Sashe 170
Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wani mahaukacin mari ta sau'ke masa ta sake 'karawa akaro na biyu har bakin sa na jini, kafin tayi na uku Noor bata san lokacin da ta taso da gudu ta shiga tsakanin su ba, duk yanda take jin tsanar sa cikin ranta amma bazata ta6a juran ganin irin hakan tsakanin sa da iyayen sa ba, sosai taji tausayin sa da Ammin ke dukan sa, kuka take tana ro'kon Ammi akan tayi ha'kuri ta bar shi, tavyafe masa, shi da kansa yayi mamakin ta sosai duk kuwa cikin matsanancin tashin hankali yake.
Jikin Ammin ta shige tana kuka tana bata ha'kuri, sosai jikin Ammi yayi sanyi, ta rasa wani irin.zuciya ce ke ga Hudah, duk wanda yaji wanna labarin yasan sosai aka shiga hakkin ta amma duk da hakan alamun tausayi take nuna agare shi.
Yarinyar nan dama na jima ina tunanin bata cikin walwala, tunda na bashi auren ta yarinyar nan bata canza ba, hakan nan take kullum kamar wacce bata cin abinci ashe ita ka'dai tasan me ta 6oye cikin ranta.."
Ammi ce ke wannan tunanin cike da matsancin tausayin ta.
Ita ka'dai ce agaban ta yanzu, Jasmine ai 'yar sa ce, sai yaje can yaji da da ita tunda shine ya lalata mata rayuwa, duk tausayin Baby da Ammi ke ji awanni biyu da suka gabata duk sun tashi sun dawo kan Noor, yayin da haushin Yah Deen ya mamaye mata zuciya.
Mummyn Safwan ha'kuri itama take bawa Ammi at same time kuma tana bata misalai da manyan-manyan 'kaddarorin dake faruwa a wannan duniyar, tace tunda har ya kasance halin sa ya zayyano da bakin sa bai kamata kuma tayi masa irin wannan hukuncin ba, ga dukkan alamu nadama ce mai girma ta shige shi dan haka.nasiha ya kamata tayi masa ba duka ba.
Huci ammi ta sau'ke dan sosai ranta ya 6aci da su, Allah wadai take yi cikin zuciyar ta da rayuwar Mu'een, sam bakin ta ya kasa furta komai, illah nuna shi da take yi da yatsa idanun ta jajazir...da 'kyar ta fizgi magana tace" Allah ya sauwa'ke in sake 6ata yawun baki na dan.kawai in yiwa wannan banzan nasiha, idan har wanda akayi masa abaya bai shiga kansa ba to banga alamar shiryuwa tattare da shi ba, yaje can shi yasa ni rayuwar sa ce ai...banza marar hankali wanda bai san ciwon kansa ba.."
Ta 'karasa fa'da da yaren su na Igbo.
Shi kam sai hawaye kawai yake yi hannun sa dafe da kuncin sa, yacriga ya shiryawa duk hukuncin da za'a yi masa a yau 'din, cuz aganin sa ya cancanci koma wani irin hukunci ne.
Safwan gefe yake da Alhaji Baba yana bashi ha'kuri da kwantar masa da hankali.
Abinda bakin Ammi ya iya sake fa'di kawai shine" Wallahi...ka yi asaran rayuwar ka Mu'een..."
Kafin ta sake yin wata magana Mummyn Safwan tayi saurin rufe mata baki..tana bata ha'kuri.
Gaban ta Yah Deen ya jawo gwiwan sa ya dawo gaban ta yana hawaye yake fa'din" Ammi dan Allah idan duka na zai sa zuciyar ki tayi sanyi ki min komai, ki dake ni ki min duk abinda zaki min indai ranki zai yi sanyi, ni da kaina ma na tsani kaina Ammi, wallahi bana so in sake rayuwa a duniya saboda ban iya faranta wa masoya na rai ba...Mummy ki bar min Ammi tayi ta bugu na son ranta koda kuwa zai yi sanadin rayuwa ta ne bazan ji ciwon sa ba, kaico na da na kasance mujiya cikin ahali na, kaico na da na za6i kazamar rayuwa na sa ta zamto wani 6angare cikin rayuwa ta ....."
Bai kai ga rufe bakin sa ba sai ya fara tari akai-akai yana dafe 'kirjin sa da duk hannuwan sa biyu...wani jini ne ya sake fitowa ta bakin sa take sai ya 'dur'kusar da kansa 'kasa cike da azaba ko hawayen ma tsayawa suka yi.
Da sauri Safwan ya bar Alhaji Baba yayo kansa ya ri'ke shi haka ma Mummy dake yi masa sannu a rikice take bawa Safwan umarnin yayi wani abu mana.
Shi kam da 'kyr yake fizgan kalmar" Ku...bar ni na mutu Safwan...bani da amfani yanzu.....".
Mummy cike da ausayawa take girgiza kanta gaba 'daya jikin ta yayi sanyi 'kalau.
...Safwan ne yayi 'kira wanda ba'a fi mintina biyar ba sai ga shi anzo da gadon tura marasa lafiya za'a tafi da shi inda ya kamata aduba shi.
Har a lokacin Alhaji Baba bai motsa daga inda yake ba, gaba 'daya jin halayen Mu'een daga bakin sa ya matu'kar sanyatar masa da jiki, ya tattabata ko 'karya babu a cikin zancen sa tunda yasan bazai yiwa kansa 'karya ba.
Ammi kuwa rungume take da Noor dukkan sau suna hawaye gwanin tausayi, da dubara ta kautar da fuskan Noor ta yanda bazata hango Yah Deen ba balle har taji tausayin sa.
'Bangaren Yah Deen kuwa fir ya'ki amincewa da a tafi da shi 'din da ka gansa kasan yana jin jiki amma ya'ki.bada daman da za'a taimaka masa wai shi sai yaga Jasmine tukunna, duk yanda suka zo su yi hanzarin tafiya aduba shi 'kin amincewa yayi, dole yasa Safwan fa'din abar shi ya ganta kawai 'din.
Da Safwan in suka shiga yana ri'ke da kafa'dar sa...bakin gadon da Jasmine ke kwance yaje ya tsaya sai yaga kuma an jona mata wani sabon drip a hannun ta bacin yasan tun jiya aka gama da wannan.
Haske sosai yaga ta 'kara yi masa a idanun sa.
Da mamaki natare da ya kalli inda Safwan yake ba da yana duban ta ya tambayi Safwan me kuma ya sake faruwa da Jasmine?"
Yayi maganar ne yana barin jikin Safwan daga ri'kon da yai masa a hankali ya isa gaban ta, hannun sa 'dayan ya 'daga ya ta6a jikin ta da shi sai yaji zafi rau a hankali ya shafa fuskar ta...yana jin tsananin tausayin ta na ratsa shi...ga wani masiffafen 'kaunar ta da yake ji kamar ya ha'diye abin sa ta huta da wannan wahalar.
Sai dai ya san koma me ze mata a yanzu ba zai saka ta farin ciki ba, musamman ranar da ta fahimci cewa shine ya ja mata wannan abin yasan duk daren da'dewa Baby tsanar sa zata yi kamar yadda mahaifiyar ta ta tsane shi yanzu.
Shafa fuskan ta da yayin ne ya sanya ta 'dan bu'de idanu, bata iya ta bu'de idanun duka ba saboda zazzafan zazza6in dake jikin ta a lokacin, banda cikin jikin ta dake gudu ko iya 'daga hannun ta bata yi.
Tana ha'da idanu da mahaifin ta sai ta saki murmushi irin na 'karfin hali da murnar ganin mahaifinta.
Bakin ta ka'dai ya iya motsawa tace" Daddy"..Wanda in ba idanu ka na kanta bane bazaka ta6a fahimtar tayi magana ba cuz bata yi shi da wani sauti ba amma a hakan Yah Deen ya fahimci abinda ta fa'di.
Shima murmushin yayi mata tare da 'dora hannun sa 'dayan saman goshin ta yana kallon cikin idanun ta, yayin da 'dayan hannun nasa ke dafe da 'kirjin sa har a lokacin.
Duk ya fita hayyacin sa kamar ba shi ba...amma zaman sa gaban Baby ya 'dan sanyatar masa da wani 6angare daga cikin halin da yake ciki.
Da 'kyar yake magana saboda numafshin sa dake fita akai-akai hannun san dafe da kanta yace"...Allah ya baki lafiya Maman Daddy...Allah tashi kafa'dun ki, Allah ya ta'kaita miki...ciwon nan ki warke cikin...'kan...'kanin lokaci, ko ba na raye Saif zai cika miki burin ki kinji Mama na, Uncles 'din ki da Mummyn ki zasu kaiki Makkah da Madinan ki ko?"
Jasmine bata yi magana ba illah idanu da ta zuba masa tana kallon fuksar sa.
Bai damu ba sai yayi murmushi bayan fahimtar abinda take kallo saman fuskar sa in.
Yasan yanda yarinyar shi take da tausayi, musamman kuma yasan.yanda take 'kaunar sa da rashin son.ganin damuwa tattare da shi, Jasmine yarinya ce 'karama amma sossai yake alfahari da ita wurin tausayi da 'kaunar mahaifanta, yasan badan itama fama take da kanta ba da babu abinda zai.hana ta tambayar abinda yake yiwa hawaye.
Hannu yakai ya share hawayen dake kan fuskar sa sannan ya sake maida hannun sa da hankalin sa gareta.
Safwan.kam tsaye yayi a gefe yana ganin ikon Allah..gaba 'daya gani yake Mu'een ya canza ya zama kamar ba shi ba, bai sanshi da yawan surutu sai gashi yau in surutun sa har na neman zarta iyaka a gaban yarinya 'karama.
A hankali ya cigaba da fa'din" Inajin kamar rayuwa ta ta 'kare ne Baby, ina ina ganin tankar bazan sake ganin ki ba, na so in canza muku.rayuwa ke da Mummyn ki amma bani da damar hakan yanzu , dan Allah Baby..ki yafe min kinji? Ki yafe wa Daddyn ki da yayi sanadin da aka cutar da rayuwar ki Baby, wallahi ji nake kamar in raba kaina da rayuwa saboda yanda nake tsananin jin tsanar kaina, da kaina na cutar da ke na cutar da mahaifiyar ki...
Idanun sa ya lumshe sannan ya cigaba da fa'din" Ki gafar ce ni Maman Daddy..ki yafe min, Insha Allahu daga yau bazaku 'kara yin ba'kin ciki saboda ni ba....".
Kallon sa kawai Jasmine take yi tana kallon bakin sa inda taga jini ba ma ta fahimtar abubuwan da yake fa'di dan maganganun nasa sun girmi shekarun ta sosai, hakan yasa tayi shiru kawai tana duban sa batare da ta fahimci ko.kalma 'daya daga cikin zantukan nasa ba.
"...ki yafe min duk abubuwan da suka faru badan hali na ba, nasan nine na ja miki gashi ya faru a lokacin da bani da ikon hana faruwar sa wallahi kunyar in 'kira kaina matsayin mahaifi agare ki nake yi a yanzu Baby dan Allah ki yafe min kinji, ke da Mummyn ki ku yafe min, idan Allah ya kar6i raina kiyi min addu'ah, idan kin girma ki tuna cewa mahaifin ki mai 'kaunar ki ne dan Allah kar ki tuna munanan laifuka na, ban ta6a yin wani abu dan na 'kuntatawa rayuwar ki ba sai dan farin cikin ki, ko wannan ma da ace nasan da faruwar hakan da wallahi har abada bazan ta6a ko fara kwatanta aikata alfasha ba, Baby...".