cewa baki amince da za6in da nayi miki ba ko?"
Da sauri ta 'daga kai ta kalle shi tana girgiza kai tace" Ba haka bane Abbah..Mummy fa bata ce da ni in ce ban yadda da za6in ka ba..."
Tun kan ta rufe baki yace" To ai shikenan..sai ki je ki jira ranar 'daurin auren dan ba dogon lokaci za'a saka ba, mahaifan sa sunce min already kun daidaita kanku da yaron dan haka ba wani abinda zamu jira... daga Shuwarin suka zo wai sunan sa Muhammad...sai kije ki bincika cikin maneman ki babu mamaki kiyi saurin gano shi".
Sum-sum ta tashi tana juya sunan cikin ranta da matu'kar mamaki sai taji yace" Yauwa tunda kin riga kin dawo to babu kuma batun komawa sai bayan auren, idan mijin ki ya yarje miki komawa Falillahil hamd in kuwa yace a a shikenan sai ki fawwalawa Allah kinji?"
Kai ta 'daga masa alamar " Erh taji".
Sannan ta juya ta 'karasa fita daga 'dakin nasa wanda ada ya kasance 6angaren mahaifin ta ne.
Yanda 'karara wan mahaifin ta ya nuna rashin damuwa kan halin da zata shiga ya nuna rashin damuwar sa kan farin cikin ta ko akasin haka yasa a daren ranar sai da ta sha kuka amma babu wanda ya sani daga ita sai Allahn ta ne ka'dai da ta gaji ta lallashi kanta.
Shiyasa yanzun ta damu sosai wajen ganin ta same shi a waya, tafara gano kamar shi 'din ne amma bata da hujjar gaskatawa inba taji daga bakin sa ba....ko kashe wayar tasa ma sai take ganin kamar yana da nasaba da faruwar maganar auren amma duk tayaya zata gaskata hakan?..No way".
Ta riga ta san halin sa da kafiya da kuma bakin hali in ba dan haka ba da ko wata friend 'din zata 'kira tace a kai masa waya suyi magana amma tasan inba ra'ayi yayi ba Mu'een ba zai ta6a ansan wayar ba sai dai a idon 'kawartata yayi 'karyar ta bari zai 'kira ta kawai.
Ishaq ne ya fa'do mata cikin ranta, sai kuma ta tuna bata da contact 'din sa..haka ta zauna tayi tagumi tana tunani ta ringa sa'ma sa'ka abubuwa tana kuma warware su da kanta.
*****
Shi kuwa Mu'een har lokacin ya 'ki 'daga wayar ta sa ma a inda ya wullata balle ya kunna ta, haka zai yi duk abubuwan da suka zame masa dole ya yi shirin sa ya wuce makaranta ko kallo wayar bata ishe sa ba, wani sa'in ma bai zuwa makarantar sai dai ya yini a gida yana tunani...Ishaq ne yafi damuwa da lamarin sa, cuz sosai ya fahimci akwai abinda ke damun sa da yake so ya hana shi sukuni yake kuma faman 6oye musu.
Watarana da bai shiga school ba sai Ishaq da Imran da wani abokin su Anas jibo suka taho gidan sa dan duba shi dan sau tari idan basu gan sa ba suka sha gwada 'kiran wayar sa amma bata tafiya dole suke hakura su bar sa.
Yau kam Ishaq yace suje gidan su dubo shi, tun zaman su da shi kuwa ranar shine rana na farko da suka ziyar ce shi har gida, yau din ma bazata suka yi masa da yake already sun riga da sun san gidan, Mu'een bai ta6a basu daman zuwa inda yake ba ko da wasa.
Da sallama suka shiga gidan inda suka zarce har ciki.
A palour suka tarar da shi kwance fuskar na kallon ceilling, jikin sa kuwa ko singlate babu balle riga wandon jikin sa ne dai dogon ba'kin jeans ya sanya...hannun sa 'daya ya lan'kwaso ta ta ratsa ta saman fuskar sa yayin da 'dayan kuma ya dafe saman 'kirjin sa da shi.
Wanda Ishaq da yake yafi son shi da damuwa da shi yana ganin sa a haka yayi saurin zuwa gare shi inda ya taho yana fa'din" Me ke damun ka ne gaye har haka please?"
Yana jin tun daga yin sallamar su har isowan su kanshi amma ya kasa 'daga idanu ya dube su duk kuwa da cewa ya gane su, amma haushin zuwa masa da suka yi yasa yayi luf kamar mai bacci... 'kofar gidan ma sa'a suka ci da ya dawo daga masjid 'dazu ya manta bai kulle ta ba, amma ba dan hakan ba inda ace bugawa zasu yi to da kuwa ko kwana zasu yi suna bugawa ba zai ta6a tashi yaje ya bu'de ba sai dai su ha'kura suyi tafiyar su.
Gefen sa Ishaq ya zauna ya dafa hannun sa dake kan fuskar tasa yana sake tambayar " wai lafiya kuwa?"
Hannun ya 'dauke a hankali sannan ya bude idanun sa ya kalli Ishaq dake gefen sa, Ishaq gani yayi idanun sa sun koma jajazur tamkar ba nashi ba" Subhanallah"!
Ishaq yace a fili yana tattare goshin sa sannan ya sake fa'din " Me ke damun ka dan Allah Mu'een?"
Bai kula shi ba sai ya 'dan juya idanu ka'dan a 'dan fizge ya kalli Imran da Anas dake tsaye sai ya sake maida hannun sa kan fuskar ta sa ya rufe idanun sa.
Cikin dauriyar magana yace da su" Ya studies?"
Anas ne ya amsa da " Alhamdulillah".
Yayin da Imran ya jinjina kansa kawai yana 'ko'karin zama kan kujera...Ishaq kam baki bu'de yake binsa da kallon mamakin yanda ya koma a 'yan kwanaki 'kalilan din nan.
Duk yadda Ishaq yayi 'ko'kari wajen gano abinda ke damun sa amma Mu'een ya'ki sake furta komai sai da ya ga kamar hankalin Ishaq kwata-kwata bai kwanta da ganin sa hakan ba shine yayi dauriyar fa'din" kar ka damu babu abinda ke damuna".
Ishaq bai yadda ba sam amma haka ya 'kyale shi, har yamma suna tare da shi, tare suke zuwa Masjid su dawo amma babu wata hirar kirki ta 6angaren sa, sai bayan Sallar Maghrib kafin suka yi masa sallama suka wuce cikin makaranta.
Sam bai damu ba shi kam, dama dauriya kawai yayi amma wanzuwar ta su ba 'karamin takura shi yayi ba a gidan, surutun su na damun sa sosai da ya samu suka tafi kuwa sai da ya sau'ke ajiyan zuciya na jin dafi, har girki Anas yai musu suka ci amma shi Yah Deen bai ra'ayin abinci sam-sam, hakan yasa bai ko yiwa abincin nasu kallon arzi'ki ba.
Sai bayan ya dawo daga sallar Isha'i kafin ya ha'da Tea ya sha yayi kwanciyar sa....har a lokacin bai yi tunanin le'ko inda ya yada wayar tasa ba.
A kwanciyar san nan nema Ammi ta fa'do ransa sai yaji yana so yayi magana da ita 'kilan ko akwai taimakon da zatayi masa wajen hana faruwar auren.
Amma yanda yasan Alhaji Baba yasan Ammi bazata iya dakatar da shi ba...hakan yasa shi gyara kwanciyar sa da kyau batare da ya tashi ya 'dauko wayar ba...cuz ya lura babu amfani yin 'kiran ma.