← Book details Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 211

Sashe 28

Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jas kuwa sai kallon shi takeyi tana jin babu da'di, ganin tarin ya tsaya ne ya sanya ta cikin sanyin murya tace " Sorry Daddy...inaso in tashi amma 'kafana ciwo yake min....".

Cikin 'karfin hali shima yace " kar ki damu mamana ai ya daina ma kingani ko?"

Cike da takaici Noor taja dan guntun tsaki
" Mthew" kana ta koma tayi zaman ta gefen Jas tana gyara mata mayafin jikin ta ta'ki ko da kallon inda yake ma.

Tsaye Deen ya mi'ke da 'kyar cikin 'karfin hali dafe da 'kirjin na sa ya saiti hanyar fita.
Taku 'daya zuwa uku yayi sannan sai ya juyo ga Noor ya kalle ta yaga ko bi ta kansa ma batayi ba illah hannun Jas da ta kamo cikin nata, a hankali cikin sanyi da nutsuwa yace " Ki gafarce ni Nuree.....ina so ki sani....banta6a aikata wani abu ba....dan na 'kuntata miki ko rayuwar ki ba koka'dan, sai dai wannan karon bansan ta yanda zanyi in wanke laifina a gareki ba duk dama nasan....cewa ehh ni 'din....ni mai laifi ne....amma ya zanyi?
Ya zanyi Nuree bazan ta6a iya goge abinda ya riga ya faru ba tunda bani da ikon yin hakan....but
instead i regret everything.....i regret every step of my life Nuree.... har abada nasan ni mai laifi ne agareku dukkan ku amma please ki yafe min ko Allah zaiji 'kaina Nureee, ki yafe min ko zanyi sa'an samun gurbi a gefen manzon tsira.....trust me Nuree insha Allahu daga yau d'in nan i promise u bazaki sake shiga damuwa saboda ni ba, bazan sake shigowa cikin rayuwar ku in hargitsa muku farin cikin ku ba....zan barku har abada Nuree tunda hakan kika fi bu'kata......."

Jas ne ta yanke maganar tasa da fa'din " Daddy is still begging mummy please forgive him".
Tayi maganar tamkar zatayi kuka.
Noor kuwa cewa tayi
"Shut up da Allah....rufe min baki....baki ga baki da lafiya bane Baby...ina ruwan ki da surutun sa".

Kai Deen ya girgiza sannan ya 'daga 'kafa a hankali ya juya da 'kyar yake 'daga 'kafafun na sa ga jiri dake faman 'diban sa amma a haka ya daure yake tafiyar, lokaci-lokaci ya kan
rufe idanun nasa sai ya kuma bu'dewa a take dan ganin hanya da kyau.

Bai damu da halin dayake ciki ba a lokacin, burin sa kawai ya isa gidan sa, ya gansa cikin gidan sa.

Safwan ne ya iso bakin ward 'din da sassarfa, wanda sai yanzun yayi tunanin zuwa duba shi anan 'din dan tun fitar sa hankalin Safwan bai kwanta ba musamman daya ga a halin da ya fita.......sai kuma yayi turus ganin Hafsat tsaye daga waje da mamaki yace " har yanzu baku same su bane?"

Murmushi Hafsat tayi tace " ah no mun same su, kawai mun fito ne dan naga kamar suna bu'katan sarari, ban dai san meke faruwa ba amma naga Noor ta hana Mu'een ta6a jikin Jasmine bansani ba ko wani abin daban ke faruwa".

" Yana ciki ne?"
Safwan ya tambaye ta.
Sai tace " ehh yana ciki".

Bai sake jiran jin komai daga bakinta ba kawai yayi cikin ward 'din da 'dan hanzari, daga bakin 'kofa suka ci karo da Deen dake faman jan 'kafafu at the same time yana tari 'da'd'daya ga jini a hannu da kuma gefen bakin sa amma kuma dan taurin zuciya a hakan ya'ki tsayawa da tafiyar.

Aikuwa Safwan na ri'ko shi sai yayi luu ya fa'da jikin sa, idanun sa lumshewa sukayi nan take.

'Kasa suka zube dukkan su Safwan ne ke fa'din" innalillahi Mu'een meke faruwa ne?"

Noor na jin su amma ko motsin kirki batayi ba daga inda take zaunen sai ma sake kwantar da kanta da tayi gefen Baby ta dauke mata hankali da labarin su Alhaji da uncles 'din ta.

Hafsat dake biyo bayan Safwan ne ta iso ta tarar da su Safwan cigaba da fa'din " dole fa ka tsaya a duba lafiyar ka kaima Mu'een in ba haka ba abin naga 'karuwa yake yi".

Deen kam bai ma san da waye bane sukayi karon sai da yaji muryar sa kafin ya gane shi .

" Me yafaru ne haka wai....a kira likita ya duba shi to idan bazaka iya ba"
Hafsat ta fadi a d'an rikice.

A hankali cikin murya mai kama da ta maye Deen yace " Saf..wan....Nureee".

" Me tayi, me ya faru?"
Safwan ya tambaya a k'agauce".

" Ta'ki kula ni Safwan...ta'ki ta..yafe min..ya zanyi...? idan na mutu ka kula....min da su kaji...dan Allah ka kula min da su...ba zan iya juran fushin ta ba it hurts me....tell her i really love her...i love her...with all of my heart...and...and i was so sorry for all my mistakes...i...i....."
Sai kuma yayi shiru 'dif sai numfashin sa dake fita a hankali.

Hafsat kuwa tsorata tayi da ganin hakan instead ta kalli Deen 'din ah ah sai ta tsurawa Safwan idanu dan jin me ze ce game da hakan.

Shi kam bai ma san tanayi ba domin waya ya ciro cikin hanzari ya yi 'kira domin azo atafi da Deen 'din inda za'a bashi taimako cikin gaggawa.

Mintina biyar mai kyau basu cika ba kuwa sai ga shi anzo.

Kan gadon tura marasa lafiya aka 'daura shi sannan batare da wani 6ata lokaci ba suka wuce dashi cikin sauri.

Tun a kan hanya Safwan ya 'kira Alhaji Baba ya sanar dashi abinda ke faruwa, shima kuwa yanaji duk ya rikice ya tabbatar wa Safwan cewa insha Allahu gobe suna hanya suma.

Duk abinda ya faru a kunnen Noor ne, kuka take jinyi amma kukan ta na yau tana jin ya 'kare, dan tun safe kuka takeyi, har ta gaji da shi, kanta ciwo yakeyi a yanzun tausayin ahalin ta gaba 'daya yake ratsata.

Yini 'daya tak cikin rayuwar su yayi nasaran rusa musu dukkan farin cikin su wanda a kullum take yi musu fatan ya dore har abada,..amma hakan bai faru ba.....yini 'daya tak dukkanin farin cikin su yayi musu 'kaura, sai dai duk da haka al'kawari ta 'daukar wa kanta insha Allahu daga yanzu bazata sake yin kuka ba, bazata sake zubda hawayen ta ba, duk kuwa da cewa a duk lokacin da ta kalli Jasmine ta tuna abinda ya faru da ita, ta tuna ta'asar da akayi mata sai taji wani sabon kukan yana shirin zubo mata ji take inama...inama....inama ana maida rayuwa baya da sai ta bawa Deen mamaki, da sai ta kasance uwa 'daya mai tambari biyu, sai ta kasance abin kwatance a duk inda ta gifta, domin sai ta zamewa Jas uwa da kuma uba gaba 'daya, da bazata ta6a barinta tayi kuka ba...duk da hakama tana ganin bata makara ba, tana jin daga yanzu babu wani shegen da zai 'kara ra6a mata 'yar ta koda kuwa wanene shi, hatta Deen 'din kansa kuwa bata tunanin zai 'kara samun wannan daman, zata je ta rungumi 'yar ta ta kula da ita da tarbiyar ta, ta goge wannan mummunan tambarin da akayi mata, ......dana sanin auren ta da Deen kawai takeyi dana sanin rayuwa dashi dana sanin kasance wa dashi da kuma sonta da kuma yarda da tayi da shi gaba 'daya takeyi ahalin yanzun.

" Wai daman Doctor nada ciwon zuciya ne?"
Muryar Hafsat da taji ta fa'di hakan ne ya sanya ta dawowa daga dogon nazarin da ta tafi, sai tayi saurin bu'de idanun ta.

Four eyes suka yi da Hafsat 'din sai ta kawar da nata idanun gefe.
Ciki-ciki cikin halin ko'in kula ta amsa da fa'din " ummm yana da shi".

Hafsat sai tace
" amma gaskiya baki kyauta masa ba Hudah, shine kin san hakan kuma yazo duba halin da 'yar sa take ciki bayan tayi hatsari kuma sai ki hanasa ta6a ta?
kin san yanda ta6a yarinyar zai sanyaya masa rai kuwa?
anya Hudah kin yi adalci da wannan hukuncin?
Mahaifin ta ne fah?

" That was gone Hafsat....not anymore....yanzu shi ba mahaifin ta bane, ni nan da kike gani ni zan maye mata gurbin sa, ni zan zame mata uwa da uba bata da kowa daga Allah sai ni a duniya nan".
A zafafe Noor ta fa'di hakan cikin dakiya.

Sosai Hafsat tayi mamakin jin kalaman Noor 'din, sosai kanta ya kulle gaba 'daya.
Zama tayi daga gefen ta cikin kwantar da murya tace
" ban fahimce ki ba Huda, ganar dani manufar hakan.... bacin ga mahaifin yarinya nan araye sannan kike wani zance... ko ce miki akayi mutuwa yayi?"

" I said shi ba mahaifin ta bane ko....please ki daina danganta min ya da shi"
Tayi maganar cike da masifa sannan taci gaba da fa'din " bamu da ala'ka da shi har abada".

" Wai saboda menene, what do you mean Hudah bacin ko makaho ya kalli Jas ya kuma kallon Doctor gani na farko zaka fahimci cewa jinin sa ce, me yasa kike son raba abinda Allah ya riga ya ha'da?"

Noor wannan karan shiru tayi tana kallon fuskar Hafsat tsawon mintina uku suna kallon kallo, sannan Noor ta sau'ke ajiyan zuciya gami da fesar da numfashi mai huci cikin sanyin murya tace" bazaki gane bane Hafsat....ke sunan Mu'inudeen kawai kika sani amma sam baki san halin sa ba"

Hafsat kam binta kawai take da idanu yayin da Noor ta juya ta kalli Jas da bacci ya fara daukan ta, kanta ta shafo a hankali sannan ta dawo da kallon ta kan Hafsat tace ".....wai anya kuwa kinsan asalin me ya samu Baby ne?"

Hafsat cewa tayi
" yes nasani mana, they had an accident on there way back home ita da driver ko ba haka bane...."

Murmushin takaici Noor tayi gami da fa'din
" zahiriyya kenan....shi kika sani Hafsat kamar yanda dukkan mutane suka sani...kuma suka shaida."

Da mamaki Hafsat ta kalle ta sannan tace " akwai wani abu ne bayan hakan?"
Chapter 28 · 0% Book details