← Book details Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 211

Sashe 46

Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana 'daga wayar sai ta ci karo da sa'kon sa saurin bu'dewa tayi ta karanta " _Rahma kiyi ha'kuri ki gafarce ni dan Allah_ "
Haka kawai taga ya rubuta, sai ta saki murmushi a fili, wani sanyi taji ya ratsa mata zuciya da ganin sa'kon nasa.....fita tayi daga wurin sa'konnin ta fara gwada 'kiran layin sa amma baya tafiya, wasa-wasa har bayan maghrib bata same shi a wayar ba..... wannan dalilin ne ya sanya damuwar ta 'kara yawaita ta so taji ko muryar sa ne a yau 'din amma hakan bai faru ba.
(' *Kalubalen mu iyaye....kamata yayi mu kula da rayuwar yaran mu musamman 'ya'ya mata, bai kamata ace 'yar ki yarinya mace na rayuwa tsakanin gidaje biyu ko uku ba wasu ma zaka ga fiye da hakan....saboda* *gudun ta6ar6arewar tarbiyya dan Allah a kiyaye, ni bance dukka ba.....bhu majority akan samu matsala daga irin hakan idan ba Allah ya gyara ba, ta iya yiyuwa ke kinsa rai tana* *can gidan ne, yayin da suma can 'dayan gidan zasu yi zaton* *tana wurin ki ko kuma 'dayan gidan alhalin ita daga 6angaren ta ba haka abin yake ba... sai ta ringa wasa da hankalin ku cikin rashin sani.....sai* *fa an kula sosai 'ya'yan mu amana ne aka bamu dole ne kuma mu dage wurin kula da rayuwar su da tarbiyar su......kar* *ku manta cewar kulawa da rayuwar yarinya mace da bata ingantacciyar tarbiya zuwa aurar* *da ita ga mijin da ya dace na iya yi maka/ki sanadin* *Aljannah).....* 🤷‍♀ ~BA FA'DA TA BACE NIMA~ 🤷‍♀

Tana idar da sallar maghrib taji ana buga 'kofa da tsoro ta tashi taje jikin 'kofar ta tsaya batare da ta bu'de ba, daga wajen ta jiyo muryar Yayan ta Hayat na 'kiran sunan ta sai taji wani sabon firgici cuz bata san dame yazo yanzun ba.

Tsinkewa zuciyar ta tayi da 'karfi kana ta cigaba da bugawa akai-akai......yayin da Hayat ya cigaba da ambatan sunan ta at d same time yana buga 'kofar.

Dole badan taso ba ta barwa Allah komai ta tsaida zuciyar ta akan koma menene zai yi mata tana maraba da shi in dai akan Mu'een ne.

A hankali ta matsa jikin 'kofar ta sa hannu ta bu'de masa gami da matsawa baya ka'dan, Hayat tsaki ya saki ka'dan gami da fa'din " me kike yi tun dazu inata magana baki amsa ba?"

Da rawar murya ta bashi amsa da fa'din " sallah nakeyi".

Be 'kara furta komai ba kawai ya sako kai ya shigo sannan yace sai yace da ita " je 'dauko abinda zaki 'dauka da keys 'din gidan ki kulle mu tafi".

Da sanyin murya yayi maganar dan haka sai ta tafi 'dakin ta ta dauki kayanta kala biyu tasa cikin jaka sai wayar ta da hijab din da tayi sallar ta fito ta same shi hannun ta ri'ke da makulli.

Kar6an makullib yayi yasa ta agaba da kanshi ya kulle ko'ina sannan ya ri'ke makullin a wurin sa suka tafi inda ya wuce da ita gidan mahaifin su.

A parlour suka tarar da yaran gidan sama-sama ta gaisa dasu sannan ta wuce ciki....ko mahaifiyar su bata nema ba ta tafi 'dakin ta na gidan......wanka tayi da ruwa mai 'dan 'dumi saboda ciwon da jikin ta ke yi mata sannan ta gabatar da sallahr isha'i daga nan tayi shirin bacci ko abinci bata nema ba.

Da kwanciyar tan ma sai da ta sake gwada layin Mu'een amma switch off akace mata.

Da tunanin dalilin hakan tayi bacci, Allah ya taimake ta washegari da ta tashi garau taji ta illah kumburarren idanu wanda shima ta san hakan ne lokacin data je gaida matar Baban su ta tambayeta abinda ya sameta da idanun ta suka kumbura take sai tace mata da dare ne kanta yayi ta yi mata ciwo bata samu isasshen bacci ba shiyasa....." sorry" kawai tace da ita gami da ta6e baki sannan ta 'kara fa'din " Jiya ban ma san kinzo ba sai abakin yara naji...kuma yau da safe sai Hayatu yake cemin wai kin dawo kenan gaba 'daya meyasa ko de fa'da kukayi da yayar taki?.Ta 'karasa da tambaya gami da tsare ta da idanu....Rahma sai ta girgiza kai.
" to menene ko gajiya akayi da yawace yawacen?"

Shiru Rahma tayi mata bata bata amsa ba.
'Kasa-'kasa sai matar tace " ku de kuka sani munafukai kawai".

Rahma juyawa tayi ta fita abinta batare da ta amsa ta ba ita kanta matar sai da ta bita da kallon mamaki dan tasan Rahma ba haka take ba sam bata 'daukan 'kananun zagin nan shiyasa kullum basu fiye shiri da juna ba, da wuya tace mata munafuka tayi shiru sai tayi 'kun'kuni yau 'din ta tsammaci jin " mu de ba munafukai bane" daga bakin ta kamar yanda ta saba amma ga mamakin ta Rahma bata tanka ba.

Wannan dalilin ne ya sanya ta fahimtar lallai akwai abinda ke faruwa.

Rahma kam wurin mahaifin ta wuce, inda ta same shi akwance kamar kullum sai yanda akayi dashi, zuwa tayi ta zauna bakin gadon gami da kamo hannun sa d'aya " Daddy!
tace dashi a hankali sai ya tsur mata idanu " Ina kwana Daddy!"
Ta sake fadi da rawar murya take kuma sai kuka ya 'kwace mata.

Cikin kukan take fa'din " Daddy pls kacewa yaya kar ya rabani dashi, shi ka'dai nakeso Daddy...."

Maganar sa bata fita sosai dan bakin sa ya karkace amma ahaka yake 'ko'karin lallashin ta har tayi shiru.

Matar Daddy dake tsaye la6e daga bakin kofa ta6e baki tayi jin cewa damuwar Rahman kan soyayya ce.
" nasan ai dole akwai wani abu"
Tafa'da cikin ranta.

Wasa-wasa kusan satin Rahma guda agidan bata samu dama ko sau daya tayi waya da mu'een ba...duk ta fita hayyacin ta dan ba da'din zaman gidan take ji ba, babu wanda zata zauna da shi suyi hira illah mahaifin ta shi kuma a kullum ma ta ganshi ta tuno da lokacin da yake da lafiya sai tausayin sa ya karya mata zuciya, kullum da kuka take barin wurin sa.

Gashi yanzu bata da ranar barin gidan dan Hayatu da kansa yaje ya kwaso mata kayan ta gidan kaka Anty kuma yace mata ai Daddyn su ne yace ta zauna kusa dashi.

Sosai zaman ya gundureta 'dan hutun da suke yi ma jitayi yayi mata tsayi tsabar yanda ta damu sosai....kuma Hayat ya hanata fita ko'ina.

Akwai wani 'dan abokin Daddyn su da ya jima yake binta take wula'kanta shi dan bai mata ba...a 'yan kwanakin taga yana ta matsa mata da 'kira sam tarasa dalili.

Bata ma bashi fuska ko awayar ma amma kwatsam ranan wata talata sai gashi ya kirata wai tafito yana harabar gidan su.....

Share sa tayi ta'ki fita har kusan mintina talatin sannan taga ya sake k'iran ta 'kin 'dauka tayi sai da ya sake 'kira sannan ta 'daga " ina jiranki fa 'yan mata".
Yace da ita tsaki tayi gami da kashe 'kiran.

Basu fi mintina biyar bayan hakan ba sai ga kiran Hayatu ya shigo cikin wayar ta.
Tana 'dauka shima taji yana fa'din " Amin bai 'kiraki bane?"

" ya 'kirani"?
Ta bashi amsa da sanyin murya sai yace " to angaya miki bashi da aikin yi ne da ya zo 'din?"

" Yayah nifa bance masa yazo wurina ba"!

A harzu'ke ya ce da ita " zan sassa6a miki Rahma....baki da hankali ne?
Maza ki shirya ki fita yana jiranki saura kuma inji kinyi masa rashin kunya".

Da kuka ta fita wurin Al'amin 'din zuciyar ta tamkar zata faso 'kirjin ta.

Tana isa gaban sa ko gaishesa batayi ba kawai tace " shine ka 'kira Yayah kayi masa gulmata ko?"

Dariya ma ta bashi shikam sai da yayi dariyar kafin yace mata " shine kike kuka dan ance kizo wurina?"

" To ni nace ina son ganin ka ne? Kawai zaka sa yayi ta min masifa"

" sorry matas ba za'a sake ba na matsu in ganki ne shiyasa kuma nasan in ba hakan nayi ba bazaki fito ba....yanzu ba gashi na ga crying face din matata ba "

Baki ta tura gami da fa'din " ni ba matar ka ba ce...."

" hmm" kawai yace da ita sai ya tsaya kallon ta yana murmushi.

Haushi sosai ya kamata kawai ta juya ta koma gida.
Dai-dai tana shiga 'dakin ta sako ya shigo wayar ta _Sai nazo gobe ko matars_ .

" _sai kazo din ai mu gani_ " tace afili tare da yin jifa da mayafin ta.

A daren ranar Hayat ya sanar da ita abinda ke faruwa.....tayi kuka ranar kamar ranta zai fita ko bacci bata iya tayi ba.

Duk iya tsawon tunanin ta ta kasa fahimtar da yaushe akayi wannan kullin, duk abinda ke faruwa tsakanin da Amin abaya bata ta6a sanin cewa Hayat nada labarin ba.

Sai gashi kwatsam ya 'dauki ragamar ragomawar rayuwar ta yana shirin dam'kawa Amin nan da sati uku masu zuwa......bacin har ya ha'kura da ita tuntini ya daina damun rayuwar ta ta kasa fahimtar ta inda wannan alakar ta sake 'kulluwa.

....to ya zatayi da 'dimbin soyayyar da take yiwa Mu'een?"

Comment
Vote
Share

*Salmerh ce*😍
[1/6, 7:55 AM] 🌸Salmerh🌸: 💕 *NOORUL* 💕
(Haske nah)

By
*Salmerh MD*

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

🅿 *24*

........Ba 'karamin so take yi masa ba...gashi ba ta samun sa a waya ko ta nemeshi, a yanzu babu mai kwantar mata da hankali ko mutun 'daya, gara ma 6angaren Amin 'din ta kanji 'dan dama-dama domin shi ba laifi yana shiga rayuwar ta da nashi salon soyayyar bayaga shi kuwa kowa tsareta yake yi, mahaifin ta kuwa ba magana sosai yakeyi ba shi ko taje wurin sa ma ita ka'dai zata 'karaci kukan ta tafito shi kam sai dai yayi ta kallon ta.
Chapter 46 · 0% Book details