Sashe 96
Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Uncle J bai bi ta kan maganar da yayi ba sai ya 'dan 'kan'kance idanu yana kallon fuskar sa yace
" Sai naga ma kamar bakayi murna da zuwa na ba Mu'een ko duk farin cikin zuwan nawa ne ya maida ka haka?"
" Ya ka ganni Uncle na canza ne?"
Shima ya tambaya yana bin jikin sa da kallo.
" Ai yanayin ka ka'dai ya bayyana min halin da kake ciki...meke faruwa da kai to ko zafin karatu ne, gashi ma naga ka baza takaddu ko'ina a gidan".
Murmushi ya 'ka'kalo sannan yace " Kamar kuwa ka sani wallahi, kasan yanzu mun zama manya karatu babu sassauci har kaina na 'dan min ciwo ma wasu lokutan".
" ..'Kilan baka baccin dare da kyau ne ko?"
Uncle J ya tambaya yana kallon sa.
Sai yace
" Ina yi Uncle kawai damuwa ce ta ishe ni sosai".
" Subhanallah..damuwa wace iri kuma Mu'een da baka iya ka sanar min ba tuntuni".
Uncle J ya fa'di yana duban sa da kulawa.
Kalar tausayi Yah Deen yayi yace" Maganar Alhaji Baba nake ta tunani Uncle, ban san inda maganar tasa ta kwana ba, kuma har yau bai sanar da ni komai akai ba.."
"...Ka kwantar da hankalin ka abinda ya kawo ni ma kenan fa musamman...amma sai naga dacewar zuwa in ganka tukunna kafin mu gana da shi..."
" Uncle to ya ake ciki ne..?"
" Ba komai ka kwantar da hankalin ka nace ai duk yanda mukayi da shi zan sanar da kai..amma dai yanzu ina so fara ka sanar dani abinda kace idan nazo zaka gaya min...menene silar tado maganar auren tell me".
Shagwa6e fuska yayi yace"...Nifa ba komai Uncle...ina dai zargin yaga lokacin da wata course mate 'dina tazo wuri na amsan wani manual ne shiyasa.."
Uncle J ido ya tsura masa yana kallon sa da son karantar yanayin sa..so yake ya fasa maganar dan ya fahimce ta da kyau ya kuma san fassarar da ta dace da maganar tasa
Shi kam wuya ya karyar gefe looking so innocent...idanun Uncle cikin nashi yace"
Wata daga ina kenan?"
" Azare".
Yace a hankali.
"..Tun daga cikin Azare ta bika har Shuwarin dan kawai kar6an manual...ka gaya min gaskiya Mu'een..banson 'karya nasan haka nan dan 'dan wannan dalilin Alhaji ba zai ce zai yi maka aure ba.."
"...Uncle da gaske babu komai..ni kam iya abinda na sani kenan".
Tsaye Uncle Ja'afar ya mi'ke yana nanna'de hannun rigar sa yake fa'din" Bari mu hanzarta zuwa masallaci kar mu makara".
Comment
Vote
Share
*Salmerh ce* 😍
💕 *NOORUL* 💕
(Haske nah)
By
*Salmerh MD*
*Wattpad @*
*Serlmerh-md*
💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*
_*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_
*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*
Those who remember Allah standing, sitting, nd lying down on their sides, nd think about d creation of d heavens nd d earth, (saying): “Our Lord! You have not created all this without purpose, glory to You! Give us salvation from the torment of the Fire.(Ali ‘Imran,3:191)🌷
🅿 *47*
'Dakin Yah Deen suka shiga tare inda yayi masa jagora gami da nuna masa bayin yace" Bismillah".
Shiga yayi ya 'dauro alwalar ya fito, yana fitowa sai idanun sa ya sau'ka kan gadon Yah Deen yanda ya sha gyara sosai sai da ya bashi mamaki, yana murmushi bayan ya kawar da idanun sa yace" Ashe fa yaron nawa nada tsafta sosai, irin wannan gyaran gado da ka iya ai har kafi wasu matan ma...kenan ma ko auren Alhaji yayi maka matar bazata sha wahala ba tunda har ka iya 6ata lokaci kayi irin wannan gyaran to sauran ayyukan ma duk zaka iya su...yaushe ka koyi aikin mata har haka ban sani ba...?"
Dum zuciyar sa ta tsinke da 'karfi dan yasan ba shine yayi komai ba.
Yayin da Uncle ya cigaba da fa'din" Kaida na san ko sharar 'dakin ka ma wahala yake baka ada...amma ji gidan nan fa ko'ina tsaf..."
Murmushin 'karfin hali kawai ya 'ka'kalo ya sanya wa fuskar sa, sai dai inda zaka tona zuciyar sa Allah ne ka'dai ya san yawan beating 'din da take yi wanda ya kasance ba bisa ka'ida ba, a zahirin ma bai iya ya furta komai ba...cikin ransa yake ayyana" Allah ka rufa min asiri...harda rero addu'ar _Allahu Allahu Rabbii..la'ushriku bihi shai'an_..Har baisan sau nawa ya ambace ta bama tsabar rikicewa.
Da haka ya nifi hanyar bayi yana mai sunkuyar da kansa 'kasa...cikin zuciyar cike da tunanin..in shine zai yiwa mace irin wa'dan nan aiyukan ashe kuwa ba zata ta6a zama da shi ba har abada...baki ya ta6e sannan ya shige bathroom 'din.
Alwalar shima ya 'dauro ya samo Uncle a palour wanda da ganin sa sai ya mi'ke yana sake bin palourn da kallo yace.." Wai har da wannan abin matan ma ka'iya amfani da shi?"
Wannan karan kam sai da ya lumshe idanu ya furta" Rabbi help me" Kafin ya juyo ga Uncle 'din bayan ya bu'de idanu cikin dakiya ya amsa da fa'din" Wani abu ne Uncle?"
Da baki Uncle J ya nuno masa Burner..sai ya saki salati cikin ransa shaf ya manta da shi kwata-kwata in ba dan haka ba ai da ba zai bari ba ma balle har yazo ya gani, da i ina ya fara fa'din" Na..iya mana..Uncle ai babu wani wahala...Ishaq ne.. ya kawo min tsarabar turaren wuta daga garin su... kasan 'yan Borno ne su, shine fa na siyo wannan 'din".
Ya fa'di hakan ne kawai dan kare kansa amma ba wai dan ya san ko yanda ake kunna burner 'din ba..bai ta6a bi ta kansa ba, tsakanin sa da abin kawai yaji gidan sa na tashin da'd'dan 'kamshi idan Husnah ta kunna.
Hanyar waje suka nufa Uncle na fa'din" Ko de waccen yar Azare 'din ke zuwa tayaka ayyukan gidan?"
Ya fa'da da sigar zolaya.
Da sauri Deen ya ja ya tsaya kamar zai yi kukan an fara gano sirrin shi yace " Haba-haba.. Uncle kaifa mahaifi ne...me yasa zaka min irin wannan zargin dan Allah..yarinyar da ma tun dawowa ta bansa ta idanu na ba taya zata taya ni yin wani abu?"
Murmushi Uncle J yayi sannan yace" Abin naka ne ai da ban mamaki ga duk wanda ya sanka Mu'een..."
Shiru yayi bai sake fa'din komai ba, cuz ya lura idan ya cigaba da tanka masa zai iya tona asirin kansa da kansa.
Da haka suka nufi masallacin still Uncle J na sake masa zolayar shifa sai ya fa'da masa inda ya koyi aikin gida har haka".
Da 'kyar ya samo abin fa'da cikin ransa bayan ya gama tsarawa sannan daf da zasu shiga Masjid ya furta" Zama ni ka'dai ne ya sani koyan komai Uncle harda girki ma duk na iya yanzun".
Yayi maganar ne afili amma cikin ransa da fatan Allah yasa kar Uncle ya sake fa'din komai...
Cikin sa'a kuwa murmushi kawai yayi masa da jin amsar da ya bashi.
Ganin hakan kuwa sai da ya sa shi sakin ajiyar zuciya ciki-ciki, wani 6ari na zuciyar sa kuma na fatan Allah yasa kar Husnah ta dawo gidan balle Uncle ya ganta ya gaskata zargin sa.
Ko da ya idar da Sallah ma sai da ya ro'ki Allah akan ya rufa masa asiri ya kautar da idanun Uncle da tunanin sa akan rayuwar sa.
Da ikon Allah kuwa suna dawowa daga Masjid 'din sai Uncle J yace shi kam zai wuce kar yamma ta same shi.
Sai da ya sake tambayar Yah Deen akan abinda suka tattauna farkon isowan domin neman 'karin bayani, Mu'een sai cewa yayi" a a ya bari kawai sai sunyi magana da Alhaji Baba tukun..ya 'karashe da fa'din" Ni dai auren banaso yanzu Uncle"
Ya fa'di haka ne kawai gudun kar ya tonawa kansa asiri da abinda zai sake furtawa musamman da ya san cewa yanzun Uncle J ma na jin zargin irin rayuwar da yake yi cikin zuciyar sa duk da be bayyana gaba 'daya ba but dole ya san akwai ayar tambaya cikin ransa.
Uncle kuwa cewa yayi" Idan Alhaji ya dage akai dole ne kayi ha'kuri, sannan kasani nima bazan yi ta jajayya da shi ba tunda auren ba haramun bane ha'kuri kawai zakayi kayi na'am da batun...
Yatsa ya 'dago ya nuna shi da shi sannan ya cigaba da fa'din" Kuma ka sani idan har ka kuskura bincike na ya bayyana min rashin gaskiyar ka akan maganar nan, ko kuma naji wani abu na daban kai kanka kasan ba zamu shirya da kai ba ko?"
Shiru yayi illah jinjina kai da yayi yana mai sau'ke idanun sa 'kasa...
Wanda ganin hakan yasa Uncle J sau'ke ajiyar zuciya
bai wani 6ata lokaci ba kawai ya 'dau jakar sa Yah Deen sai yayi saurin amsar jakar daga hannun sa...suka fice daga gidan Deen ya sake kullewa.
Suna kan hanya yana raka shi kafin su isa bakin titi sai ya hango Husnah na tahowa cikin tafiyar ta mai 'daukan hankali..take hankalin sa ya tashi fiye da zaton mai karatu" Me kuma ya dawo da ita yanzun?"
Ya tambayi kansa..shaf ya manta da cewar dama 'karfe hu'du zata dawo..2-3 ne last lecturen ta na yau...tuni hankalin sa ya koma gare ta sai dai bai bari Uncle ya gano sa ba ya dake kawai suka cigaba da tafiya zuciyar sa cike da fargabar kar ta tona mai asiri, har suka kusan ha'duwa da ita bai daina satan kallon ta ba.
Yayin da itama Husnah tun da ta hango shi tafe da wani mutun ta tsura musu idanu da tunanin ko wanene mutumin oho...sai dai Husnah har cikin ranta bata yi niyyar tanka shi ba..cuz da gani mutumin ba sa'an shi bane in kuwa haka ne magana ga junan su agaban idanun sa sam bai dace ba ko dan su bashi girman sa matsayin babba agare su.
Shi kam Ya Deen ya kasa natsuwa sam duk sai ya raba hankalin sa gida biyu, ji yake da da wata hanyar agaban su kafin ha'duwar su da Husnah da yace su bita koda kuwa ba ita ta dace su bi ba amma a lokacin kaucewa Husnah shi zai fi komai yi masa da'di cuz gani yake kamar zata tona asirin sa.