Sashe 19
Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
_Godiya mara iyaka gareku 'yan uwa na, sosai naji da'din addu'o'in ku gare ni....Allahu ya saka muku da mafificin alkhairi, baiwa_ _da rahamar sa._ 😍
*_Fatan alkhairi masoyana Allahu ya bar 'kauna_ 🤝*
*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*
🅿 *10*
Iya k'ololuwar tashin hankali babu inda na Noorul bai kai ba a ranar, amma taurin kanta da kuma haushin abinda ta gani ya sanya ta ta tsani sake 'daga wayar ta ma balle har ta 'kira Deen kan batun Jasmine 'din.
Haka ta daure ta sake 'kara mintina kusan talatin akai batare da ta kira Deen 'din.
Ga mamakin ta kuwa har a lokacin shiru babu labarin su.
Wnda zuwa lokacin kuwa duk wani dauriyar ta 'karfin su ya tafi, wani sabon kuka take jin yake taso mata, ita kanta tausayin kanta ta keji, da wanne zataji?
Da damuwar miji ko kuwa damuwar Sani?.
'Dan guntun hawayen da ya zubo mata tasa hannu ta goge shi da bayan hannun ta sannan ta mi'ke cikin hanzari ta zari mayafin ta, cikin jakar ta laluba ta zaro 2k sannan ta fita bayan ta rufe jikin ta da mayafin.
Ko da ta isa parlourn ma ko kallon inda wayar tata take bata yi ba, kawar da kanta tayi gefe ta fice abinta cikin sauri.
Kafin ta fita sai da ta saka mai gadi ya sake 'kiran Sani, amma har yanzun dai wayar sa bata tafiya, sai tace ya 'kira mata Deen tana so tayi magana da shi.
Ko daya gwada layin Deen ma a lokacin bata shiga, dan already jirgin su ya lula sararin samaniya zuwa Bauchi.
Noor da bata san da batun zuwan nashi ba sai taji wani sabon takaici ya kama ta, idan zata biye abinda 'kirjin ta ke mata da ko tafiya taku biyar mai kyau bazata iya ba.
Amma rashin sanin halin da 'yar ta Jasmine take ciki a lokacin shi yafi komai 'daga mata hankali......fiye da komai.
Cikin 'karfin hali ta ringa karanto maso sauran layukan Deen 'din yana gwadawa amma ko 'daya babu wanda ya shiga.
Rintse idanu da karfi ji take kamar iska zai yi sama da ita tsaban yanda take jin kanta, bata bari mai gadi yaga hawayen daya sauko mata ba....sai da ta juya ta fuskanci gate kafin ta furta " nagode Bala".
Bai ma ji da kyua ba amma kuma kuma bata kuma maimaitawa ba ta cigaba da 'daga kafafun ta a hankali ta fara tafiya izuwa bakin gate 'din.
Tunanin 'kiran Saif take yi amma bata rike numbern ki ba kuma baya san komawa ciki a yanzun balle ta dubo cikin wayar ta.
Wani tunani ne ya sake zuwa ranta cak sai ta tsaya sai kuma ta juya ta kalli Bala tare da fa'din " Bala....dan Allah Sani bai ce.....da kai zai biya wani.... wuri ba kafin ya fita?"
Muryar ta na cracking tayi maganar kana ji ba sai an sanar da kai ba zaka fahimci cewa tana tare da matsanciyar damuwa.
Mai gadi jijjiga kansa yayi, shima 'din duk jikin sa yayi sanyi domin irin hakan bai ta6a faruwa ba iya zaman sa a gidan, ace har 'karfe biyu na shirin haurawa amma babu labarin mai tashi 'karfe sha biyu daga makaranta.....abin gaskiya bai yi ba kuma dole hankalin ta ya tashi matsayin ta na uwa.
Yana jijjiga kai 'din ya ke wannan tunanin.
Sai kuma ya 'kara da fadin ....." Babu inda yace min zashi Hajiya, ni Sani ma tunda nake da shi a gidan nan bai ta6a sanar dani inda zashi ba...."
Ya 'karashe maganar a hankali domin tuno wani abu da yayi cikin ransa
Sai yace "...sai dai kwanaki ya ta6a ce min daga nan in ya bar aiki Lagos zai wuce amma ban san yaushe yayi niyyan tafiyar ba gaskiya".
Take lumsassun idanun Noor suka bayyana 6aro- 6aro, bakin ta har na 6ari tace da Bala " Lagos dai?
Shine ya gaya ma hakan kuma?"
" Ehh 'kwarai kuwa Hajiya...shine da bakin sa ya sanar dani, sai dai bai har ga Allah bai gaya min ranar da zai yi tafiyar ba".
Ya bata amsa cikin tabbatar wa.
Noor ji tayi tamkar ta sa hannu aka tayi ihu...bata sake waiwayan Bala maigadi ba balle maganganun sa, tasa kai kawai tayi waje da sassarfa tana share hawaye.....a fili kamar zautacciya take fa'din " Allah ka sa hasashena ba gaskiya bane, Yah Allah ka dawo min da yarinya ta....ina son 'yata Yah ka taimake ni ka sada ni da ita".
Tafiya take tana zubda hawaye har ta 'karasa bakin titi ta tari 'dan adaidaita, shigewa kaia tayi bata ma ko tuna ta gaya masa inda zai kaita ba dan tsananin tashin hankalin da take ciki, sai da yayi tafiya mai 'dan tsayi kafin yace da ita " Hajiya ina muka dosa ne?".
Firgigi tayi cikin damuwa ta sanar da shi sunan makarantar.
Ciki-ciki yayi tsaki dan kuwa shi ba hanyar ya 'dauka ba sai da ya 'dan 'kara tafiya ka'dan kafin suka yi U- turn zuwa hanyan makarantar su Jasmine 'din.
Bata yi mamaki ba lokacin da ta isa bakin gate 'din makarantar ganin tamkar mutane basu ta6a rayuwa a wurin ba domin kuwa shiru arean gurin babu kowa, ita kanta tasan babu mamaki koda ta ga hakan, cuz almost 2hrs kenan da tashin 'daliban makarantar to kuwa wa zata samu?
Kafin ta shiga sai da ta juya ta kakkali gefe da gefen hanya wai ko zata hango motar dasu Sanin ke ciki amma ina, bata ga komai ba.
A hankali ta tura gate 'din ta shiga hango mai securites biyu da tayi zaune kan table ne ya sanya ta nufan inda suke, 'daya sai faman zuba surutu yake yayin da dayan kokuwa da da asuwaki cikin bakin sa.
Kafin ma ta 'karasa mai asuwakin ya taso ya iso gare ta yana fa'din barka da zuwa Hajiya....wani matsala ne?"
Yana gama fa'din hakan sai ya karkata kai gefe ya tufar da yawu.
Noor kai ta 'dage masa tare da fa'din " ehh Baba yarinya ta ce har yanzu bata koma gida ba....bansan meke faruwa ba wallahi kuma tunda 'karfe sha 'daya na turo driver 'daukan ta".
Batare da wani dogon tunani ba securityn yace " ya sunan ta?"
Noor da sauri ta bashi amsa da fa'din " Jasmine ake 'kiran ta amma sunan Aisha Muhammad Tahir, nursery 2 take Baba shekarun ta kuma biyar ne!"
Inda ta bashi amsar tambayar tasa hadda ma wanda bai tambaya ba.
Sai yanzun ne ya 'dan kai hannu bakin sa alamar nazari, sannan yace " ehh toh a gaskiya dai ban gane ta ba......amma kuma yara yau duk babu wanda ya zarce 'ka'ida anan....kusan kowa ya watse tun ma kafin mu shiga Sallah, dama manyan sun ne ma ke 'dan 6ata lokaci amma yaran kam gaskiya duk basu da'de anan ba, sai dai ko ki tuntu6i drivern 'kila wani uzuri ya ri'ke su....."
Tun ma kafin ya rufe bakin sa tace " Na shiga uku ni kam, Allah ka rufa min asiri?"
Tayi maganar ha'di da dafe 'kirji.
Kallon da security 'din yayi mata ne ya sanya ta sau'ke hannun data 'dora a kanta dama na 'kirjin gaba 'daya.
" Me ke faruwa ne wai?"
Ya sake tambayar ta da kulawa, sai tace " Numbern drivern baya tafiya tun 'dazu wallahi an ta gwadawa".
Da sauri ya furta " subhanallahi......ashsha, Allah dai yasa lafiya....."
Bata amsa ba sai kawai ta juya ta fita tana share hawaye yayin da Baba security ya cigaba da fa'din rayuwar yanzu sai a hankali komai ya lalace gaba 'daya, zu'katan mutane ya gur6ace da son abin duniya....Allah dai yasa ba salwantar musu da rayuwar yarinya wannan mutumin yayi ba".
Daga inda take cigaba da tafiya tana iya jiyo duk abinda security 'din ke fa'di, daf da zata bu'de gate 'din ta amsa da " Amin".
Sannan ta fice tana tunanin ashe ba ita ka'dai ke zargin hakan ba.....ita dai ro'kon ta Allah ya ku6utar mata da 'yar ta ya kuma bata kariya a duk inda take.
Maganar da Securityn yayi sai ya 'kara birkita mata lissafi.........what if sayar min da yarinya yayi!.
Da sauri ta jijjiga kanta ha'di da fa'din no no it can't be....Sani ba zai yi hakan ba.
Wani zuciyar yace da ita idan kuma Lagos 'din ya tafi da ita fa........innalillahi Allah ka rufa min asiri......Allah kar ka tabbatar min da duk wadan nan abubuwan, Allah ka dawo min da baby lafiya.
Ita ka'dai take tafiya tana sa'ka da warwar ta a zuci sam bata cikin natsuwar ta wani mota da ya auno ta da ka'dan yayi wulgi da ita sai yayi saurin jan birki, ita kam ma duk bata kulaba.
Masifa ya so balbale ta da shi amma ganin tana kuka ya sanya shi jan bakin sa yayi shiru....haka taui wucewar ta ta gaban motar batare da ta kula da yanayin kallon da yakeyi mata ba.
Mace har mace amma duk ta zama wata tamkar mahaukaciya.......jijjiga kansa yayi sannan yaja motar sa yayi gaba.
'Kin taran abin hawa tayi taci gaba da tafiya tana yi tana 'dan dube-dube wai ko zata hangi motar a wani wuri, lokaci-lokaci ta kan share hawayen dake gangaro mata, gaba 'daya ta fita hayyacin ta, wuni guda amma idan ka ganta sai kayi mamakin yanda duk ta birkice.
Bata ta6a tunanin akwai ranar da zata tsinci kanta cikin tagwayen damuwa irin wannan ba, bata ta6a tunanin haka ba, ashe farin cikin mu da ba'kin cikin mu duk suna faruwa ne daga yanayin rayuwar mu.
Yunwa take ji sosai domin tun safe bata saka komai cikin bakin ta ba, amma sam bama ta jin cin komai a wannan yanayin, damuwar ta Jasmine ne, burin ta ta ganta tasan halin da take ciki.
Har yanzun kuwa hawaye na cigaba da sa'k'ko mata wanda yake tilasta ta yawan goge shi, domin da saurin sa yake sau'kowa hakan yasa bata jinkirin 'daga hannun ta takai saman fuskar ta ha'di da ro'kon Allah ya ji'kan ta ya ta'kaita mata wannan abin, Allah ya bayyana mata 'yar ta gudan jinin ta.