Sashe 128
Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ammi kam sam tace bata yaddada abinda na fa'di ba, yayin da na cigaba da kuka na ahankali ina sake fa'din ni gida nake so Ammi dan Allah kice kar na koma can..idan na koma mutuwa zanyi".
" Kiyi min shiru ni "Ammi ta daka min tsawa jin ina ambatar mutuwa.
Ga Yah deen ta dawo da kallon ta tace" Ka gaya min gaskiya Mu'een...wallahi idan na bincika na tarar da laifin ka wannan lamarin ka tabbatar ba zakaji da'di ba ko?"
Da seriousness yace
" Haba Ammi ni kenan bazaki ta6a yadda da ni ba, gata fa agaban ki da bakin ta kuma ta gaya miki ba komai...fisabilillahi ni me zan mata da har zan 6oye miki?...in dai zaman gidan take so a barta mana ta yi zaman ta tunda har yanzu takasa sabawa da can in, ni 'din ma ai next week zan koma school insha Allahu kinga ba wata matsala ai".
Tun zuwan sa sai yanzu ya iya yin dogon bayani wa Ammi saboda ya samu 'kwarin gwiwa.
Ammi hararar sa tayi kana tace" Dama ai ba son zaman nata kake ba shiyasa kayi saurin yanke wannan hukuncin".
Yace" Ammi za6in ranta ne fa..yanzu idan nace a a bazata zauna anan 'din bama laifi na zaki gani".
Tace" Ko.ma miye ne ai da laifin ka, am sure that da kana mata adalci agidan bazata ce nan take so ba...amma kai babu abinda ka sani sai mugun hali da ba'kar zuciya".
'Kasa yayi da kansa yana fa'din" Sorry Ammi..insha Allahu zan gyara".
" Ya rage maka ai..yanzu kam sai ka kawo mata kayan ta dan bazata sake komawan bama balle ka 6ata ranta...gashivsai wani.kakkauda kai kake yi na munafurci..ai.nasan dole baka da gaskiya Mu'een kawai kun 6oye min ne".
Sai da ya sosa kansa da hannun sa 'daya yana 'dan murmushi kafin yace" Zan kawo mata kayan Ammi...amma please idan Alhaji yayi magana kice da shi itace kanta tace gida zata dawo kar yaga kaifi na".
A takaice Ammi tace
" Naji".
Murmushi ya sake yi yana jin da'di har cikin zuciyar sa, fatan sa Allah ubangiji ya sa kamar yadda na 6oye yanzun ya cigaba da 6oyuwa cikin zuciya ta kar na bayyana lamarin ga kowa...
Tashi yayi yana fa'din barin je inyi sallah zanzo inci abinci idan nayi sallahr.
Ko 'kala Ammi ba tace da shi ba har ya fita daga 'dakin.
Daga haka ya Ammi tace da ni" Tashi to ki ha'da muku abinci a dinning kafin ya dawo ko dan kema banga alamun kinci abinci ba.."
Kafa'da na no'ke tare da fa'din" Ni na 'koshi".
Ammi saurin cire ni tayi daga jikin ta da mamaki tace" Hudah ban san rashin ji fa, dama ko agidan naki haka kuke zama da yunwa ko?"
Girgiza kai nayi alamar a a.
" To yanzun fa? ko so kike ince ki koma can 'din".
Sake girgiza kaina nayi harda fa'din " a a"
" Oya to go and serve ur lunch now".
Da hanzari na 'daga kai sannan na mi'ke tsaye.
Har na fara tafiya sai Ammi ta 'kira ni da sanyin murya tace min zo nan Hudah.." gefen ta na dawo na zauna..nifa hatta Ammin kunyar ta nake ji yanzu har zuciya ta...amma ita bata san hakan ba.
Cikin kwantar da murya tace dani
" Wani abin ya miki kuke 6oye min ke da shi ko?"
Kaina 'kasa nace" Bakomai Ammi kawai fa nayi kewar ku ne".
A 'dan fusace tace
" Akan kawai kinyi kewar mu shine kike irin wannan kukan Hudah? Meyasa bazaki ce ya kawo ki ki gan mu ba?..kinsan yanda kukan kinnan ya 'daga hankali na kuwa?".
Da sanyin murya nace da ita" Kiyi ha'kuri Ammi bazan sake ba".
Hmm kawai tace daga haka tayi shiru...yayin da ni kam na wuce dinning na ha'da masa abincin iya bakin sa na sake komawa 'dakin Ammi na yi kwanciya ta.
Koda ya dawo Ammi tayi 'kirana kan batun abincin, sai cewa da ita nayi ni kam na 'koshi.
Ammi bata matsamin ba ta bar ni har ya kammala cin abincin sa ya tafi kuwa ban kuma ganin sa ba...dama ni yanzu ba 'kaunar ganin sa nake sake yi ba balle yasa ni yawan tuna abinda naga yana aikatawa...wanda ko giyar wake nasha bazan ta6a iya furta shi ga wani daban ba...
Sam ban yi mamakin ganin san da macen da na jima ina ganin su tare ba wato Husnah, nasan kuma ba yau suka fara aikata irin hakan ba, bambamcin kawai shine na yau 'din yafi 'kona min zuciya ban kuma san dalili ba...sai dai nasan babu mamaki dalilin bazai wuce igiyar aure dake tsakanin ni da shi ba.
Dan sam bansan miye kishi ba balle nasan dililin da yasa ake yinsa...wannan abinda na ganin nan kuwa cikin sallah ta ne ka'dai bana tunawa da shi, sosai abin ya tsaye min a raina, shi yasa a kullum yake 'karamin tsoro da tsanar sa a zuciya ta...a yanzu ko 'kaunar ganin fuskar sa banyi...ko sunan sa banso inji an 'kira.
Sai dare ya kawo min kayana akwati 'daya kawai ya kawo min da sauran abubuwan da yasan zan bu'kata.
Ammi ce me ce da shi tunda basake komawa gidan zanyi kwana kusa ba ai da ya kawo min kayan nawa gaba 'daya.
Sai yace" Ammi tace ta kwaso da kanta idan ta bu'kace su".
Ko da Alhaji Baba ma ya dawo abinda Ammi ta sani shi ta fa'da masa...bai damu ba shima illah cewa da yayi dama ina zata iya zama da wannan mai ba'kin halin".
Bai ce in koma ba haka kuma bai damu da ya 'kira Yah Deen kan maganar ba...daya ke wannan karan labarin zuwan Husnah bai isa gare shi ba shiyasa tunanin sa ma bai yi zurfi ta can 'din ba..balle da yasan cewa Yah Deen 'din ya kusa komawa shikenan shima ya barni a gidan kawai na cigaba da zuwa makaranta ta.
Haka na cigaba da rayuwa gidan Ammi hankali na ya 'dan fi kwanciya acan sai dai a duk lokacin da naji muryar sa ya zo na kan ji tsananin fargaba na shiga ta da bugun zuciya.
Gaisuwa wannan badan gudun fa'dan Ammi ba da bazan 'kara gaida shi ba, balle yaga ko fuskata, amma Ammi a kullum tana 'ko'kari sosai wajen nuna darajar da miji ke da shi a wurin iyalin sa.
Hakan yasa nake daure zuciya ta ina zuwa inda yake, daga gaisuwar kuwa babu abinda ke sake ha'da ni da shi zan dawo 'daki...hakan da me faruwa tsakani na dashi sai yake 'kara 'daure kan Ammi ranar har ta tambaye ni dama ko can gidan ma irin zaman da muke yi kenan?"
Shiru nayi ban bata amsa ba cuz a yanayin da tayi tambayar nasan duk amsar da na bata wata tambayar ce zata sake biyo baya dangin son jin dalili...cuz idan nace nasan zata ce to me yasa yanzu kuma nake yi masa haka?"
Ni kuwa sam bani da amsar bata kan irin wa'dannan tambayoyin.
Ana gobe zai koma ne Ammi tace in tambaye shi zuwa gidan Ummah ta, raina baya so ma amma daya ke tace dole mace ta tambayi iznin mijin ta kafin ta fita ya sanya ni tilastawa kaina dauriyar tambayar sa..musamnan da yake naji gidan mu zani..dama da wani wurin daban ne da wallahi sai dai in yafe fitar amma bazan ta6a tambayar sa ba.
Sai da ya shiga ya gaida Alhaji Baba kafin ya fito wurin Ammi itama ya gaida ta..da yake bayan maghrib ne so shima Alhajin dawowar kenan gidan bai da'de ba, suna gaisawa da ita daga nan kuwa Ammi sai ta wuce side 'din Alhaji Baba bayan ta sanar dani cewa in tambaye shi kar na manta.
Ina son zuwa in tambaye shin amma sai nake jin nauyin ta shi in fita, gani nake kamar bazan iya harha'do dogon kalaman da zan iya furtawa ga Yah Deen ba..hakan yasa na cigaba da zama na kan dadduma ina lazimi na da tunanin ta ina zan fara, ban tashi ba tunda na idar da sallar maghrib ina zaune a wuri guda...duk da ina jin haushin sa yanzu amma tun faruwar lamarin nake addu'ar Allah ubangiji ya shiryar da shi ban ta6a tsallake ko rana guda ba.
Ina zaune a wurin na ji motsin mutun ya shigo..zato na Ammi ce dan nasan ita ka'dai ke shigowa a duk lokacin da ra ga dama, hakan yasa na fara harha'da 'karyar da zan gaya mata idan ta tambaye ni batun zuwa gun nasa...ban gama tunanin da nake yi ba naji 'kamshin turaren da na tabbatar ba na Ammi bane ta baya.
Da sauri na waiga da yake nasan ba 'kamshin da na saba ji ba ne wurin Ammi, sai naji ya zame min ba'ko.
Bazata kawai naga Yah Deen na shirin zama kan side drawern gefen gadon Ammi.
Komawa nayi na gyara zama na ina ta6e baki tare da cigaba da abinda nakeyi duk dama dai na daina fahimtar komai amma still ban daina yi ba...ban ma san me dame kuma nake anbata ba a lokacin.
" Noorul Hudah"!
Ya 'kira sunana yana wani jan sunan kamar dole aka sanya shi 'kira, ban amsa ba haka kuma ban motsa daga yanda nake bai.
Bayan wasu sakannivya sake fa'din" Noor".
Instead na amsa shi a a sai nace" Ina yini"?
Murmushi yayi mai sauti kafin ya amsa da" Lafiya lau".
Shiru ya 'dan biyo baya sai can yace da ni" Gobe zan koma".
Tun kan ya rufe baki nace
" Allah ya bada sa'a".
" Ameen".
Yace yana shafa kansa.
Tare da kallon 6angaren da nake.