← Book details Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 75 OF 211

Sashe 75

Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haka Husnah ta sha maganin bata san na menene ba, awa 'daya bayan haka cikin ta ya fara ciwo sosai kamar zata mutu, lokacin da ta ga jini ya fara fito mata sai hankalin ta ya 'kara tashi, da 'kyar ta daddafa ta shiga bayi anan ciwon ya ci 'karfin ta gashi ita ka'dai ce a gidan Yah Deen baya nan.

Kafin ace kwabo kuwa har jinin ya fara bin 'kafafun ta,  'kara rikicewa tayi ga ciwo ga tashin hankali, a bayin ta zube tana rizgan kuka.

Allah ma sai ya taimaka bai dade ba ya dawo gidan ashe daya bata maganin masallaci ya tafi, jin kukan sautin kukan ta ne ya sanya shi hanzarin garzayawa 'dakin ta, bata 'dakin amma yajiyo kukan daga bathroom, hakan yasa ya 'karasa jikin bayin ya 'dan yi knocking tare da 'kiran sunan ta.

Tana jin muryar sa sai ta sake sakin wani kukan tana fa'din" Mutuwa zanyi ni kam Mu'een ka taimake ni".

Saurin tura 'kofan yayi yana fadin " Subhanallah Husnah"!

Ganin ta kwance 'kasan tiles 'din bayi kaca-kaca da jini ne ya sanya shi rikicewa shima...tsugunne yayi gaban ta yana 'ko'karin tallafan ta amma Husanh kam ina ji take kamqr an tsagata biyu, kukan ma daina fita yayi dan azaba, hawayen ta ma ya 'kafe yayi ga bakin ta da yayi ja saboda kukan da ta sha, ban da " Waiyo Allah!....waiyo Allah!!, zan mutu, Abbah na..waiyo Allah"...babu abinda take iya fa'di shi 'din ma a wahale take furta shi.

Sosai Yah Deen ya tausaywa halin da take ciki, har yayi tunanin kaita asbiti amma sai yayi tunanin a wani matsayi kenan hakan, tsoro sosai ne ya kama shi da ya tuna cewa yin abortion na iya kashe mutum, tsoron idan ta rasu agidan sa kallon da za'ayi masa, me ma zai ce da iyayen sa da kuma nata iyayen?.

Tashi yayi tsaye cikin tunani amma bai iya tsawaita hakan ba ya kuma tsugunnawa gefen ta" sannu" ya ringa jera mata sau ba adadi, cikin ransa yake Addu'ahn Allah ya takaita musu.

Bayan tsawon lokaci sannan cikin ya fita bayan taci uwar wuya shi kansa Yah Deen din sai da ya fita hayyacin sa.

Da 'kyar ta samu ta kintsa kanta wanda sai da Yah Deen ya saki ajiyan zuciya.

Basu je asbitin ba har sai da aka kwana uku kafin sukaje nan aka tabbatar musu da cewa ciki kam babu shi ya fita.

Sai a wannan lokacin bayan sun dawo yake sanar da ita abinda ya faru.

Tayi murna 'kwarai da fitar cikin duk da kuwa tasha azaba amma ita aganin ta rabuwa da cikin shine dai-dai in haka ba ta ina zata fara tunkarar iyayen ta da batun bata san me zata ce da su ba.

Haka tayi ta gama jinyar kanta har ta koma dai-dai, da warkewar ta kuwa ya nemi su sake komawa irin rayuwar su ta baya, anan Husnah ta nuna 'kin amincewar ta yayin da tsoro ya bayyana kan fuskar ta 'karara.

Duk yadda yaso ya lalla6a ta da cewa da 'din ma bai tuna bane har ya bari ciki ya shiga amma yanzu ba zai sake kuskuren hakan ba...Husnah ta'ki yadda wataran kuwa ce mata yakeyi idan an ha'da kaza da kaza aka sha to cikin ko fara zama ba zaiyi ba zai fita...nan ma Husnah taki amince masa duk ta'ki yadda, har misalai yake buga mata ya nuna mata a wayar sa har cikin laptop 'din sa amma a banza, ta kan barshi yayi duk yadda yake so da jikin ta amma bata ta6a bari ya shige ta, da ya 'dauko hanyar hakan saita bijire ta tashi ta bar shi.

Da abin ya ishe sa ne sai ya sata gaba suka je akayi mata allura... tun daga ranar suka 'dora daga inda suka tsaya dan kuwa sosai suka jarabtu da juna shiyasa ma  suke abinda ran su ke so batare da damuwar komai ba musamman da Husnah ta san cewa yanzu an mata katanga da daukan ciki.

Haka suka ci wannan semester kaf suna sha'anin su, dan daga baya ma Husnah da kanta take zuwa tayi allauran, sai da akayi hutu kafin suka rabu Yah Deen ya koma gida.

Ni kuwa daga ranar da ya dawo to nima daga ranar damuwa ta take farawa.

Zuwa yanzu na tsani ganin sa har cikin raina, ji nake dama ya mutu a wancan lokacin da bashi da lafiyan nan kowa ya huta da masifar sa.

Kwanan sa yau uku da dawowa amma kwata-kwata sau biyu kacal na ha'du da shi, ba'a kuma gayyace ni aiki ba da yake wannan karon tun kafin ya iso ta tura ni da mai aikin ta, Saif ma ya raka mu da yake sun zo hutu muka je muka gyara masa ko'ina.

    Har kwana uku bayan dawowar sa babu abinda ya 'kara ha'damu da shi, har hankali na ya fara kwanciya da ganin hakan na fara sakin raina.

Kwatsam ranar wata Talata bayan nayi shirina tsaf na fito da niyyar tafiya islmiya, da yake yanzu su Saif ko sun zo hutu basa zuwa shiyasa ni ka'dai nake tafiya ta, Uniform 'dina yasha guga ina tafiya ta a hankali na rungumi takaddu na da sallaya a kirji na, dai-dai 'kofar fita daga gidan sai muka ha'du dashi, da sauri nayi baya ka'dan kaina 'kasa 'kirji na na dokawa nace " Sannu da zuwa ".
Bai amsa ba sai yace da ni" sai ina kuma?"
"..ni..ni?"na tambaye shi da rawar murya sai yace " a a ni"!
"..Islamiya zan tafi".

" Munafuka ashe kin jini".
Ya fa'da tare da wuce ni ka'dan kamar zai tafi sai kuma ya waigo..." akan me ma muka rabu da ke?"
"..babu komai"
Na bashi amsa da sauri sai yace
" shara fa? Ko kin manta?"
'Daga idanu na nayi na kalle shi sai naji hawaye na taruwa min da sauri na maida kaina 'kasa kamar zan yi ihu saboda takaici.

" Aikin ki zai fara daga gobe...kinji baki ji ba?"
" Naji"
Na bashi amsa da muryar kuka.
Shi kam bai damu ba sai ma ya taka yayi gaba abin sa.

    Raina ajagule har na isa islamiya duk da na tuno Ma'u amma duk da haka hankali na ya kasa kwanciya.

Ai kuwa ban shiga aji ba sai da na tabbatar na ha'du da Ma'u, ga mamaki na ita kam da jin abinda nace sai ta saki murmushi abin ta tace min in kwantar da hankali na zata ringa taya ni.

Sai a lokacin na 'danji dama-dama har ma na samu na nutsu a aji muka yi karatu.

     Da yake ana hutun makaranta yanzu sai nace da Ammi zanje in gaida Ummah na, nan kuwa Ammi tace Saif ko Zaidu wani ya raka ni...Zaidu kam sarkin ba'kin hali take yace shi kansa na ciwo ba zai iya fita ba....Saif kuwa cewa yayi in bari mana gobe sai muje shi yau agajiye yake jin kansa.

Ni kam ma duk hakan yafi min dan bana son wanin su ya san inda zanje balle har su gayawa Ammi.

  Haka na tafi Ammi na fa'din in gaida su nace to zasu ji...

Da fita ta sai na wuce gidan su Ma'u...ban ma zauna ba dana gaida matar baban ta kawai sai ta suri mayafi muka fito da yake tasan kwanan zancen...ita fuskar ta wasai idan kin ganmu yayin da ni nake nan kawai zanje ne dan babu yadda na iya.

Muna 'ko'karin shiga sai ga Imrana nan yana fitowa daga gidan sai muka bashi hanya ya 'karasa fitowa....idanun sa 'kyat akan Ma'u mu kuwa gaida shi mu kayi tare da shigewar mu ciki...Imrana sai ya bimu da idanu.

Yah Deen na kwance abin sa tsakiyar gado da yake akwai 'dan sanyi a lokacin shiyasa bai fito ba.

   Ni dai ban damu da ganin sa ba sai naji ma hakan yafi min har Allah-Allah nake yi mu kammala mu wuce kafin ya fito.

Har kuwa muka kammala bai fito ba, ina murnar zamu tafi sai naji Ma'u ta 6aro min wani aikin wai " cikin baza'a gyara ba?"
'Bata rai nayi nace " yana fa ciki".
" To ke ina ruwan ki da shi ba aiki kawai zamu yi ba?
Baki na tura nace " ni gaskiya tsoro nake ji".

Ma'u kam hannu na ta kama da nufin mu shiga sai na wafce hannu na da sauri nace ni ki kyale ni, ke 'din kije in kin sharewa sai ki zo mu tafi.

Ma'u kam bata damu ba ta 'dauki tsintsiya ta nufi 'dakin ta shiga ni kam sai na yi zama na a parlour ina jiran ta gama mu wuce gida.

Koda ta shiga sai ta same shi kwance amma bai rufe kansa ba, ashema duk yana jin mu sai da yaji zata shigo ne sannan ya 'dan lumshe idanun sa.

Yana ganin sanda ta shigo ta kalle shi, ganin kamar yana bacci ne yasa ta da san'da-san'da ta isa gaban sa ta tsaya tana 'kare mai kallo, shima kuma haka, yarinyar ba laifi tana da kyau a hakan ya 'karewa fuskar ta da jikin ta kallo, shai'dan sai ya 'kara 'kawata masa siffar ta gashi dama ba 'karamin missing Husnah yayi ba.

Yi yayi kamar zai motsa sai tayi saurin tsugunnawa ta fara shara.

Haka ya dinga binta da kallo idan zata waigo sai ya lumshe idanu yayi luf kamar mai bacci motsin kirki bayyi da jikin sa.

Har ta kammala sharar ta fita bai motsa ba, ni kuwa ganin ta kammala ta fito yasa nayi saurin mi'kewa harma na riga ta barin parlourn ta biyo ni a baya tana murmushi take fa'din " matsoraciyar banza".
Yah Deen kuwa sai da ya tabbatar ta fita sannan ya taso ya koma parlour ya zauna....Kamar wasa ya 'daga wayar sa ya dannawa Husnah 'kira tana 'dauka ya zaiyano mata 'karya da gaskiya na halin da yake ciki da  kewar ta da yayi.
Chapter 75 · 0% Book details