← Book details Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 104 OF 211

Sashe 104

Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Anty Zainab kam Murmushi tayi ganin yau abinda yayi, rasan duk cikin fushin auren ne.." Ban da abinka ai Alkhairin sa zaka nema".
Ta fa'di hakan ne cikin zuciyar ta.

Wani shegen yadi ta za6a masa mai kyau da tsada, dan tasan wannan sarkin tempern da wuya idan zai natsu har ya 'dinka kayayyakin da ya dace a sanya su wurin biki.

Sai da ta gama za5a masa duk abubuwan da ta ga cewa sun dace da shi sannan ta dawo kaina a fili ta furta" Ba za'a bar yarinyar Ammi a baya ba".
Ta 'kaeashe da murmushi.

Siya min nima tayi tsadaddun lace kala biyu ta bada 'dinki tun acan aka 'din ka min dan ita Anty Zainab haka kawai take jina har cikin ranta, Ammi ma am mata nata kala uku masu masifar 'daukan hankali abin sai wanda ya gani, gaskiya Anty Zee tayi 'ko'kari sosai dan kayan da ta siyawa Yah Deen ma sun kusan kaiwa akwati guda.

Haka Anty Zainab suka dawo gida da kaya kaca-kaca, lokacin da ta nunawa Ammi kayan da ta 'din ko min sai duk farin cikin Ammi ya ninku akan nada, ko nata kayan bai sata farin ciki kamar yadda taga nawa ba, dama already ta bayar da kayan Yah Deen da ya ta6a siyawa Nanne tace a 'dinka min riga da skirt inda ta ha'da da wata super atampa tace duk a'dinkamin na fitan bikin Yah Deen, ta kuma siya min takalma na da mayafai, sai nake jina tamkar wata sarauniya tsabar da'di musamman da naga wanda Anty Zee ta kawo min suma da mayafan su da takalma sai nakasa 6oye farin ciki na...wanda Alhaji Baba ya siya mana kuwa ban san guda nawa ba amma dai daga ni sai Ammi ya siyawa...su Saif yace sai sun dawo.

Ma'u itace mutun ta biyu dana gaya wa cewa an 'dinko min kaya da yawa na bikin Yah Deen wanda tuni na kaiwa Ummah ta labarin...ina murna ta na fa'da mata lokacin an taso daga islamiya muna hanyar mu ta zuwa gida, gani nayi Ma'u ta tsura min idanu kawai tana kallo na, ban damu d kallon ba ni kam kawai na cigaba da bata labarin yawan kayan da kuma kyan su cikin jin da'di.

Muna kan hanya wani mai suna Ahmad dake matu'kar son Ma'u ya tari gaban mu yana yi mata magana, har a lokqcin kuwa bata ce da ni komai ba ni ke ta zuba abina, kawai tashin farko kamar dama jira take tga ya bayyana gaban ta sai gani nayi ta fara zazzaga masa masifa tamkar wani 'dan cikin ta, ni kuwa da ban iya yiwa wanda ya fini rashin kunya ba sai na zaro idanu na ina kallon ta, ina 'kiyasta shekarun tsakanin su kamar wacce aka gaya min, na dan yafi ta tsayi da girma amma bansan shekarun sa ba, Ma'u ce dai nasan sha shida ne shekarun ta cuz asali bata kai Nannen mu shekaru ba kawai dai Allah ya ha'da jinin su ne balle kuma da yake ita Nanne na da matsalar rashin lafiya shiyasa ma bata da saurin girma sai duk mu ka zama 'daya harda ni.

Ma'u na gama masifar tayi gaba abinta nima dake faman tunanin sai na bita abaya, har nayi gaba sai kuma na waigo na kalle shi" Yah Ahmad dan Allah kayi ha'kuri". nace da shi da karyayyiyar murya dan har ga Allah banji da'din abinda ya farun ba.

" Bakomai 'kanwata kar ki damu".
Yace da ni yana murmushi da alamu masifar tata bata wani 6ata ransa ba.

Kai na jinjina masa ina juya sunan da ya 'kira ni da shi wato 'kanwa ta..nasan babu mamaki Yah Ahmad da nacecda shh ne ya sa shi ce min 'kanwar shi..ni kuwa Ammi ce ta ce da ni duj wanda ya fini ince da shh Yah..in macece kuma ince Anty tace min mutane na matu'kar son yaro mai girmama manya..shiyasa na saba da hakan.

Kusa da Ma'u na tsaya ta gaban ta da niyyan gaya mata kuskuren da tayi  sai dai kafin nayi magana sai kuma naga tana share hawaye...baki na ta6e gefe batare da na ce da ita 'kala ba...Gaba ta yi sai na bh bayan ta da kallon mamakin kukan kuma, wannan shine fin 'karfi ita da masifa kuma itace ke da kuka.

Ban bh ta ba na tafi a nutse kamar yanda saba har na isa gida, dama ma ko mhn tafi tare ma mhna rabuwa a hanya dan 6angare daban muke da ita.

Bintu 'kawata da muke aji 'daya amakaranta itama sai da na bata labarin kayan nawa ina mai matu'kar farin ciki.

Bayan kwana biyu sannan muka ha'du da Ma'u cuz bata zo jiya ba, bayan an tashi daga Islamiyar ban damu inji mai ya hanata zuwa jiyan ba sai kawai nace mata" Rann nan baki kyauta ba gaskiya Ma'u da kika ta yiwa Yah Ahmad masifa,  naga shi 'din ba sa'anki ba ne, Allah ki daina rashin kunya..in ba haka ba duk ranar da kika ha'du da irin su Yah Deen wallahi dukan tsiya zaki sha babu ruwa na".

Baki ta mur'da tare da fa'din" Dama nace da ke akwai ruwan ki a ciki ne?"

Jin abinda tace 'din ya sani kawar da kai na gefe nima nace" Ni dai na gaya miki..."

Kafin ma in gama rufe baki na sai ta waigo ta kalle ni tare da saurin taran baki na da fa'din" Wai dagaske aure zai yi?"

" Wa 'din?"
Nima na tambaye ta ina yatsina fuska ta...sai tace " Yah Deen 'din mana".
Nace mata" ehh mana Auren kwanan nan za'ayi".

Shiru tayi bata sake ce da ni komai ba, har muka rabu nima ban sake yi mata magana ba dan haushin rashin kunyar da ta yi kuma bata ce mjn bazata sake ba shiyasa naji haushi.

*****
      Wasa-wasa lokaci na ta faman 'karatowa yanzu Mu'een ya saki ransa a makaranta ba'a gane cewa yana cikin damuwa sai dai a kowanni lokaci bashi da aiki sai tunanin irin abinda zai yiwa matar da za'a aura masa, lokuta da dama zaki ga ya saki murmushi shi ka'dai wanda ba na komai bane face na tsantsan mugunta..bai ta6a furtawa kowa shirin sa ba daga shi sai zuciyar sa yake shirya abin sa dan ya san idan Ishaq ya sani wa'azi zai ringa yi masa kullum har yaji ya fasa shi kuwa abinda zai hana shi aiwatar da niyyar sa akan ta to mutuwa ce ka'dai..hakan yasa yaja bakin sa yayi shiru.

Sha'kuwar sa da su Ishaq kuwa sai abinda yayi gaba cuz weekend 'din da ya wuce ma a gidan sa suka yi ta...Ishaq na matu'kar jin da'din yanda yaga lokaci guda Mu'een yayi watsi da damuwar sa ya rungumi 'kaddarar sa, shi ka'dai ya san farin cikin da ya shiga da ya fahimci yanzu Mu'een baya tare da damuwar komai, shine kuma ya fara fahimtar yawan murmushi da Mu'een ke saki a mafiya yawan lokuta batare da dalili ba, harma da ya tambaye shi dalilin sai yace wai mamaki kawai yake yi wai shi za'a yiwa aure.

Ishaq sai yace" Zaka iya ne ai shiyasa tun yanzu Allah ya za6eka tun kana 'dan shekara ashirin da shida a funiya ya baka damar cika sunnar ma'aikin sa..so is better ka gode masa kawai".

Ajiyar numfashi ya sau'ke yana fa'din" dole na ai".

Anas sai yace" Kaga mu har yanzu bamu samu wannan damar ba kuma babu wanda ya tuna da mu yayi mana gatan hakan".
Ya 'karashe maganar yana murmushi.

Mu'een sai yace" Karka damu Anas lokaci ne ai".

" Hakane".
Imam yace yana 'daukan wayar sa, yayin da Ishaq ya jinjina kansa up and down vike da gamsuwa.

*****
      Yau ta kama kwanaki tara kenan da yin wayar sa da Alhaji Baba har yau 'din kuwa basu sake ba, kuma yana sane da cewa gobe ne ya kama ta ya tafi Shuwarin kamar yadda Alhaji ya bu'kata amma sam bai shiryawa hakan ba, musamman da ya san cewa a dalilin auren Alhaji yace ya je tun sauran sati guda shiyasa yayi biris da maganar.

Yana waya da Ammin sa, Anty Zee da Uncle J da suka shirya bayan yasha masifar raina masa hankali da yayi ya kashe wayar sa acewar sa...da 'kyar Yah Deen ya bashi ha'kuri ya sa'k'ko sannan suka shirya da shi.

Tun daga lokacin suka koma normal tamkar baya, shine ma yace Mu'een 'din kar ya sayi komai zai taho masa da duk kayan da zai yi amfani da su wurin bikin.

'Kasan ma'koshi ya furta" Dama ka hutar da ranka" ji yake shi ko da polo da jeans zashi wurin 'daurin auren babu abinda ya dame sa...A fili ya furta" Wannan mutumin ma brain 'din kifi gare sa wallahi".
Ni kaina sai da na zaro idanu nace kardai uban naka ne mai brain 'din kifi?

Sai kuma naji yana fa'din" In ba haka ba taya baka ta6a ganin mutun yazo wurin 'yar ka ba ba ka san sanin mutum ba sai ka 'dauki aure ka bayar".

Kai 'dan kuka mai jawa uwar sa jifa rayuwa kenan... _Allah ubangiji ka shirya mu ka shiryar da zuri'ar mu, Yah allah kar ka bamu 'ya'yayen da zasu ja mana zagi...Ameeen._

*****
Zauna yake kishingi'de kan kujera mai zaman mutun 'daya, kan cinyar sa Tablet ce yana dubawa yayin da wayar sa ke ajiye gefe dashi a hannun kujera.

Ishaq na daga can gefe kwance kan 2seater yayin da Anas da Imam suke daga 'kasan carpet zaune suna buga wasan karta gefen su lemun coca cola ne suna sipping lokaci zuwa lokaci.

Wayar Mu'een ce ta fara Vibrating sai ya kai duban sa kan fuskar wayar da tunanin ko Alhaji Baba ne ya 'kira.

Comment
Vote
Share

*Salmerh ce*😍

💕 *NOORUL* 💕
(Haske nah)

By
*Salmerh MD*

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

_*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

🅿 *50*
Chapter 104 · 0% Book details