← Book details Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 164 OF 211

Sashe 164

Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sabbin hawaye taji suna gangaro mata, a hankali tace da ita" Kiyi ha'kuri Mama na ni bani da ikon rama miki amma nasan Allah da kansa zai miki sakayya akan duk wanda ya zalunce ki kinji Baby na?"

Jasmine kanta ta 'dage sama alamar" Erh".
Noor sai a lokacin ta iya sakin jikin ta, tana shafa kanta tace" Baby..."
Kallon ta Jasmine tayi batare da ta amsa ba.
Itama bata damu ba kawai ta cigaba da fa'din" Dama Sani ya ta6a yi miki irin tsarkin nan shine baki ta6a gaya min ba ko?".

Kai ta girgiza mata sannan tace" A a Mummy..yau ne kawai ya min tsarkin kuma ai Mummy ban yi fitsari a school ba".
" Bai ta6a saka miki hannu a wandon ki ba?"
" Erh Mummy...kullum baki na kawai yake cinye min idan ya 'dauke ni a cinyan sa sai ya 'dora ni akan wani abu, kuma yace kar in fa'da ma kowa hadda Daddy ma".

Tana jin ciwon abin cikin zuciyar ta amma dole ta danne saboda tana taji komai, tana so tasan ta inda ya kamata ta fara dawo da tunanin Jasmine ya zam dai-dai irin ta yara.
Dan haka sai ta ha'diye duk abinda takeji.

Rufe mata jikin ta tayi zuwa cikin ta da abinda ake lullu6e ta da shi sannan ta sake dawo da hannun ta kan Baby tana shafawa tace" Baby na...kullum kuma Sanin yake 'dora ki a cinyar tasa?"
Kai ta 'dage sama.
" Kuma har yake cinye miki bakin naki kullum?".
Da yake bata da wayo sai ta 'dage kanta sama alamar Erh tana mai turo baki gaba.
Noor sai tace
" Shiyasa ashe nake ganin bakin naki wani iri amma ai Baby idan na tambaye ki 'kin gaya min kike yi".
Shiru Jasmine tayi tana kallon idanun mahaifiyar tata...ganin.hakan yasa Noor fa'din" Ko tsoro kike ji idan kin fa'da min kar in do ke ki.." A a Mummy ai Sani yace kar in fa'da miki da Daddy, kuma ai Mummy kin hanani surutu ko..."
Rintse idanu Noor tayi wani mahaukacin suka taji cikin zuciyar ta, ha'ki'ka ita da kanta tasan ta aikata hakan, a lokacin da take tsaka da damuwar Yah Deen, sosai ta tsani wata damuwar kuma shiyasa take hana Baby yawan yi mata surutu, amma bata ta6a sanin cewa babban kuskure ta aikata ba sai yanzun da lokaci ya riga ya 'kure mata bayan anyia rayuwar 'yar ta Babbar illah.
Ha'kika tayi babban asara tayi sake a rayuwar ta ta tafka kuskure, kuskure mafi muni da ya kaita ya baro, bata ja Baby ajikin ta ba saboda rashin natsuwa gashi wanda take abin domin san ma bai san tana yi ba, bata ci wata riba face 'karin takaici tunda gashi abinda idanun ta ya sake gane mata a karo na biyu.

Bata ta6a jin dana sani irin na yau, ji taka da tasan wannan 'kaddarar na tafe cikin rayuwar su da wallahi mantawa zatayi da soyayyar Yah Deen ya tayi jifa da batun makarantar ta ta dan kawai ta bawa Baby kulawar da ta dace, amma ina ba dama, da kanta ta hana kanta sauraran surutan Baby, ta 'ki.janta ajiki balle taji damuwar ta, ta 'ki warewa kanta lokacin da ya kamat su zauna da Baby su sha'ku ganin cewa ta samu soyayyar mahaifin ta a dili shikenan tayi watsi da nata 6angaren, ba ta wani damu ba tunda aganin ta ai tana son.abin ta tunda ta haifa so ba sai ta nuna mata kulawar zahiri ba, a ganin ta yanda suke rayuwa a hakan ya wadatar bata san ashe abubuwa da dama ke cikin zuciyar yarinyar ba, da ya ha'du da garga'din sani kuma sai ya kasance ko Yah Deen 'din ma bata iya sakewa ta sanar da shi halin da take ciki ba.

Bu'de idanun ta tayi akan fuskan Babyn a fili ta furta" Yah Allah ka yafe min, ka yafe min cin amanar da na yiwa rayuwar Jasmine.

Ha'da idanu suka yi da Baby sai ta 'danyi mata murmushi sannan ta tataro dauriya ta sanyawa muryar ta a hankali" Daga yau Duk wanda ya sake yi miki abu ko wani iri ne ko zagin ki mutum yayi kizo ki fa'da min kinji Baby..bana sake fatan faruwar wani abu amma ko hannun ki mutun ya gwada kamawa kizo ki gaya min kinji Mama na".
" Sani yace zai yanka min ciki na da wu'ka idan na fa'dawa Daddy".
" Kar ki damu ba ruwan ki da su Sani yanzu, bama ganin ki zai sake yi ba insha Allahu, ni zaki na gayawa duk abinda akayi miki kinji ko?"
" Toh Mummy...amma kice kar ya yanka min ciki na nima".

Murmushin 'karfin hali tayi mata gami da jinjina mata kai tana shafo fuskar ta.

Tana nan tana jan Baby da surutu har gari yayi haske ma'aikata suka shigo suka yi aikin su bayan sun yi mata ya jiki tsaf suka gyare wurin kafin suka fita.

*****
'Bangaren Safwan kuwa bai dawo da wuri ba dan ko daya gama abinda yake ma sai da ya jira Hafsat ta ha'dawa su abin kari kafin ya fito a gidan, daga nan kuma sai ya biya gidan Mummy (mahaifiyar sa) ya sanar da ita abinda yake faruwa kafin ya 'karaso asibitin.

Mummy kam hankalin ta tashi yayi sosai, duk abubuwan da ke faruwa ko 'daya bata da labarin su sai yanzu da Safwan ya biya ya gaya mata...haka suka rabu da al'kawarin itama yanzu tana tahowa, Allah sarki Safwan duk da take matsayin mahaifiyar sa amma bai fito fili ya sanar da ita ainahin abinda ya faru ba, ya dai ce mata ne kawai Jasmine na asbiti sun samu accident jiya ita da drivern ta amma bai gaya mata abinda Sani yayi mata ba.

'Karfe takwas da mintina kafin Safwan ya dawo asbitin inda yazo musu da sa'kon Hafsat kan cewa itama anjima ko zuwa yamma zata dawo.

Sai da ya duba Baby yayi mata abinda ya dace kafin ya fita bayan ya sanar da Noor abinda zatai mata, warm wata yace ta sanya ta ciki na 'yan mintina saboda kumburin jikin tan, sai Noor tace da shi ai ta sanya ta ma tun 'dazun har tayi fitsari ma.

Take ya nuna farin cikin sa gami da godewa Allah cikin ransa da irin kulawan da Noor tayi da Baby, shaf ya mance ne kafin ya tafi bai sanar da ita hakan ba, da yake ma bai shige ta ba so ba bu'katan sai anyi mata aiki a hankali in ankula komai zai daidaita.
Da gama wannan tunanin ya fita ya basu wuri dan su samu daman sanya abu a cikin su.

Tea mai kyau Noor ta ha'da musu sai da ta bawa Baby sannan itama ta sha, dukkan su bawani abun kirki kuwa suka shaba cuz cup 'daya da ta ha'da musun ma sai da ya rage basu shanye ba.

Comment
Vote
Share

*Salmern ku ce* 😍

💕 *NOORUL* 💕
(Haske nah)

By
*Salmerh MD*

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

_*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

🅿 *76*

Safwan da barin inda suke 'din sai ya nufi 'dakin da aka kwantar da Deen, shi ka'dai ne 'dakin sai na'ura da aka sanya masa a hancin sa, hannun sa kuwa canular ne da tun jiya aka cire drip 'din da aka jona masa bayan ya 'kare.

Ko motsi baya yi amma kuma idanun sa gefe da gefe hawaye ne ke bi a hankali, hakan ne ya tabbatar masa da cewa Mu'een ya farka daga suman da yayi... _Alhamdulillah_ ya furta a fili yana me 'karasawa bakin gadon.

Hannu yasa ya cire masa abin hancin tare da zama gefen sa yana 'kiran sunan sa cikin natsuwa, bai amsa ba haka kuma bai bu'de idanun sa ya dubi Safwan ba illah hawayen sa da suka cigaba da tsiyaya sai dan wannan karon cikin turereniya wani ke bin wani.

Ko ba'a fa'da masa ba ya san zuwa yanzun kowa ya tsane sa, kowa ya riga ya san mugun halin sa da ke 6oye...kunyar Safwan yake ji mafi tsananin kunya, domin Safwan ba sau 'daya ba ba sau biyu ba yake yawan yi masa tuni akan illar Zina, Safwan sosai ya so yaga rayuwar gidan sa ta daidaita ko dan yadda da yayi da natsuwar Nuree yake kuma bata wata daraja ta daban, amma duk ya watsar da shawarwarin Safwan ya cigaba da rayuwar sa yanda yaga dama.

Ganin bai tanka shi ba sai aikin hawaye da ke bin gefen idanun sa ya sanya Safwan furta" Haba Mu'een manta ko kai waye kayi ne, me yasa zaka dinga zubda hawayen ka har haka? Cuta ai ba mutuwa bace Insha Allahu ba abinda zai sami Jasmine...bu'de idanun ka inyi maka wani albishir.."
Ya 'karashe maganar yana murmushi.

A hankali Mu'een ya bu'de lumsassun idanun sa ya sau'ke su kan Safwan dake zaune gefen sa, yun'kurawa yayi da niyyan tashi Safwan sai yayi saurin taimaka masa ya zauna da 'kyar yana dafe 'kirjin sa da hannun daman sa.

Bai iya ya kalli Safwan cikin idanu ba, fuskar sa gefe cikin muryar da daka ji zaka fahimci cewa yana jin jiki yace
"...Safwan Allah yasa albishir 'din Nuree ta yafe min zaka yi min...kuma kace min Baby na tana lafiya".
Chapter 164 · 0% Book details