← Book details Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 211

Sashe 45

Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin rashin nuna damuwar komai Mu'een ya nuno Rahma dake zaune ta takure tana aikin kuka yace " gata nan ka tambaye ta, babu mamaki zata fini iya yi maka bayani....."
Bai gama rufe baki baki Hayat ya 'daga hannu da niyyar sake masa naushi sai yayi saurin dakatar dashi da ri'ke hannun sannan yace " kwantar da hankalin ka abokina abin bai kai nan ba, ga dukkan alamu na fahimci a bakina kafi son jin bayanin....bakomai zan sanar da kai......"
Ya 'karashe da sakin hannun Hayatu sannan ya cigaba da fa'din " Rahma 'kanwar ka nada kyau Hayat kuma komai nata mai kyau ne, nayi babban sa'a domin tana so na sosai sai dai 6angare na ni abin sam ba haka yake ba.... dan ban ta6a jin ta a zuciya ta ba.....Hayat da naso cutar da Rahma da na yi hakan tun ba yau ba amma ban aikata ba dan sam ba shine a gabana ba, ban ta6a tunanin faruwar haka tsakanin mu ba kuma ina so kaima karka zarge ni.....idan ka lura bani da laifi musamman idan kana da masaniyar cewa ni 'din mutun lafiyayye ta kowani 6angare taya kake tunanin zan iya juran ganin hakan kuma ya zame min ba komai ba bayan na samu damar da ta dace?".

Ya 'karashe da nuno Rahma da hannun sa gami da cigaba da fa'din " ka kwantar da hankalin ka amma....abin bai munana ba ka bayyana kan lokaci in baka yadda ba kuma ka tambaye ta, ni zan wuce nice meeting u once again Hayat....na barku lafiya".

Yana gama fa'din hakan ya ratsa gefen sa ya fice abinsa.
Har cikin zuciyar sa yake jin babu da'di da faruwar hakan, bai so ace sha'ki'kin ta ya gansu cikin wannan yanayin ba, dan yasan abin bazai masa da'di ba, amma wata 6arin zuciyar sa sai zuga shi takeyi akan yayi dai-dai harma take tabbatar masa da cewa a yau fansar sa ta kammala burin sa ya cika ya 'kunsawa Hayat 'kunshin ba'kin cikin da zai jima bai bar idanun sa da zuciyar sa ba.

Yanajin da'di idan ya tuna hakan at the same time kuma yana tuna yafewar da yayi tun farkon tarayyar sa da Rahma....hakan sai yake tabbatar masa da cewa sam bai kyauta ba...duk dama yasan itama da laifin ta amma babban laifin nasa ne, tsintan kansa da yayi a wata duniyar bayan fara kissing 'dinta ya sanya shi mantawa da cewa ba akan dai dai yake ba.

Da ire iren tunanin nan ya tunkari bakin titi dan neman abin hawa zuwa gida ji yake tamkar iska na hure shi kamar 'kafar sa bazata juri 'daukan sa ba amma a hakan ya cigaba da tafiya.

' Bangaren Hayat kuwa da idanu yabi bayan sa har ya idasa barin 'dakin take wani 'kululun ba'kin ciki ya turnu'ke shi , hawaye masu zafi na takaici da ba'kin ciki ne ya gangaro masa.

Da hanzari ya 'karasa gabanta ya finciko hannun ta ta mi'ke tsaye arazane kafin ta ankara sai jin sau'kar mari tayi mai sa hauka ihu tayi niyyan sakewa sai yayi saurin kwarfan 'kafafun ta ta tafi 'kasa ta bugu da tiles 'din dake shimfi'de a parlourn.

Kasa yin kukan ma tayi dan azaba amma hakan bai hana Hayat dukan ta ba.

Comment
Vote
Share

*Salmerh ce*😍
[1/5, 11:23 AM] 🌸Salmerh🌸: 💕 *NOORUL* 💕
(Haske nah)

By
*Salmerh MD*

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

🅿 *23*

Cable na cajin lanta ya rarumo ya nufo kanta da shi a fusace, bata ankara ba sai jin sau'kan sa tayi a jikin ta haka ya dinga zabga mata cable 'din cike da 6acin rai.

Sai da yayi mata lilis kafin ya barta ya zauna bakin kujera yana hawaye dafe da kansa, yayin da Rahma ta takure a gefe tana kukan ceton rai wanda ko muryar ta ma baya iya fita sosai.

"....Rahma me kika rasa a gidan nan, da me aka rage ki da har zaki biyewa wannan 'dan iskan yaron, an gaya miki ana soyayya hakane?
Ko angaya miki idan ya gama lalata rayuwar ki zai aure ki?

Shiru bata bashi amsa ba sai ya sake fa'din " wama ya baki damar kulashi?....
Yanzun ma shiru tayi tana mai cigaba da sau'ke ajiyan zuciya.....Hayat sai ya sake mi'kewa a fusace yace " tambayar ki nake yi a ina kika sanshi?"

Yanda yayi maganar da yanda taga ya taso kanta ne ya sanya ta saurin furta " wallahi Yayah a school muka ha'du.....shine fa wanda nake gaya maka yake min Assignment idan an bamu"

Hayat kansa ya dafe gami da juyawa a hankali ya fara takawa....'kuna yake ji cikin ransa ji yake tamkar yayi ta zabga ihu, me yasa sai Mu'een Rahma zata kula?
Baya tantama kan cewa Mu'een da gangan ya shiga rayuwar Rahma, kenan yau 'din nan da banzo ba da Allah ne ka'dai ya san abinda zai faru da Rahma".

Innalillahi wa inna ilaihiraji'un....ya furta a fili gami da komawa da6as ya zauna bakin kujera......hannayen sa ya ha'da wuri guda yayin da zuciyar sa ta 'dai'dai ta sam ya kasa dai-dai ta natsuwar shi.

Batare da ya kalle ta ba ya fara fa'din " Duk haukata Rahma ni bana aikata zina bana lalata yaran mutane....amma me yasa zai min haka?
nawa ma Mu'een yake da har zaki bashi dama har cikin gidan ku har 'daki yana lalumar ki Rahma?, kinsan waye shi ne...kinsan miye tsakani na da shi?

" Dan Allah Yayah kayi ha'kuri ba zan sake ba...."
Tayi maganar da 'kyar cikin kuka.
Sai ya dakatar da ita da fa'din
" Wallahi Rahma idan kika 'kara biyewa yaron nan koda wasa ko Allah zaki ga abinda zan miki zaki sha mamaki na".

Da 'kyar take kuka amma hakan bai hanata bu'den baki cikin kukan tace dashi " dan Allah kayi ha'kuri Yaya wallahi ni ina son shi sosai bazan iya rabuwa da shi ba".

" Ya ta6a ce miki zai aure ki ne?"

Shiru tayi ta cigaba da kukan ta tana tunanin yaushe ma ita kanta tasamu amsar soyayyar ta ballantana har aje ga maganar aure.....shirun da Hayat yaga tayi ne ya bashi damar cigaba da fa'din......" Mu'inuddeen ba auren ki zai yi ba Rahma gara tun wuri ki cire shi a ranki dan ko yace zai aure kin ma ni ba amincewa zanyi ba, dan haka tun wuri ki cire shi a ranki, idan har a wannan shekarun nasa ya iya ya ke6ewa da mace to kiyi tunanin gaba mai zai aikata dan haka daga yau babu ke babu shi har abada".

Yana gama fa'din hakan ya tashi ya fice daga parlourn inda ya barta tana faman sake wani sabon kukan da fa'din " dan Allah yayah kayi ha'kuri wallahi shi ka'dai nake so ni....."
Ko sauraren ta Hayat bai yi ba yayi tafiyar sa....haka bai ko sake tunawa da takaddun da yazo kar6a a wurin ta ba.

*****
A hankali yake tafiya har ya isa bakin titi shi kansa bai jin da'di har cikin ransa bai san me ya kaishi aikata irin wannan aikin ba.

Mashin ya tara ya hau zuwa gida wanda da sau'kar sa ya wuce 'dakin sa batare da yabi ta kan kowa a gidan ba, dana sani kawai yake yi na sanin Rahma da kuma abinda ya aikata sai dai koma me ya faru yafi bawa Hayat laifi domin a ganin sa duk shine sanadi dan da be sashi ya bar wancan makarantar ba ai da bazai ta6a ha'duwa da Rahma ba balle ma har hakan ya faru tsakanin su.

Wayar sa ya 'dago ya shiga wurin text kan sunan Rahma ya shiga ya rubuta mata sa'kon kalmomi guda biyar kacal ya tura mata sannan ya bu'de bayan wayar ya ciro sim 'din ya 6alla shi gida biyu ya zuba cikin drawer.
Daga haka sai ya fa'da bayi yana mai istigfari cikin ransa.

*****
Cikin 'karfin hali ta tashi dan duk jikin ta ciwo yake yi mata da kuka ta shirya ta fito a gidan har ta kulle sai kuma ta tsaya saboda tunanin inda ya kamata taje a wannan halin, tsoron zuwa gidan Anty takeyi dan tasan inta ganta a haka dole ne sai ta tambayi abinda ya same ta inko tace ga wanda ya dake har hakan Anty sai ta nemi jin dalilin dukan to ince mata me? ta tambayi kanta.
Can gida kuma tsoron sake gamuwa da Hayat take ji tsoron sake ha'duwar su kar kuma taje gidan cikin wannan yanayin damuwar ta ya fallasa sirrin dake 6oye har ma'kiyan ta su fahimci damuwar ta wanda tasan daga nan kuma babu wani kima da zai rage nata a idanun kowa, domin sarai tasan halin matar baban su ba kau da kai zatayi daga gareta ba kuma kowa idan ya ganta a hakan dole sai ya tambayi dalili.
Gara Yayah Hayat tana da tabbacin in dai dan ta shine babu wanda zaiji labarin to in kuwa hakane me ze hana itam ta canza tunani.

Wannan tunanin ne ya sanya ta sake bu'de 'kofan ta koma ciki ta je da gudu ta fa'da gadon ta cigaba da kukan ta, ta gwammaci ta zauna anan ita ka'dai har sai kaka ta dawo da taje inda za'a 'kara 'daga mata hankali.

Sai da tasha kukan ta son ranta kafin ta tashi tayi alwala ta gabar da sallar la'asar.

Wayar ta ta 'dago da niyyar 'kiran Mu'een domin duk faruwar wannan abin bai sa ko 'dis daga cikin soyayyar da take yi masa ta ragu ba.
Chapter 45 · 0% Book details