Sashe 139
Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Anty takaita dariyar ta ta tayi sannan cikin kwantar da murya tace" Ai to ba abin damuwa bane, ki kwantar da hankalin ki kinji?, kinsan koma miye ne yake faruwa Allah bai 'dauke matsayin sa akanki ba ko da 'kwayar zarra still shine dai mijin ki, dole ne kuma kiyi masa biyayya kinsan shine aljannar ki ko?"
'Kasan ma'koshi na amsa da" Umm".
Sai tace" Yauwa kin gani...ai ni hakan ma da yayin ba 'karamin birge ni yayi ba, ko ba komai yanzu nasan ya damu da ke, kin san ya za'ayi?"
Nace" a a?"
Anty sai tace" Yanzu ki gayawa Addan ki cewa yace ki koma gobe ai bazata hana ki ba nasani sai ki shirya ki taho zamu yi waya daga baya kinji..?"
" Uhum" nace da ita sannan na ajiye wayar raina ba'ki'kirin, ni ba haka naso ba sam.
Ko da na sanar da Addah ta ma da mamaki ta tambaye ni cewa da kansa kuma yace ki koma?"
Nace mata" Erh shi ne ya 'kira ni jiya ya fa'da min".
Ina maganar kamar zan fasa ihu saboda haushi.
Sai naji tace
" To ai shikenan tafiya ta kama ki".
" Ni wallahi Addah banso.in tafi yanzu".
Na yi maganar kamar zan saki kuka sai tace" Dolen ki ai, kinsan ni ba goya miki baya zanyi ki aikata son ranki ba".
Da fa'din.hakan.sai ta fice ta barni cikin 'dakin.
Haka ina ji ina gani Addah ta shirya min kaya na na taho ba dan raina ya so ba.
Ai kuwa gidan Ummah ta na sau'ka waya kawai nayi da Ammi na sanar da ita dawowa ta, ko Anty Zainab ban 'kira ba dan haushin yau bata goyi baya na ba.
Shi 'din kuwa 'kin 'kiran sa nayi duk da kuwa yace da ni idan na dawo in 'kirasa amma na share shi har sai can bayan sallahr Isha'i kafin na 'kira sa lokacin ma har na gama shirin bacci zan kwanta.
Da ganin ya 'dauka na gaida shi tare da fa'din" Na dawo".
A ta'kaice.
" Dan baki da sence kuma sai kika jira har dare sannan zaki taho?"
Take sai nace
" a a fa ni tun 'dazu na dawo".
Yace
" Kuma shine yanzu zaki gaya min?"
Nace
" Mantawa nayi ne..."
Tsaki yaja sannan ya kashe wayar sa.
Ni kam baki na ta6e a fili na furta" _Almasifatu_ "
A hakan ne Addah take tunanin watarana zaka canza? Hmm so take in mutu kawai a hannun sa wannan me kai biyun kam ba canzawa zai yi ba...cikin zuciya ta nayi wannan tunanin a fili kuwa baki kawai na ta6e.
Washe gari kuwa na shirya naje na gaida Ammi na da Alhaji Baba.
Yini nayi da Ammi sannan da yamma na koma gida.
Sai da na kwana biyu da dawowa kafin na fara zuwa makarantar har ranar kuwa ban kuma waya da shi ba...ai kuwa karatu ya barni sosai a makaranta balle gashi SS class muke yanzu abin ba sau'ki dole na na dukufa da karatu dan kar abar ni abaya...gefe guda kuma Ammi na yawan cewa da ni na 'ki ta yanzu, wanda ni kaina bansan me yasa yanzu na fi jin da'din zama a gidan mu ba..gidan Ammin ne yazama shiru yanzu ba da'di ba su Saif gidan shiru ita ka'dai take yini abin kuma ya fara isanta.
Da kaina na fara jin tausayin ta kuma sai na yi tunanin dawowa gidan kawai, banyi maganar da kowa ba na dai bar shi cikin raina, kafin in sanar da Ummah ta kuma sai Ammi ta riga ni, ai kuwa Ummah ta tace maza in shirya in koma gidan miji na, dama ai rasuwa ce kuma ta jima da shu'dewa, tace zaman mace 'dakin mijin ta shine darajar ta.
Ni dai bance da Ummah ta komai ba, tunani nake cikin rina, cewar indai wancan 'dakin da yaci sunan nawan ne ma take tunanin zan koma ni kam har abada na yafe shi, bana jin zan iya sake rayuwa cikin wannan gidan da ya kasance wurin aikata masha' a tun kafin zuwa na..ina.babkashevkaina nake son yi ba bazan koma can ba cuz ni ka'dai nasan me nake ji cikin zuciya ta game da gidan, to tuno shi nayi ballnatana ace in sake rayuwa cikin sa, abu ne da har yau banga alamun zan iya mantawa da shi ba.
Duk da yake ita ma Ummahn nasan ba can 'din take nufi ba amma cewa da tayi gidan mijina ya sa ni zurfafa tunani akai tunda nasan can 'din shine gidan mijin nawa, kuma nasan Ummah ta baza ta6a cewa dani in koma wancan gidan ni ka'dai ba dan haka ko da na shirya kaya na sai na koma gidan Ammi muka cigaba da zaman mu.
Ko guda daga cikin kulan da take min kuwa bata daina ba, sai abinda ma ya 'karu...Alhaji Baba ma kan yawaita yi min kyauta ta musamman ni da kaina nasan iyayen Yah Deen na 'kauna ta sosai.
Kwanaki na goma sha uku da dawowa gidan Ammi sai ga Yah Deen ma ya dawo wai ya kammala karatun sa gaba 'daya.
Ni dai bazan ce ga yanayin da na shiga da dawowar tasa ba amma har zuciya ta na taya shi farin cikin kammala makarantar da yayi.
Tun dawowar sa kuwa maganar kirki bata ha'da ni da shi ba, saboda bai ma wani zauna ba, ya kan yawaita yin 'kananun tafiye-tafiye amma duk da hakan ranar da akace yana gari kuwa ranar bana yin yinin farin ciki, na kan tsinci kaina cikin rashin sukuni musamman saboda wani salon tsareni da ya fara wanda ban san dalilin sa ba, Allah ma ya taimaka ni 'din ma ba gwanar shiga sabgar da bata shafe ni ba ce shiyasa ba kasafai lamari ke ha'da mu ba.
A yanda na fahimta ma sai naga tamkar ni ka'dai yake wa hakan, tamkar mai jin haushi na, duk dama ko a wurin Ammi yake ba kasafai zaki ga suna hira kamar da ba amma da sau'ki akan innice tare da shi sai na rasa dalilin wannan canjin.
Gani na abin farin ciki ne ya same shi daya kamata ace yafi kowa nuna farin ciki amma 6angaren sa kam abin ba haka bane.
Sai nake tunanin ta6 ashe kuwa zamu da'de mafarkin Addah bai tabbata ba in dai Yah Deen ne, mutun da kullum halayen sa canzawa suke yi gaba 'daya sai ka kasa gane inda ya dosa.
Ban sani ba ashe hakan na faruwa ne sanadiyyan tsintan kansa da yayi dumu-dumu cikin so da 'kauna ta, sai yake ganin in ba haka yake min ba tamkar abin zai girmama ne a zuciyar sa shi kuma baya so kowa ya fahimce shi domin ayanda yake ji 'din idan yace zai bayyana soyayyar da yake min kowa dariya zai masa musamman su Anty Zainab hatta Ammi yasan sai ta masa dariya bayan duk iyayin da yai ta musu akaina.
Kafin cikar 3weeks da dadowar sa kuwa wai sai ji muka yi har zai fara aiki da wani abokin Uncle Ja'afar cikin garin Bauchi.
Comment
Vote
Share
*Salmerh ce* 😍
💕 *NOORUL* 💕
(Haske nah)
By
*Salmerh MD*
*Wattpad @*
*Serlmerh-md*
💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*
_*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_
*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*
🅿 *67*
Sosai nayi farin ciki da samun wannan aikin nasa dan ko ba komai zan huta da ganin sa, nima in sake kamar kowa ma.
Abin mamaki da lokacin tafiyar tasa tayi kuma sai Alhaji yace wai dole tare da matar sa zai tafi jin wannan labarin sosai ya 'daga hankali na bada wasa ba.
Kamar wasa sai gani nayi Ammi ta fara shiri gadan-gadan, ragowar akwatina na da kayayyaki na dake can gidan tasa wai akwaso, da tace ma wai da ni za'a je can 'din amma tun daga lokacin kuka na ya 6alle ina fa'din ni bazani gidan ba, duk yadda Ammi ta so aje da ni wai ko zan duba wani abin amfani na 'kin zuwa nayi sai turawa tayi akwai aka 'debo mata kayan bisa jagorancin Yah Deen.
Shi kam da yake yana zargin kansa ne bisa dalili na na 'kin zuwa sai bai damu da shiga maganar ba gudun kar allura ta tono garma.
Ni kuwa sam kuka na sai ya kasa tsayawa yinin ranar kuwa kaf haka na sa Ammi gaba da kuka ina fa'din ni ba matar sa bace bazan bisa ba.
Ammi ko kula ni ba tayi ba har sai yamma sannan ta zaunar da ni tayi ta lallashi na da ban baki harda al'kwarurruka tayi min akan wai da kanta watarana ma zataje ta duba ni in tana raye...tace kuma koda wasa naga abinda bai min ba ko kuma ya aikata wani abin wanda raina bai kwanta da shi ba in 'kira in gaya mata uban sa zata ci...taceckovwaya naga yana yi da wata macen in sanar da ita sai taji dalili.
Ni kam bance da ita komai ba, damuwa ta ni kawai a yanzu shine inji ance bazan bishi ba.
Abakin Ammin ma nake jin wai za'a kwashe kayan kitchen 'din mu na wancen gidan a tafi mana da shi can Bauchin, ni kam baki na ta6e na kauda kaina.
Ko ranar da za'a 'dibi kayan ma ba yadda Ammi bata yi da ni akan muje ba sam na'ki, Yah Deen ne ya sau'ke ta gidan dama lokacin da Ammi zata tafin da na'ki binta sai naga ya sa kai yayi gaba inda ya jira ta a waje har ta fito.
Yana sau'ke ta ba'ajima ba ya dawo gidan, da shigowar sa kuwa bai zame ko'ina ba sai cikin 'dakin Ammi da yake bai ganni a parlour ba.
Lokacin da ya shigo ina bayi ban san ya shigo 'dakin ba dan haka skirt 'di na a sama na fito ban sau'ke shi ba, da fitowa ta ne sai na ganshi tsaye ya wani cika iska cikin bakin sa take kuwa na sau'ke skirt 'din nawa cikin sauri har da jan shi sosai zuwa 'kasa.