Sashe 179
Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kai ya 'dab sosa sannan yace" kiyi ha'kuri Ammi naga ai mijin nata ba lafiya sosai gare shi ba..."
" Ya mutu mana shi ya sani ai...ita ma lafiyar bata ishe ta ba jinyar ta zanje inyi bazan iya barin ta ku 'karasar min da ita ba...".
" Ammi kiyi ha'kuri dan Allah kar ki yanke wannan hukuncin wallahi Mu'een na bu'katan kulawa yanzu kuma na tabbata zai canza tunda ga abubuwan da suka yi ta faruwa nasan sazu zame masa izna, ga dukkan alamu ma already yayi nadama ai Ammi..."
Baki Ammi ta ta6e cikin nuna halin ko'in kula ta kawar da kanta.
Ga Noor ya dawo da kallon sa yace" Please Noor ki yafewa mijin ki kuma ki taya ni bawa Ammi ha'kuri...."
Noor tun bata kai ga jin 'karshen furucin nasa bama kuka ya 'kwace mata.
Ganin hakan yasa Ammi saurin fa'din" Baruwan ka da ita Safwan, ku bar min yarinya ta yi numfashi mai kyau dan Allah, ba ita ta aiki mutun aikata abinda yaso ba so bata da alhakin jinyar sa, sam bashi da alamar gyaruwa, ba yau ya fara irin munafurcin nan ba daga baya kuma sai kaga ya koma ruwa dan haka ka barshi...yaje shiya sani nasan akwai ranar da duniya zata juya mai baya, idan ta'kamar shi kyau da Allah yayi masa ne ai mai gushewa ne, kuma kansa yake yiwa mummunan tabo ba wani ba...Jasmine kam sai dai muyi fatan Allah ta mata Rahama kuma ya jira sakayyar ta wurin Ubangiji...idan yace bazai bari ba ma shiyasa ni, yaje can yayi ta haifa ana lalatawa amma kam ba da 'ya ta ba...."
Ha'kuri Safwan ya cigaba da bata amma Ammi kam sai ta 'ki sauraron sa fa'di take ka gaya masa, kar ya kuskura ya tako inda nake matu'kar ba tafe yake da sakin Noor ba, akan wannan sakin har kotu zan iya kaisa, dan bazata sake zaman aure da shi ba..."
Safwan kam wannan karan shiru yayi yana jinjina kansa...ya lura Ammi da gaske take bata sassauta musu ba, d kansa yasan Noor tayi ha'kuri amma ai ba gajiyawa da ha'kuri tunda ba'a san mai gaba zai haifar ba, ha'kuri baya yawa ko da wasa, idan kayi shi da ikhlasi ma sai kaga Allah ya dubi zuciyar ka ya sada ka Rahamar sa.
Ita kanta Noor in ga dukkan alamu rabuwar dole ta zame mata amma ba wai haka ta so ba.
Ya fahimci hakan ne sanadiyyan kukan Noor da ya kasa tsaya wa.
Cuz lokaci-lokaci take share hawaye.
Yana so ya tambayi inda Deen 'din yake amma tsoron Ammi yasa yayi shiru...sai dai ganin har sun kulle gidan ya sashi fahimtar baya ciki kuma babu motar sa agidan koda ya shigo bai gani ba.
Shine ya kaisu tasha da motar sa bayan sun damka makullin gidan hannun Bala mai gadi.
Bai yi wani dogon nazari ba bayan ya sau'ke su sai ya nufi sabon gidan sa da tabbacin yana can cuz cikin kwanakin acan yafiye zama.
Ruf da ciki Safwan ya same shi kan dadduma da alamun tashin hankali, duk ya galabaita numfashin sa na fita da 'kyar.
" Subhanallahi.."
Safwan yayi saurin furtawa tare da 'karasowa kusa dashi.
Da ganin Safwan sai yayi 'ko'karin mi'kewa zaune yana duban sa da jajayen idanun sa da suka 'kan'kance.
" Me ke faruwa ne Mu'een? Me yasa ka taho nan kuma?"
Safwan ya tambaye shi yana duban sa da kulawa.
" Bakomai...kaina ke ciwo".
" Ayyah sannu, na ta 'kiran ka baka 'dagawa hankali na ya tashi sosai..I thought wani abin ne ya faru..".
Cikin galabaita ya bashi amsa da fa'din" wayar na can gidan ne .."
" Ohh..yanzun nan na sau'ke su Ammi me yasa baka je kunyi sallama ba har suka wuce? Naga ma har da Noor suka tafi...".
Rintse idanun sa yayi da 'karfi yana jin ciwon tafiyan da Noor tayi ta bar shi...
Idanun sa a lumshen muryar sa na rawa ya furta"...Ammi bata..so..na yanzu Safwan, Ammi na...da kanta tace in...sakar mata Noor, Ammi tace bazata sake..ba..rin ta zama tare dani ba, Safwan zan cinye ta ne? Ban san ya zanyi da Ammi su gane cewa nayi nadamar gaskiya ba, wallahi da kaina Allah wadai nake da rayuwa ta ta baya, me yasa suke tunanin zan sake maimaitawa?
Ina son Noor sosai, i can't let her go just like that batare da na bata farin cikin da ta rasa atare dani abaya ba,
Safwan wannan ma laifi ne please?"
Kai Safwan ya girgiza tare da fa'din" Ka kwantar da hankalin ka komai zai wuce insha Allah.."
" Ni dai ka taimake ni ka dawo min da ita Safwan, ka bawa Ammi ha'kuri ta dawo min da Mata ta....".
Kasa 'karasa maganar yayi kawai ya dafe kansa da yake jin yana sara masa sosai, Safwan kam duban sa yake yi cike da tausayawa, shi al'amuran Deen 'din yanzu duk sun fi 'karfin tunanin sa, ha'kika yasan a yanda Ammi ta ji labarin halin sa daga bakin sa ya kuma ga yanayin ta 'dazun ya tabbatar abu ne mai wahala ta sake barin Noor zama da shi tunda har kotu yaji take ambata, sai dai bazai fa'di wa Deen hakan ba saboda gudun kar ya 'kara masa wani ciwon akan wanda yake ciki.
Sam bai ga laifin Ammi ba, domin ba ita ka'dai ba duk iyaye idan suka tsinci hakan cikin rayuwar 'yar su dole ne yasan sai sunyi wani yun'kuri...sai dai ai shima Deen in a yanzu yana bu'katar agaji kuma iyayen sa su ya kamata ace sun tsaya masa wajen ganin lafiyar sa ta samu me yasa duk zasu guje shi akan kuskuren da ya aikata?"
A fili kuwa" Allah ya kyauta" ka'dai ya furta tare da sakin ajiyan numafashi.
Tare suka fito da Safwan inda ya sauqe shi a 'kofar gidan sa tare da kwantar masa da hankali cikin nutsatstsiyar murya da kalamai masu sanyi inda ya tabbatar masa da cewa ya bari ya 'dan basu chance zuciyar su tayi sanyi nan da 2weeks zasu je da shi su 'kara basu ha'kuri.
Girgiza kai Yah Deen yayi yana duban fuskar sa yace" Bazan iya ba Safwan, 2weeks yayi min yawa mu tafi gobe..".
" Kayi ha'kuri dai, komai cikin natsuwa yafi, kuma nafi son ka warware da kyau tukunna don kaga yanzun halin da kake ciki kaima kana bu'katan hutu".
Shiru kawai yayi masa yana jin sa ba wai dan zancen nasa ya shige shi ba sai dai kawai ba yanda zaiyi da Safwan
Maganar ma 'karfin halin yin ta yake yi amma sosai yake jin babu da'di...kuma ga alama kowa ba fahimtar halin da yake ciki suke yi ba, ga dukkan alamu shi ka'dai yasan ciwin da ke zuciyar sa, sam gani yake komai ya yi masa duhu musamman da yasan a yanzu Noor bata tare da shi.
Daga 'karshe Safwan tabbaci ya bashi na cewa Insha Allahu zuwa dare zai zo ya sake duba shi, da haka suka rabu Safwan ya wuce inda zashi.
Mai gadi na ganin sa ya taho wurin sa da sauri-sauri yana gaida shi, key 'din da su Ammi suka bashi ya bawa Yah Deen cike da girmamawa.
Hannu ya sa ya kar6a sannan ya nufi ciki da tuanin da gaske kenan ta tafi... 'kafafuwan sa ma da 'kyar yake iya 'daga su, dishi-dishi yake gani sosai, ya san koma menene ya faru ga rayuwar sa shine sanadin komai, yau gashi gidan sa babu kowa sai shi ka'dai, bai ta6a tunanin irin wannan ranar na zuwa masa bazata kuma kwana kusa irin haka ba.
Baby ta rasu ta tafi ta barshi yayin da Noor ta guje shi batare da ta tsaya ta saurari amincewar sa ba....
Haka ya bu'de 'kofan parlourn ya shiga yana rarraba idanu, kwanaki 'kalilan da suka gabata idan ya shigo gidan da gudu Jasmine ke zuwa wurin sa tana dariya take yi mai oyoyo Daddy..inda yake 'daga ta sama yana dariya haka itama...idanu ya lumshe ya kuma bu'de su nan take...lokacin yana 'ko'karin zama kan kujera...ya furta Allah ya ji'kan ki Mama na, Allah yasa ki kasance me ceton mu, duk da nasan ban cancanci hakan daga gareki ba.
Bayan sa ya kwantar tare da 'dago 'kafafun sa ya mi'ke yana lumshe idanu.
Tunani ne fal aransa amma duk ya rasa wanda zai sanyayar masa da zuciya...
Haka ya yini shi ka'dai agidan batare da ya ko iya saka ruwa abakin sa ba, kusan la'asar ya fara jin zazza6i sosai ya rufe shi jikin sa na ta kakkarwar sanyi, motsin kirki ya kasa ballantana ya samu damar jan abincrufa ya rufe jikin sa da shi, tunda ya kwanta bai sake ko motsin kirki ba har yanzun da fever ya ratsa shi.
Fat-fat yake jin 'kirjin sa na bugawa ji yake tamkar dutsi aka aza masa akan zuciyar sa, ga ciwon kai ga zazza6i...cikin hakan ya fara amai kamar zai amayar da hanjin cikin sa, dayake cikin sa babu komai sai hakan ya 'kara galabaitar da shi..jikin sa babu 'karfi ko ka'dan.
'Kasa ya dawo ya kwanta yana maida numfashi sama-sama gwanin tausayi.
Gashi gidan babu mai taimakon sa, mai gadi ne ka'dai a harabar gidan shima in kuma bai san abinda ke faruwa da shi ba balle ya taimaka masa.
Da 'kyar ya samu numfashin sa ya daidaita sannan ya mi'ke ganin jiri na 'diban sa yasa ya fara dafe bango da hakan ya samu ya isa bathroom.
Sai da yatsaya ya dinga sau'ke numfashi anan in ma sannan ya samu ya tsaftace jikin shi, ya 'dauki tsawon lokaci a hakan kafin ya samu ya fito boxer da rigar jallabiya kawai ya iya sanyawa ya sallaci La'asar ko azkar bai iya jerowa ba ya cire jallabiyan saboda ji yake tana takura sa haka ya koma ya kwanta tare da jan abin rufa ya lullu6e jikin sa da shi har zuwa kansa gaba 'daya.
Saman abin rufan idan ka ta6a zaka iya jin 'dumin daya 'dauka sanadiyan zazzafan zazza6in dake jikin sa a lokacin, rawar sanyi kawai yake yi ha'koran sa na karo da juna.
Safwan bai dawo gidan ba sai 'karfe biyar, koda ya shigo ma haka ya dinga doka sallama amma babu wanda ya amsa shi.