← Book details Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 186 OF 211

Sashe 186

Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hakan ya sa batarecda 6ata lokaci ba ta ajiye sim 'din ta sauya wani,
sai daga baya take yiwa Anty Zainab bayani da msmaki tace" To meyasa sai anyi hakan kuma..ko duk gujewa 'dan nawa haka Noor?"
Noor murmushi tayi tana sunkuyarcda kai tace" A a fa Anty...Ammi ce tacecin sauya ba wai dan shi bane.."
" Ita Ammin fa? Ai na lura itama yanzu duk a tsarge take...bansan meyasa hakan ba wallahi, ai abin zai masa yawa, ni nan gashi an hanani waya da shi 'karfi da yaji, Uncle Ja'afar har mamaki yake bani yanda ya hau dokin fushi da shi sai inga kamar ya manta waye Mu'een ne..kuskure kam ai kowa nayi haka ma laifi amma nashin sai aka tsaurara sosai wallahi bana jin da'di sam...sosai nake tausayin sa, yaro ba'a da'de ba ya rasa 'yar sa wacce kowa yasan irin 'kaunar da yake yi mata kuma sai a sake sashi agaba cewa ya rabu da matar sa ba ko tausayawa fisabilillahi akwai adalci anan kenan....fushin da suka 'dauka da shima ai wani tashin hankalin ne a gareshi...haba dan Allah, kema kuma sai kika biye musu ko?".
Shiru Hudah tayi ta sunkuyar da kanta.
Anty ne ta cigaba da fa'din" Harda canza layin ki bayan kinsan dole zai nemeki ko min da'dewa...".
" Ayyah Anty nifa haka kawai ne na canza ba dan wani abu ba..kawai na gaji da wancan 'din ne".
"..hmm ke de ki bi a hankali..kar ki biyewa zuciya Noor mijinki na 'kaunar ki ke kanki kinsani wallahi ko yanzun ma da aka jishi shirun nan nasan ba cikin natsuwa yake ba..Allah ne ka'dai yasan halin da yake ciki amma kowa ya kasa tausaya masa...kun ha'de mai baki kuna azabtar da shi abanza bacin duka abubuwan da aya aikata 'din ba akansa aka fara ba, kuma ma inada ya'kinin zai nutsu ko dan abinda ya faru ma...me yasa sai kun 'kara mai da wani...?."
Sosai zuciyar Noor ta karye sosai jikin yayi sanyi 'kalau.
Mi'kewa tayi ta koma 'dakin ta cuz tasan idan ta cigaba da zama anan kuka ne zai 'kwace mata.
Ko bayan fitan ta Anty kam surutu ta ringa yi dan harga Allah ita kam bata jin da'din wannan hukuncin.

Tayi 'ko'kari sosai wajen ganin ta manta da komai, ta manta rayuwar ta na baya, musamman dacyake Anty bata sake tada maganar atsakanin su ba, Addu'a kawai take yiwa Mahaifin ta su Nanne da kuma Jasmine fatan ta a kullum shine Allah Ubangiji ya ji'kan su da Rahma ya kyautata zuwan na baya.

Cikin lokaci 'kan'kani ta murje jikin ta ya dawo, tayi wani fresh da ita, yayin da Yah Deen ke can kwance rai a hannun Allah zuciyar sa tayi mummunan bugun da likitan sa ma sai da ya tsorata da shi.

Tun da ya gwada 'kiran ta yaji baya shiga sai hankalin sa ya tashi sosai.

Shi tsoron sa ma kar ace wani abin ne ya same ta batare da ya sani ba.
Cikin rashin sa'a kuma duk 'kiran da yake gwada yi mata sai yake zuwa da sa6ani da farko kafin ta canza layin baya 'kira sosai amma tunda ta canza a lokacin kuma sai yafi jin damuwa da ita a kullum sai ya gwada 'kiran layin nata fin sau biyar amma yaji baya samu.

Hankalin sa sosai yake tashi, ranar sai ya 'kira Ammi bai ma zaci zata 'dauka ba ga mamakin sa sai yaji ta 'daga..
Jikin sa har na rawa saboda jin da'di yace
"...Ina yini Ammi.."
Tace " Lafiya".
A takaice.
" Ya wajen su Alhaji..?"
shima 'din" Lafiya" ta sake fa'di.
ji yayi kamar ya rushe da kuka saboda takaici, wai yau shi Ammin sa ke yiwa irin wannan abin, me za'ayi da banzar rayuwa...kwantar da murya yayi tamkar gaban ta yake da kaji muryar zaka san cikin matsanancin halin da za'a tausaya masa yake ciki a hankali cikin raunin murya ya fara magana...
" ...Ammi kiyi ha'kuri badan hali na ba, Ammi ku yafe min, wallahi ji nake kamar zan mutu saboda rashin sukuni bansan inda zan saka rayuwa ta ba, abubuwa dayawa nayi nadamar su Ammi..ko ban fa'da ba da kanki ma nasan kin fahimce ni, ko kowa ya guje ni Ammi ke be kamata ace kin guje ni ba, ki tausaya min Ammi ba dan hali na ba, gashi inata 'kiran Noor kullum ba ya shiga please Ammi ke uwata ce wacce ta haife ni nasan baza'a rasa birbishin 'kaunata a zuciyar ki ba, Ammi ko dan saboda nawin ciki na da kika 'dauka na tsawon watanni..dan Allah ki yafe min Ammi...ki yafe min ko zan samu sassauci daga wani 6angaren cikin abubuwan da ke damu na, Ammi ki yafe min kuma ki tausaya min ki ceci zuciya ta ki gaya min inda Noor take Ammi hankali na ya kasa kwanciya...".
" Ta mutu".
Shine amsar da Ammi ta bashi ata'kaice,.amsar da ya doki zuciyar sa take ya haddasawa jikin sa karkkarwa.
Da rawan muray murya yace" Ammi Noor fa nake nufi Nuree...na...my wife..".
" I said ta mutu, kasa aranka bata raye kawai dan bazaka sake ganin ta ba..".
Tana kaiwa nan ta cire wayar a kunnan ta gami da hanging call in.

Ita kanta ba 'dadi take ji ba, sai take jin wani tashin hankali game da shi musamman da yake tasan ba lafiya cikakka gare sa ba, gashi a kwanakin takan yawaita mafarki da shi marasa kan gado duk tana ankare da hakan amma babu yanda zatayi..so take yasan muhimmancin Noor ya kuma san muhimmancin zama mutum nagari, so take da kansa ya fahimci illar rayuwar da ya za6a ma kansa...so take yayi tuba na gaskiya, can cikin zuciyar ta ba son rabuwar su take ba sam, domin tasan kafin ya sake samun madadain Noor zai matu'kar wahala sosai, ko kalan ha'kurin da tayi ma da wuya kasamu mai ma irin sa balle kuma hankali da natsuwar ta, amma aganin ta hakan ka'dai shine mafita tunda ma Noor da kanta ta nemi sakin, kuma tasan tayi ha'kuri da shi abaya baya ga haka da bazata ta6a saka baki 6angaren sakin ba sai dai kawai ta hora shi.
Shiru tayi tana tunani jikin ta sanyi 'kalau.

'Bangaren Yah Deen kuwa bai ma san lokacin da wayar ta bar hannun sa ta fa'di 'kasa ba, ji yayi ya kasa tantance tsakanin sama da 'kasa ina yake rayuwa, idanun duk sun cika da wasu kalan 'kwalla masu matu'kar numama zuciyaya, 'kirjin sa tafarfasa ya fara....danganta Noor da mutuwa daidai yake da fitan nashi numfashin ya haka yake ji kamar...da wanne zai ji? da alhinin rashin Jasmine zai ji ko da fushin da suke yi da shi ko kuwa da rashin Noor da ya dame shi.

Idan kana daga kusa da shi a fili zaka dinga ganin yanda 'kirjin sa ke hawa da sau'ka, wanda cike da matsanciyar azaba ya dafe saitin zuciyar sa, hawaten sa suka gangaro har tsawon wani lokaci zai 'dauka yana azabtuwa da rashin makusantan sa, masoyan sa masu matu'kar daraja agare shi? mai yasa bazasu fahimci halin da yake ciki ba?
Da 'kyar numfashin sa yake fita yana komawa.
'kiran Ushaq ne ya shigo masa a daidai lokacin..sai ya lumshe idanu kawai baya son.Isahqvya fahimci halin da yake ciki danbhaka bai 'daga wayar ba har ta tsinke wani 'kiran ya sake shigowa.

'Karfin.halin 'dagwacyayi bayan yayi 'ko'karin daidaita murya muryar sa.
Ishaq na ganin an 'daga sai yayi sallama amma ya kasa amsawa.
" Hello!
Ishaq ya sake fa'di
Mu'een sai ya 'kira sunan shi cike da 'karfin hali.
Duk 'ko'karin da yayin kuwa hakan bai hana Isahq fahimtar yanayin da yake ciki ba.
" Me ke faruwa ne?"
ya tambaye shi daga dayan 6angaren yana mai bada hankalin sa gare shi.
" Bakomai".
Yah Deen ya amsa a takaice yana mai juya kansa.
" Ja gaya min plz..I heard ur voice wani iri like akwai abinda ke damun ka...please tell me...dama na jika shiru 2days shiyasa na 'kira...hope ba wani abu bane?"
" Bakomai Ishaq kar ka damu...".
Saurin taran sa yayi da fa'din" Nasan akwai... please Mu'een tell me kar ka 6oye min hankali na ya tashi sosai".
" Ishaq...mutuwa zanyi ku yafe ni...dan Allah..".
Yayi maganar muryar sa na rawa.
" Subhanallah...me ke faruwa kuma..?"
Ishaq ya tambaya cike da kulawa yana jin tamkar ya gansa agaban sa a wannan lokacin.
" Ammi..!
Kasa karasawa yayi sakamakon ciwon da ya sake haura masa.
A hankali ya saki wayar ta sulale Isahq nata Hello! Hello!!
amma yaji shiru.
Ko da ya sake kira kuma ba'a amsa ba.
Sosai hankalin sa ya tashi...ya fara 'kiran Safwan shi kuma bai ma ji ba wayar tasa na silent so bai san ma da 'kiran ba.

Haka yayi ta gwadawa amma baya 'dagawa haka ma Mu'een.

Kansa ya dafe daga inda yake tsayen cuz tuni zama ya gagare shi.
Sai ma ya rasa wa ya kamata ya 'kira.
Addu'a ya ringa yi da fatan Allah ya ta'kaita masa.
Tuni ya yanke shawaran tafiya gobe-gobe idan ya tashi cikin masu rai dole sai ya je ya duba halin da abokin nasa ke ciki kafin zai samu natsuwa...sosai yake tausaya masa duk dama yasan wani abin har da laifin sa a ciki amma a yanzu abin tausayi yake matu'ka.

.....Deen ya 'dauki tsawon lokaci ahakan kafin Allah ya taimake shi ya kawo masa Safwan wanda tasowan sa kenan daga aiki ya nufo gidan cuz baya iya jimawa batare da yazo ya duba shi ba saboda yasan lafiya tayi masa 'karanci a yanzu, kusan ma za'a ce tare suke yini agidan dan akoda yaushe idan kaga anfita to Safwan ne, idan an shiga ma shi 'din zaka gani.

Da ganin halin da yake ciki arikice yayi kansa yana salati.

Yau ma Bala mai gadi ne ya taya shi suka kaishi mota, shikan sa Bala tausayin Ubangidan nasa yake yi sosai, yau lafiya gobe akasin haka...duk ya lalace ya zama kamar ba shi ba.
Chapter 186 · 0% Book details