Sashe 201
Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tsayuwa Noor tayi jim kamar bazata shiga ba.
A hankali ta 'daga 'kafafun ta ta bedroom 'din nasa...bakin ta nawi yayi mata sosai ko sallama bata iya ta yi ta yanda za'a ji ta ba, daga bakin 'kofa ta tsaya tana tunanin abinda zata ce da shi, daga inda take tana iya hango shi, baya ya juya ma 'kofan so baima san da tsayuwan ta wurin ba...jikin sa farin singlete ne sai abin rufa da ya lullu6e daga 'kafafun sa zuwa 'kugunsa..tana iya hango gefen fuskar sa da uban 'kasumbar da ya tara wanda ada ba hakan yake bari ba.
Bata ko yi motsin kirki ba balle ta furta wani abu har lokacin da ta 'dan ji motsin shigowa, zaton ta ko Saif ne dan yace da ita zai dawo hakan yasa ta waigowa amma sai taga Ammi ce ta shigo...take taji kunya ta lallu6e ta..sai ta 'kara yin gefe ta bawa Ammi hanya ta shigo.
Ammi da mamaki ta dube ta sannan tace" A a Hudah..dama kun baro wajen Alhajin ne?"
Sam Ammi bata ta6a zaton Noor zata yi tunanin zuwa duba shi ba.
" Erh" tace a hankali tana mai 'kara sunkuyar da kanta.
" Bacci yake ko?"
Ammi ta sake tambayar ta tana duban inda yake.
Noor shiru tayi dan bata san me zata ce da Ammi ba kuma.
Abincin da ke hannun Ammi ta ansa ta 'karasa ta ajiye kan drawern gefen gado..Ammi sai kawai ta 'karasa kusa da shi tana 'kiran sunan sa.
Shi kam tunda yaji an ambaci sunan Noor 'din sa ya kuma ji sassanyar muryar ta kusa da shi sai ya lumshe idanu, fatan sa Allah yasa ba mafarki yake yi kamar yadda ya saba ba, ko cikin Ramadan 'din da ta gaba ta ma ya ro'ki Allah sosai akanta, ya ro'ki Allah ya dawo masa da ita idan har itan ta kasance Alkhairin sa ne, sosai kuma ya du'kufa wurin neman yafiyar ubangijin sa bisa ga abubuwan da ya aikata, fatan sa Allah yasa Addu'ar sa ce ta kar6u Allah yasa ba wani mafarkin yake yi ba...bai yi ko motsin kirki ba amma da kansa ya gaskata kunnuwan sa musamman da yaji yanda yanayin bugun zuciyar sa ya canza nan take, har sanda Ammi ta iso kusa da shi ta fara 'kiran sunan sa amma ya kasa amsa ta.
Yun'kuri kawai yayi ya tashi zaune...a hankali idanun sa suka kai gare ta daga can gefe tana tsaye.
Kallo 'daya yayi mata sai ya kauda kansa gefe yana jin wani irin sanyi na ratsa masa cikin zuciya.
" Sannu ya jikin ?"
Ammi ta tambaye shi.
Saman la66a ya amsa mata da" Alhamdulillah".
" Bari in kawo ruwa ina zuwa"
Shine abinda Ammi ta fa'da kafin ta bar 'dakin zuwa waje.
Idanun sa da suka 'kara fitowa sosai ya 'kura mata yana kallon fuskar ta, itama 'din shi take kallo, zuciyoyin kowannen su da magana amma babu wanda ya iya furtawa...
Ita kam dake saurin kuka gareta har yanzun tuni hawaye ya wanke mata fuskar ta, a hankali tayi 'kasa da idanun ta ta tana share hawayen tausayin sa ne sosai ya cika mata zuciya.
Sai da ta share hawayen kafin tayi dauriyan bu'de baki ta tambaye shi" Ya jiki?"
Bai amsa mata ba sai ma kawar da kansa da yayi ya daina kallon ta, hannun sa ya koma mammatsawa a hankali haka kuma bai sake 'dagowa ya dube ta ba balle ta san ran yana da niyyan amsa ta.
Itama sai bata sake magana ba ta ja bakin ta tayi shiru....
Ammi na dawowa ta yi mata sallama gudun kar dare yayi mata tace zata koma gida..Allah ya 'kara sau'ki".
Ammi amsawa tayi da fa'din" Amin Hudah..sai gobe ko ki gaida Ummahn ta ki dan Allah".
" Zata ji Insha Allahu".
Duk muryar ta da sanyi tayi wannan maganar har Ammi taso ta fahimci sauyin yanayi tattare da ita ma amma sam bata bari sun ha'da idanu da Ammin ba dan haka kawai sai ta bita da idanu har ta yi waje.
Sallama taje yiwa Anty Zainab sai ta tarar da ita tana Sallah sai da ta jira ta idar kafin tayi mata sallaman ta fito, a harabar gida ta ha'du da Saif nan ta sanar da shi ta gama ya maida ta gida.
A fili take fahimtar farin cikin dake fuskan Saif wanda ba na komai bane face na zuwa kawai da tayi ta duba Yah Deen...tana lura dashi sosai farin cikin nasa na fita tun daga cikin zuciyar sa ne.
Hakan ne ya 'kara fahimtar da ita 'dumbin 'kaunar da suke yiwa 'dan uwan su.
'Bangaren Yah Deen kuwa bakin sa nawi yayi masa sosai, banda ma haushin dayake ji yana cin sa arai, ganin ta ka'dai da yayi ya rage masa kaso dayawa na abinda yake ji yanzu, ba gaisuwar ta yake bu'kata ba burin sa kawai yaji an sake mallaka masa ita ne, burin sa ta sake kasancewa matar shi ta har abada...a lokacin ne yake da duk wasu kalmomi da zai iya fahimtar da ita yawan 'kaunar da yake yi mata.
Washe gari Alhaji Baba da ya fita lambu sai ya samu lokaci ya 'kira 'kanin sa Ja'afar nan yake yi masa bayanin 'kudurin dake cikin ransa na son bada auren Noor da yake da buri wa Ishaq.
Uncle Ja'afar kam take ya nuna 'kin amincewra sa da fa'din.." a a ai hakan zai zama ne tamkar an shiga hakkin su gaba 'daya musamman ma shi Ishaq 'din, tunda kam ba aure ne da shi ba, kuma ma Noor matar abokin sa ace za'a bashi ai sai ya ziya ama sanadin rabuwar abotan su kenan..dan yasan Mu'een bazai juri hakan ba, kuma ma Alhaji kai baka tunanin halin da shi Mu'een 'din zai sake shiga ne? zuwa yanzun fa ya kamata ace an watsar da komai...yana son matar shi kawai a maida auren su idan ta amince da hakan shine ka'dai mafita in yaso sai a sanya idanu sosai akansa shima Ishaq 'din ayi masa fatan Alkhairi Allah ya bashi wata ta gari".
Shiru Alhaji Baba yayi yana tunani.
Uncle Jafar jin shirun yasa shi fa'din" Baka ce komai ba Alhaji?"
" Ka bari zanyi tunani".
Cewar Alhaji Baba wanda daga hakan suka yi sallama kowa ya ajiye tasa wayar.
'Bangaren Noor kuwa ganin tana gida ya sanya Abdulhakeem matsawa akan yana so kafin ta koma manyan sa suzo ayi magana in yaso data 'kare karatun sai a 'daura auren su kawai ta tare a gidan sa.
Duk yanda ta so ta kauce masa abin gagarar ta yayi domin ya matsa sosai, shi har ya yi magana ma da mahaifiyar sa akanta ta dai nuna 'kin amincewar ta amma yasan da zaran mahaifin sa ya amince shikenan.
Yanda ya matsa 'din ya sanya dole ta yiwa Ummah maganar cewa iyayen wanda ke neman auren ta naso su zo daga Kano wai.
Ummah kam shiru tayi tana duban ta da mamaki tace" Kina nufin wani auren daban zaki yi ne wai?"
Tuni ta marairaice tace" Ummah toni ya zanyi? ya matsa min kullum na rasa yadda zanyi da shi..".
Ummah baki ta ta6e gami da kawar da kanta gefe sannan tace" Sai kije ki sanar da iyayen naki ai kinsan suke da zancen auren ki ni ba ruwa na".
Koda ta shiga 'daki kuka ta ringa yi sosai, haushin kan ta ma take ji da danasanin biyo Anty Zainab da tayi, tasan ba dan ta zo 'din ba da duk hakan bazai faru ba.
Saif yace da ita Yayan sa na rashin lafiya ne saboda ita toh taya zata iya tunkarar su Ammi da batun wani daban kuma, ai sai suga kamar bata da tausayi ne shiyasa, ita kuma har ga Allah bata jin zata sake iya zaman aure da shi, a yanzu banda tausayin sa babu komai a zuciyar ta game da shi.
_Wai ina labarin Husnah ne?_
Comment
Vote
Share
*Salmerh ce*😍💕 *NOORUL* 💕
(Haske nah)
By
*Salmerh MD*
*Wattpad @*
*Serlmerh-md*
💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*
_*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_
*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*
🅿 *91*
Waya ta 'kira Anty Zainab da niyyan ta nemi shawarar ta amma sai ta kasa fa'din komai sai kuka, hankalin Anty Zainab tashi yayi sosai da jin hakan nan ta kwantar mata da hankali da al'kawarin gobe zata zo ta same ta, dama ta 'kira ne akan ga6a domin itama Anty Zainab in tana cikin tunanin ta ta 'kira, bata da'de da gama waya da Uncle Ja'afar ba tana cikin tunanin ta inda zata fuskanci abin sai gashi ta 'kira ta.
Washegari ta sa Saif ya sau'ke ta bayan tace da Ammi zataje gaida Ummahn Hudah ne.
Koda taje suka gaisa da Ummah suka 'dan ta6a hira ka'dan sai Ummah ta basu wuri kamar dama tasan da maganar da zasu yi sai ta tafi cikin gida gun ayyukan ta.
Nan Hudah ta samu sararin bayyanawa Anty abinda ke damunta...tace ita bata san ta ina zata fara tunkarar Alhaji Baba da batun auren Hakeem ba.
Anty Zainab shiru tayi tana nanata abin cikin ranta.
Wannan shine ana wata ga wata.
Ajiyan numfashi ta sau'ke sannan ta kalle ta tace" Ni har ma na rasa abinda zan ce da ke wallahi...kina nufin wai dagaske bakya tunanin sake zama da Mu'een ne yanzu?"
Shiru Noor tayi ta sunkuyar da kanta tana wasa da yatsun hannun ta...kowa irin tambayar da yake yi mata kenan, to ita me zata ce da su? amsar wannan tambayar tuntuni ta bayyanar musu da shi me yasa kuma suke son sake maida maganar baya?