← Book details Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 97 OF 211

Sashe 97

Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ganin sun kusan ha'duwa ne ya sanya shi jan hankalin Uncle J da labarin makaranta, yana fa'da masa ire-iren wahalar da yake sha, shi kuwa Uncle Ja'afar na bashi 'kwarin gwiwa da fa'din me ma ya rage kuma ai saura ka'dan, yace ha'kuri kawai zasu yi sun ma yi mai wuyar ai saura ka'dan ne cuz dudu semester biyu kacal ne ya rage masa....tun kan Husnah ta iso daf yake yi mata wani irin kallo, da ido yake nuna mata alamun kar ta kuskura ta kula shi, da suka kusan ha'duwa kuwa sai ya kauda kansa gefe tamkar bai ganta ba wanda hakan ya bayyanawa Husnah cewa shima 'din baya so tayi masa magana ne, hakan yasa itama ta 'dauke kai tayi wucewar ta kamar yadda ta yi niyyar yi da tunanin waye wannan mutumin to...sai dai ta fahimci koma wanene mutumin to mai matu'kar daraja ne a wurin Mu'een...kuma yana mutunta shi gami da girmama shi irin na musamman 'din nan.

Sam Uncle J bai fahimci komai tsakanin su ba, da yake sam baya kawo ko zargin Yah Deen akan irin wannan abin ko cikin ransa...ko abinda ya gaya masa 'dazun ma ba wai ya zarge shi haka kawai bane, illah tunanin da yayi kan cewa haka a banza Alhaji Baba bazai takura shi akan maganar aure ba dole ne akwai wani abin wanda baya fatan yaji abinda zai ta6a masa zuciya akan mafi soyuwa cikin zuciyar sa wato Mu'een.

Har ajiyan zuciya ya saki lokacin da yaga ta shin motar su Uncle J, cuz har cikin tasha ya raka shi.

Hamdala ya ringa saki ganin bayan motar tasu, musamman da Allah ya rufa mai asiri ba suje ga abokin Uncle da yace zasu je ba.. Lokacin suna wani eatry ne sunje cin abinci bayan barin gidan Yah Deen da suka yi, har sun gama cin abincin suna niyyar tafiya sai yace dashi wai zai raka shi wurin wani abokin sa har da yi masa kwatancen wurin.

Nan take hankalin sa ya tashi da jin sunan wanda Uncle J 'din ya ambata da kuma sana'ar sa...kuma already tun daga kwatancen da yake yi ya fahimci wurin.

Mamallakin babban medical center da ya ta6a zuwa sayo magani wa Husnah ne da yake tunanin yaje da nisa inda babu wanda ya sanshi ya sayo drugs 'din, sai gashi Uncle J na shirin banka'da asirin sa da fa'din wai zasu je ya gaisa da shi wai abokin sa ne..." to idan ya gane ni kuma fa?"
Ya tambayi kansa...Innalillahi wa inna ilaihi raji'un..ya nanata cikin zuciyar sa kusan sau uku.." wai yau 'din nan me ke shirin faruwa da ni ne?"
Ya tambayi kansa, sannan ya sake fa'din" Idan kuma ya gayawa Uncle na ta6a zuwa wurin sa sayan magani kaza kuma fa... ya zanyi in 'karya ta shi ni Muhammad".
Fargabar sa 'karuwa tayi sosai akan nada duk kuwa da yasan cewa ba lallai ne mutumin ya gane shi ko tuno abinda ya kaishi wurin sa ba, amma kunsan abin ku da marar gaskiya..zuciyar su rangaji take bata tsayuwa wuri guda.

Kamar Uncle J ma yasan tunanin da yake yi sai yace" Bari dai in 'kirashi inji ko yana nan".

Sai yanzu ya iya samun damar fa'din" Gaskiya is better ka 'kira shi kam dan wurin akwai nisa ga kuma tafiya a gaban ka..."

Yana 'kira kuwa bayan sun gaisa sai yace da shi ai yana Dutse, mutumin sai yace shikuwa wallahi yana Kano amma wai gobe zai dawo why not ya jira shi...Uncle sai yace masa a a yana kan hanya ne dama sai dai wani lokacin kuma idan Allah yayi".

Da haka suka yi sallama yake yiwa Mu'een bayani...tsabar murna ma bai san lokacin da ya saki ajiyan numfashi ba har har da fa'din _Alhamdulillah_
Uncle J sai da ya dube shi yace" Ya dai".

" Bakomai Uncle banson kayi dare ne kasan kasar tamu sai a hankali".
Ya bashi amsa yana 'yar dariya...sai yace" Hakane".

Daga nan suka nufi tashar mota...ya tafi abinsa.

Ko yanzun ma ganin har Uncle J ya tafi bai fahimci komai game da rayuwar sa ya sanya shi a fili ya furta" Alhamdulillah".
Sai dai har cikin zuciyar sa ba zai iya bayyana a wani matsayi ya ajiye wannan ziyara ta Uncle Ja'afar ba, shin farin ciki zaiyi da shi ko akasin haka?"

Shi da kansa ya san ba dai-dai yake aikatawa ba amma yayi watsi da sanin sa, banda nasihar Ammi gare shi...sannan ga fushin mahaifin sa, duk hakan bai sa ya bar abinda yake yi ba.

Allah ma sai ya sake rufa masa asiri ya tsallake dukkan stage 'din da ya kamata Uncle J ya gano sirrin rayuwar sa...'dan baya gane cewa idan duk ka tsallake irin wannan kalubalen bayan kayi watsi da sanin ka, ka yi watsi da fushin manyan ka ka cigaba da aikata abinda ranka ke so to Allah yana so ya maka talala ne, ranar tonuwan asirin ka na nan yana jiran ka duk da'dewan shekaru kuwa dole ranar sai tazo, ranar da baka isa ka 6oye laifukan ka ga kowa ba...(ALLAH UBANGIJI KA SADA MU DA HASKEN KA, KA KUMA GYARA MANA ZUCIYOYIN MU KA SANYA MU CIKIN BAYIN KA SALIHAI AH'LUL JANNAH...(AMEEN YA RABBAL ALAMEEN).

Mashin ya hau ya koma gida, bai bi ko ta kan Husnah ba kawai yayi alwala ya wuce masallaci abinsa cuz la'asar ake 'kira a lokacin.

Ko da ya dawo daga masjid 'din ma direct 'dakin sa ya wuce, zuwa yanzun rayuwar da yake yi 'din tafara isan sa, shi kansa ya san cewa ba abin kirki yake aikatawa ba...sannan ba ya kyautawa iyayen sa musamman ma da ya tuno nasihar Ammin sa agare shi lokacin da zai taho, sai gashi cikin lokaci 'kan'kani yayi watsi da komai yana aikata abinda yasan Allah da kansa baya so...sosai yake so ya zama mutun nagartacce kamar kowa, so yake ya zama yaron da iyayen sa zasu yi alfahari da kasancewar sa da agare su, ba irin wanda ake Allah wadai da shi ba a duk lokacin da 6oyayyen halayyar su ta bayyana....sai dai tayaya zai iya hakan?"
Ya tambayi kansa..da farko dole ya san sai ya sallami Husnah ta bar gidan shi..in hakan ya faru to ina zan je da bu'katu na?"
Ya sake tambayar kansa..goshi ya dafe sannan ya furta" Iyaye na fa?..ya zanyi da su duk ranar da suka gano abinda nake aikatawa.." Ya Rabb please help me".

Yanzu da ace Uncle Ja'afar ya kama shi kan hakan fa.. da ya zaiyi?"

Juyi yayi kan gadon sa yana sake tunanin abin sosai ya dame shi, yana so ya zama nagari amma kuma yana gudun irin halin da zai shiga...not knowing that komai sawa arai ne musamman abu dangin zunubi.

Idan kasa aranka shai'dan sai ya 'kara ingizaka ya rura maka wutar 'kaunar abin cikin ranka...juyi ya ringayi yana tunanin mafita da ya gaji sai ya tashi ya fa'da bayi.

*****
     'Bangaren Uncle Ja'afar kuwa ranar da ya isa Shuwarin basu samu daman ganawa da Alhaji ba sai washegari...sai dai ko a lokacin da suka zauna kan zancen ma.. Alhaji bai fito fili ya bayyana masa asalin dalilin da yasa yake so ayiwa Yah Deen auren ba...kawai ce masa yayi ya fahimci yana da bu'katar auren ne dan haka ba za'a 'dauki dogon lokaci ba yace already ma ya gama binciken da ya dace ayi.

Da Uncle Ja'afar yaji Alhaji Baba ya ambaci Azare ne yasa ya tuno da maganar Mu'een da ya fa'da masa kan yarinyar da yace tazo wurin sa daga Azare.

Nan ya bu'di baki dan yiwa Alhaji bayani amma ya dakatar da shi yace baya son jin komai shi dai kawai burin sa ya fahimci inda ya dosa.

Uncle Ja'afar sai yace" Amma ai Alhaji kamata yayi a tuntu6e shi aji nasa ra'ayin tukun..."
" No need..ai mun gama magana da shi tuntuni sai dai kuma in zaku ha'de min baki ne ku juya min baya kai da shi".
Alhaji Baba ya tare shi da fa'din hakan.

Jin haka yasa Uncle J jan bakin sa yayi shiru...yana tunanin abinda Mu'een ya gaya masa.

Ko iya sanar da Yah Deen ma bai yi ba kawai ya dinga juya batun cikin ransa tare da jinjinawa irin zafin da ya fahimci Alhaji ya 'dauka kan lamarin.

Babu wani 6ata lokaci washegari suka wuce Azare gidan Alhaji Hamza da sunan nemawa Mu'een auren Husnah.

Sun yi sa'a kuwa basu yi tafiyar banza ba dan Alhaji Mamman na gari a lokacin, take yasa akayi musu jagora zuwa asalin gidan da sauran matan sa suke...kafin isowar su ne ya gayyato wani ma'kwabcin sa Alhaji Halliru suka yi jiran isowar su.

Tarba ta musamman akayi musu cikin girmamawa da karamci tamkar dama ansan da zuwan su...bai nuna musu alamun komai ba har suka bayyana masa kansu da kuma abinda ya kawo su...su kam ma tafe suke harda sadakin su a hannu...ga dukkan alamu Alhaji Baba dagaske yake yi bada wasa ba.

Ba'a 'ki kar6an batun su ba take Alhaji Mamman ya amince musamman da yaga yanayin shigar su da kuma motar da suka zo da shi yasan cewa ba 'kananun mutane bane, dan haka take yayi musu albishir 'din ya basu auren Husnah batare da yayi tunanin komai ba...har ma ya basu sati guda kacal da zasu dawo a tsaida ranar 'daurin aure.

Cikin farin ciki suka rabu, su Alhaji Baba nayi musu godiya sosai da yake tare yake da makwabcin sa.

Sai daga baya ne ma ya 'dan yi tunanin abin kamar bai yi dai-dai ba, amma bai tsawaita tunanin ba yaci gaba da harkokin gaban sa.

Washegari da girki ya dawo hannun Mummyn Husnah anan yake yi mata bayanin abinda ya faru da bada auren 'yar ta da yayi batare da yayi shawara da ita ba...  inda Mummyn Husnah ta matu'kar nuna ba'kin cikin ta da 'kin amincewar ta kan batun..hankalin ta ya tashi sosai..tace da shi" Alhaji a gaskiya bai kamata kayi hakan batare da kaji ra'ayin Husnah ba, ko da ni ban kai ayi shawara da ni kan lamarin ba amma ai ita da babu mai tayata zaman auren ya kamata a tuntu6e ta..."
Tayi maganar cikin nuna 6acin ranta.
Chapter 97 · 0% Book details