Sashe 83
Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ni da nake tare da Ammi mafi yawan lokuta nice zan iya bada labarin sauyin da ya same ta a wancan lokacin, ban ta6a sanin 'kaunar da take yiwa Yah Deen ya kai irin wannan matakin ba ai da lamarin nan ya faru, yanda ta shiga damuwa, yawan gwada layin sa, yawan sakin tsaki, yawaita yi min hirar cewa bata san a wani hali yake ciki ba hatta Addu'ah bata ware ba nima sai da ta sani yin addu'a akan in ringa tayata adda'ar "Allah ya dai-dai ta tsakanin Yah Deen da mahaifin sa"
Ina kuma yi cikin ko wacce sallah ta, hatta Alhaji Baba bai kaini fahimtar 'kololuwar damuwar da Ammi take ciki ba cuz shi idan ta fara complaint baya bari ta 'karasa zai tare ta da fa'din " Karta damu lafiyar sa 'kalau kawai ta barshi ai ya girma ya san abinda ya dace ya aikata ba sai an tuna masa ba".
Ya kan yi mata maganar ne ta sigar gatse amma bata fahimtar inda ya dosa.
Cike da damuwa zata sake fa'din
" Ko abinci fa bai zuwa yaci".
Alhaji Baba murmushi kawai yake yi yace mata " Rabu da shi zaizo".
Yayin da ni kuma nake zama in nutsu in saurari damuwar ta kaf, tun bansan asalin me ya faru har yasa shi 'kauracewa zuwa gidan ba har nazo na fara fahimta a hankali cikin maganganun Ammi cewa sa6ani suka samu da Alhaji Baba akan wai wata budurwa na zuwa gidan shi, ni kaina da naji zancen ban girgiza ba haka kuma ban 'karya zancen Alhaji ba, zan iya kasancewa shaida akan cewa dagaske tana zuwa 'din cuz da idanu na nasha ganin ta amma bazan iya kallon cikin idanun Ammi in sanar da ita cewa hakan gaskiya ne ba sam, banjin zan iya hakan har abada tsoro ma ba zai barni ba in furta ba dan haka kawai sai na bi Ammi da idanu.
Yawan damuwar Ammi akan sa yasa ni fahimtar 6oyayyen sirrin 'kauna dake 'kunshe a zuciyar Ammi game da shi, ashe tun asali farin ciki ta yana wanzuwa ne da tabbacin 'danta Muhammad na nan cikin walwala, ban ta6a sanin haka ba sai a wancan lokacin da lamarin ya faru.
Ni kaina ina so inga Ammi ta saki ranta ta dawo kamar da cikin sakin fuska da walwala, wanda hakan ya sanya ni niyyar zuwa can gidan dubo sa in kuma ce da shi Ammi na 'kiran sa, na shirya hakan cikin raina ne batare da na sanar da Ammi ba.
'Karfe 7:37 na safiya ina 'ko'karin fita daga parlour da tunanin ya zanje in tarar da shi, yanayin da na same shi da waccen yarinyar a wanacen ranar shine ya sake dawowa 'kwa'kwalwa ta, kenan idan tazo kullum abinda yake yi mata kenan, bana so in yawaita tuna yadda naga hannun sa na yawo saman 'kirjin ta dake bayyane a fili, bana so in tuna balle har in bada labari, amma na kasa mantawa, har yau 'din nan hoton yanda naga Yah Deen na shan boobs 'din Husnah ya kasa barin kaina, na kanji kaina wani iri aduk lokacin da tunanin hakan yazo raina....(Addu'ar Deeni bata samu shiga ba kenan tunda Noor bata manta abinda taga yana aikatawa ba).
Ko yanzun ma da nake shirin fita ina 'dagawa Ammi hannu tunanin da ya fa'do raina kenan, tsoron yau kuma a wani hali zan tadda shi, ba dan Ammi ba da babu abinda zai kaini wannan gidan, amma soyayyar Ammi cikakkiya ce cikin zuciya ta saboda ita da da kuma son dawowar walwalar ta dole na bawa kaina 'kwarin gwiwar zuwa gidan.
Addu'ah Ammi tai min kamar yadda ta saba idan zani makaranta" Allah ya tsare ya da sa'a autar Ammi".
Haka take yimin kullum, sa6anin yau da kawai cewa tayi " Allah ya bada sa'a sai kin dawo".
Abinda kawai na samu daga gareta kenan kuma ma cikin sanyin murya ta furta hakan babu wannan fara'ar nan balle ta iya yimin kirarin "......Autar Ammi" shiyasa naji cikin raina ko dan in samu cikakkiyar Addu'ar da take yawan yi min ma dole in tayata farautan Yah Deen yazo gare ta ta ganshi, wala Allah ko zata dawo dai-dai.
A hankali nake rakawa na tunkari mafitar parlour ina gyara zaman babbar jakar dake rataye akafa'da ta wacce take cike tab da tulin takaddu na rubutu da kima textbook wanda Alhaji Baba da kansa ya aika aka siyo min su bai bari na yi rashin koda al'kalamin rubutu ba ne tunda na fara karatu a gidan sa, shiga na Jss one kuwa sai komai ya 'karu, uniform ma kala uku aka 'dinka min, safa na kusan kala biyar, canvas, sandal, tombs da kito mai kyau da tsada duk an tanadar min sai wanda naga daman anfani dashi nake sawa.
Sake gyara zaman jakar nayi karo na biyu dai-dai lokacin da na isa tsakiyar harabar gidan ina sake tunowa da Yah Deen, cikin raina nake ayyana " to meyasa zai yi purnishing Ammi akan laifin da ya san dagaske ya aikata ba sharri akayi masa ba?"
Da wannan tunanin na isa bakin gate ina shirin sa hannu in bu'de 'kofan sai naga an riga ni turowa wanda hakan ya sani 'dan matsawa baya ka'dan domin bawa mai shigowar damar shiga.
Lumshe idanu na nayi da jin yanda 'kamshin jikin sa ya buwayi hanci na take sai naji wata iriyar fargaba bansan ta menene ba, fuskar sa a hautsine ba ko alamun fara'a wanda a fizge na iya kallon yanayin fuskar ta shi take nayi 'kasa da idanu na ina fa'din " Ina kwana Yayah?"
Ko kula ni bai yi ba illah wuce ni da yayi kawai yayi shigewar sa cikin gida.
Cikin raina na furta " Bazaka ta6a canzawa ba farin cikin Ammi".
Baki na na ta6e musamnan da na tuna yanayin da naga fuskar sa, a hankali na ri'ke 'kofan hannu na ban fita ba haka kuma ban rufe 'kofar ba, bayan sa nake kallo yanda yake ajiye takun tafiyar sa" Salon ka daban ne 'dan Ammi"
Na sake fa'di cikin raina, tafiyar Yah adeen ka'dai aji ne da ita, balle idan ransa a 6ace yakan 'karawa tafiyar sa wani salo na sanyi da natsuwa da shi kansa inajin bai san hakan na da matu'kar 'daukan hankali ba...sanye yake cikin riga ba'ka da godon wandon jeans shima ba'ki, suman kansa yasha gyara sai shai'ki yake yi musamman da hasken rana ya 'dan haske shi walwalin sa gwanin birgewa, 'kafar sa ma wata ba'kar takalmi ce mai tudu da igiyoyi da dama sosai ya amshi 'kafar sa, hannun sa babu komai sai Key holder na makullin gidan da yake zama sosai yaui kyau hasken sa ya kara bayyana cikin ba'kar dressing 'din nasa bakace yana tare da damuwar komai ba.
" Hmm"
Na saki ajiyar zuciyar tare da juyawa na sa 'kafa na fita daga gidan ina ayyana " Allah yana sona sosai da bai barni naje wannan gidan ba ya ta'kaita min niyya ta".
A hankali na tunkari hanyar makaranta cikin tafiya ta ta masu natsuwa.
Ammi ka'dai ya tarar tsaye a palourn da yake yanzu ta gama sallama ta bata riga ta bar parlourn ba kuma dan yanzu Ammi komai cikin sanyin jiki take yin sa.
Tsaye take amma da ganin sa ya shigo sai ta saki ajiyan zuciya fara'a ta bayyana kan fuskar ta, komawa tayi ta zauna tana sakin ajiyar numfashi, cikin ranta take godewa mahallici da ya ta'kaita mata niyyar ta ya kawo mata shi har gida.
Gefen ta ya 'karasa ya zauna kan kujera yana shafo sumar kansa da hannun sa na dama, yayin da Ammi ke binsa kawai da idanu ita ka'dai ta san me take ji cikin ranta game da shi.
Sai da ya daidaita natsuwar sa kafin ya gaida ta ganin irin kallon da Ammi take binsa da shi da bai san na menene ba.
A hankali da muryar masu hankali ya gaida ta yayin da Ammi ta amsa shi cikin sakin fuska da fara'ar ganin sa cikin 'koshin lafiya batare da ya illatu ta wani 6angare na jikin sa ba.
Fuskar ta wasai bayan ta amsa gaisuwar tace da shi " Me yasa ka 'dauki tsawon kwanakin nan baka le'ko mu ba Mu'een? Ko fushi kake nufin zakayi da mahaifin ka dan ya gaya maka gaskiya?"
'Dago kansa yayi sosai ya kalli fuskar ta yana 'kan'kance idanu yace" Haba Ammi...ya zaki ce haka please? Ni waye da zanyi fushi da shi? ni da nake 'dan gata, har na samu mai gaya min gaskiya wani ma fa nema yake ya samu irin hakan amma bai samu ba...so dan me zan yi fushi da mahaifi na?"
Yayi maganar cikin sanyin murya da natsuwa.
Ammi ma cikin natsuwan tana duban fuskar sa tace " To me ya hana ka zuwa bacin kasan dole ne mu damu da rashin ganin ka da sanin halin da kake ciki?"
" Kiyi ha'kuri Ammi, amma ni kawai banson in 'kara 6ata ran Alhaji ne kar idan ya ganni ya sake harzu'ka shiyasa banzo ba".
Murmushi Ammi tayi da ya ratsa mata har zuciya sannan tace " Amma baka kyauta min ba".
" I'm so sorry Ammi na...kin san ai haka kawai bazan guji inda kuke ba".
" Ka kwantar da hankalin ka Alhaji bai yi fushi da kai ba...ya dai ce kawai muyi fatan Alkhairi".
Sakin numfashi yayi na jin da'di tare da fa'din " Alhamdulillah"
A fili tare da komawa ya kishingi'da da jikin kujera.
Ammi kuwa cigaba tayi da fa'din " Kwanaki uku kacal Mu'een amma ji bi ramar da kayi anya ma tun tafiyar ka ka 'kara cin abinci kuwa?"
Shima murmushin yayi tare da fa'din " Haba Ammi na, da bana ci ai da ban kawo wannan lokacin ba..."
" Banga alamaba ni".
Ta tare shi da fa'din hakan.
Sai yace " Hmm..Ammi agaban idanun ki fa Alhaji Baba ya sau'ke min yatsun hannun sa saman fuska ta alhali tunda nake da shi bai ta6a mari na ba tun haihuwa ta har sai yanzu da na girma na zama cikakken 'dan jami'ah mai shekaru ashirin har da biyar akai kinga kuwa dole in damu dan nasan abin ya ta6a ransa sosai".