← Book details Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 172 OF 211

Sashe 172

Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Videon sa da Jiddah ka'dai ma ya ishe ta gane hakan, shiyasa itama ta yanke shawaran da ta ga yafi kwanciya mata a zuci.

Addu'ar ta kawai shine Allah ya bawa Baby lafiya su yi tafiyar su su bar shi yaje can da 'yam matan sa sa da ya fi son yin rayuwa da su.

Cikin gidan ta shiga tana jin sa wani iri duk babu da'di...fili sosai taga yayi mata, da idanu ta kalli inda suka rabu da Baby jiya lokacin da Sani zai tafi da ita makaranta.. _Allah Sarki_ ta furta cikin ranta sannan ta 'dauke idanun ta.

Sai da ta tsaya suka gaisa da Bala maigadi kafin ta shige ciki, shima bayan ta yabi da kallon tausayi yana girgiza kansa dan duba na farko idan kayi mata zaka fahimci hankalin ta ba a jikin ta yake ba, duk ta fige ta rame cikin yini guda da kwana 'daya kacal...A fili ya furta Allah ya rufa asiri.

Da fitar su Noor daga asbitin sai Hafsat ta 'kira ta sanar da shi cewa yanzu zata taho ta gama abincin rana.

Nan ya sanar da ita cewa ai Noor in ma yanzu ta wuce da Mummy, amma tabiya ta can dan ta ringa 'dan 'debe mata kewa kar ta rin'ka yawan tunanin in yaso in ta gama shiryawa sai su taho tare da ita.

Hakan kuwa akayi domin Hafsat can ta wuce aka sau'ke ta ta biya 'dan sahu ku'din sa yayi gaba ita kuma ta shiga ciki.

Kayan abincin dake hannun ta ajiye a bakin parlour ta ciki tare da sau'ke Afrah suka 'karasa ciki..dan duk salkamar da take ko 'daya bataji an amsa ta ba.

Noor mamaki sosai ne ya kamata lokacin da ta shiga ciki ta tarar da kayan ta da ta shirya babu su duk an sake jere su, tayi mamakin lokacin da hakan ya faru, kuma tasan ba kowa ne zai yi hakan ba sai Yah Deen, baki ta ta6e kawai bata wani sa aka ba dan damuwar kanta ma ta ishe ta a yanzun.

Wanka ta shiga yi wanda a lokacin ne Hafsat ta iso shiyasa bata samu an amsa sallamar ta da tata yi ba.

Noor kam wankan ta tayi ha'di da wankan tsarki dan yanzu kam tasan kwanakin hailar ta ya cika jiya ma mantawa tayi har tayi gaggawan yin wanka tayi sallah batare da ta tuna ba.

Sallahr azahar ta gabatar bayan ta saka dogon riga a jikinta.
Sai da ta idar sannan ta fito nan ta tarar da Hafsat zaune, sabon  gaisuwa suka sake Hafsat ta tambayi jikin su Baby Noor ta amsa ta fa'din" Alhamdulillah.. da sau'ki.

Hafsat sai tace" Ashe shima Mu'een 'din jikin ya 'kara motsawa, 'dazun Safwan ke sanar dani".
Da" Umm" kawai Noor ta masa ta tana yin 'kasa da idanun ta.

" Ga abinci ki ci to dan nasan idan muka je can ba iya ci zakiyi ba.."
Cewar Hafsat dake 'ko'karin mi'kewa dan 'dauko mata abincin.
Saurin dakatar da ita tayi da fa'din" A a kam ki bari mu isa can 'din..Ammi na fa ta zo tana can da Alhaji Baba..".

Washe baki Hafsat tayi cike da farin cikin zuwan su Ammin tasan dama abin zai yiwa Noor yawa ita ka'dai.
Fuskar ta cike da murmushi tace" Duk da hakan dai kamata yayi kici agida nake ganin zai fi can in ko?".
Kawar da kai tayi gefe tace
" a a ki barshi Hafsat ban jin ci ma yanzun wallahi".
Komawa tayi ta zauna tana duban ta tace
" Ke dai bakya ji Noor, Baby ba lafiya, ga Dr. Ma can rai a hannun Ubangiji, kema kuma so kike Ulcer ta kwantar da ke ko...?"
Murmushi tayi mata tana kamo hannun Afrah tace" Bani da Ulcer ai ni.…bana so ne inyi nisa da Baby shiyasa nafi so mu koma can in da sauri.... ."

Kafin Hafsat tayi wata magana sai wayar ta ta 'dauki ringing ko da ta 'dauko sallama tayi ganin sunan Safwan ne ya 'kira.
" Hafsat kuna tare da Noor ne?"
Ya tambaye ta da sanyin murya sai ta amsa da " Erh ina tare da ita".
Yace
" Okay..ba sai kun taho ba ku jira mu muma gamu nan zuwa yanzu...".
Yayi maganar ne cikin sanyin murya, da ka ji kasan zuciyar sa a karye take.
Hafsat ma jikin ta sanyi yayi da jin yayanyin nasa amma sai tayi tuanin ko jikin su Mu'een 'din ne ya sashi canzawa.

Noor kam idanu ta zuba mata fuskar ta tallafe cikin hannun ta 'daya har ta kammala wayar sannan ta tambaye ta" wai ya akayi?"
" Yace kar mu koma..suma suna zuwa yanzu..'kila am sallamo su ne".

Goshi Noor ta tattare da alamun mamaki tace" Sallama kuma? naga 'dazun nan jikin Baby yayi  tsanani fa..ko de su Ammi zai kawo gida?"
Hafsat tace
" May be..kin gama sai kici abincin ki kafin su iso".
" Sako mana to inga ko zan iya ci...amma zuciya ta na tsinkewa".

Tashi Hafsat tayi ta ta nufi kitchen tana fa'din" Shai'dan ne ki dinga maimaita _Innalilliahi Wa Inna Ilaihi raji'un..._

Comment
Vote
Share

*Salmerh ce* 😍

💕 *NOORUL* 💕
      (Haske nah)

By
*Salmerh MD*

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

_*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

🅿 *79*

Hakan kuwa akayi domin  Noor cikin zuciyar ta ta ringa maimaiata _Innalillahi wa inna ilaihi raji'un_ har Hafsat ta dawo ta zuba musu abincin, a hankali ta fara ci amma sam sai nemi  natsuwar ta ta rasa, bugun da zuciyar ta ke yi sai 'kara yawaita mata yake yi, bata fi spoon biyar ba taji abincin ya ishe ta gaba 'daya, ruwa mai sanyi ta 'dauka ta sha sannan ta kwantar da kanta tare da lumshe idanu.

Ta 'dauki tsawon lokaci  a hakan Hafsat kanta bata iya fa'din komai cuz a yanda ta san Safwan da dukkan yanayin sa tasan da wani abu musamman yanda taji sauyi cikin muryar sa..amma da yake bata san ko menene ba shiyasa tayi shiru..fatan dai Allah yasa ba jikin Baby da mahaifin ta ne ya tsananta ba...tuno Sani da tayi ne yasa ta ta6e baki ashe har shima ba lafiya...

Wasa-wasa kusan mintina hamsin da uku suka 'dauka bayan wayar da Safwan ya 'kira sannan suka ji tsayuwar motoci kimanin uku daga harabar gida.

    Hafsat ne mai 'dan 'karfin hali dan haka ita ta fara mi'kewa tsaye yayin da zuciyar Noor ya amsa da 'karfi...'kafafun ta har na sar'kewa tabi bayan Hafsat Little Afrah kam tuni tayi baccin ta.

Ganin yanayin da su Ammi suka firfito daga motar yasa ta kasa motsawa daga inda take tsaye, bata san me yasa ta tsorata ba, a hankali idanun ta ya sau'ka kan  Bala Mai gadi da hannun sa duk biyu ke kansa yana kuma girgiza kan da alamun alhini.

Hakan ne ya 'kara tabbatar mata da cewa ba lafiya ba, gani tayi su Alhaji Baba, Safwan da wasu da bata ma gane ba sun tattaru wurin mota guda 'daya.
Dole cikin uku tasan akwai 'daya cikin Yah Deen, Jasmine ko Sani...Ammi ce ta taho wajen ta da sauri ta kamata tayi ciki da ita, da ka ganta kuwa zaka san cike take da damuwa, Noor dai kawai ta bita ne amma ba wai dan ranta yaso.ba, taso taga menene ya faru acan wajen, me su Alhaji suka taruwa gaban motar can.

Ji tayi kawai hawaye na gangaro mata yayin da zuciyar ta ya gama cika da waswasi..Ammi bata ce da ita komai ba har suka isa 'dakin ta da Ammi.
Anan ne Ammi ta fara bata ha'kuri da alamun kwantar da hankali  amma bata san dalilin ha'kurin ba..burinta kawai taji menene ya faru kuma.

Da 'kyar ta iya bu'dan baki tana hawaye ta tambayi Ammi" Me ya faru ne wai Ammi...?"
Kafin ta rufe bakin ta sai ji tayi murya kamar ta Hafsat tana Salati daga waje.

Ai bata san lokacin da ta zabura ta mi'ke da sauri ta fita ba, Ammi na 'ko'karin tarota amma ina ta riga tayi gaba.
.....turus taja ta tsaya sakamakon ganin abinda ke kwance a parlourn ta, gwiwoyin ta ta zuba a 'kasa kamar wacce hankalin ta ya bar jikin ta tana nuna abinda ta gani.

Da 'dayan hannun ta ta rufe bakin ta tana fatan Allah yasa zargin ta kar ya kasance gaskiya...Da muryar kuka batare da ta dubi fuskar Alhaji ba tace
" Alhaji Baba waye aka na'de haka?...Innalillahi...wa inna Ilaihi raji'un...Yah Allah kasa mafarki nake ba gaskiya ba..Hafsat waye wannan dan Allah?"
Da kuka ta rushe tana rufe bakin ta da dukkan hannuwan ta biyu, Ammi ce tazo ta kamata itama 'din hawaye take zubdawa...rungume kanta tayi a 'kirjin ta tana bubbuga bayan ta a hankali..tana fa'din" Kiyi ha'kuri Uwata...Kullu nafsin za'i'qatul maut...kinsan mutuwa dama dole ce..."

Bata jira ta 'karasa jin abinda Ammin ke fa'di ba tayi saurin barin jikin ta ta mi'ke ta tafi..jin cewa da gaske mutuwa akayi, kuma bata raba'dayan biyu 'yar ta ce domin duk cikin marasa lafiyan itace 'karama kamar yanda taga wannan abin.
Chapter 172 · 0% Book details