← Book details Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 131 OF 211

Sashe 131

Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ni kuwa da na fahimce ta sai na dinga 6oye damuwa ta agaban ta, sosai nake nuna mata babu komai ni cikin zuciya ta hakan kuwa ya matu'kar faranta ranta a yanda na lura.

A gidan Ammi Yah Deen yayi kwanaki biyun nasa har ya koma, sai bayan tafiyar tasa ne ma nake jin Ammi na labarin irin gyaran da za'a yiwa 6angaren sa na gidan saboda yace yanzu anan gida zai na zaman hutun sa har sai an kammala aikin wancen gidan gaba 'daya.

Nikam baki na ta6e cikin raina na furta damuwar sa ai ni me ruwa na..shi yasani da ba'kin halin nasa.

*****
       *Bayan watanni biyu*
Su saif suka dawo hutu, sosai zuciya ta ta cika da farin cikin dawowar su saboda sune dama abokan hira ta.

Har Ammi na min dariya lokacin da nake ta sauri da zumu'di wajen ganin na shirya musu lafiyayyen abinci.

Ammi ce ke gyara min ta na nuna min abinda ban yi dai-dai ba yayin da na zage na nuna mata 'ko'kari na sosai..ita kanta ta yaba min da 'ko'karin da nayi wajen saurin koyan kalolin girki sosai kuma ta bayyana min farin cikin ta kan haka matu'ka...tace tana so ranar da miji na ma zai dawo in yi masa fin na yau wanda zai manta inda kansa yake idan ya 'dan'dana..ta 'karashe maganar tana murmushi.

Ni kam da jin ta ambace shi sai na ta6e baki na a 6oye a fili kuwa shiru nayi, ganinbhakan yasa fa'din" Baki ce komai ba kuma".

Da sanyin murya nace" Ammi shi kam sai dai ke ki yi masa ni bazan iya ba kin san..."

Murmushin ta ta 'kara fa'da'dawa sannan tace" Ai tunda yayi aure nima na watsar da shi, ga matar sa na me zan sake dinga yi masa wahalar kuma ke de ki shirya kawai ranar da duk zai zo a kitchen zaki yini".

Ban kalle ta ba na shagwa6e murya nace" Ni dai Ammi a a".

" Toh shikenan naji".
Ta fa'di tana 'yar dariya.

*****
     Kamar de kullum Saif ne ka'dai me min fara'a acikin su banda Zaidu, shima Saif 'din yanzu sai naga duk ya canza min, duk da haka sai da nayi ta jera masa 'korafin share nin da yayi lokacin da nake wancen gidan da tafiyar da suka yi batare da sun min sallama ba.

Ha'kuri kawai ya bani yana fa'di kin san yanzu kin zama Miss Yaya sai a hankali, dole sai mun iya takun mu...yayi maganar yana 'yar murmushi daga haka kuwa bai sake fa'din komai ba har suka nufi wajen cin abinci.

Ko wajen cin abincin ma da suka fara yabawa take Ammi ta sanar da su ai duk nice nayi, bu'dan bakin Saif sai cewa yayi" Ashe yaya ya huta shi kam ya ji da'di".

Zaidu kam bai ce komai ba, Ammi kam murmushi kawai tayi yayin da ni kuma na kawar da kaina, na tsani wannan ha'din sam, ace komai nawa sai an dangana ni da shi.

Wani abu guda da na lura game da su yanzu shine kamun kai, ba kamar baya da muke zama muyi wasa da karatu cin abinci duk tare ba, yanzu kam hira ka'dai ke ha'da mu, hirar ma sai an ha'du a parlour lokaci zuwa lokaci.

Ammi ma taja kunne na game da zama da su ta garga'de ni da kame kaina matsayi na 'ya mace inda ta sake yi min tuni da igiyar Auren da ke kaina.

Nice na basu labarin mutuwar Ma'u inda duk suka nuna alhinin su sosai sai dai sam ban iya na fa'di musu asalin sanadin mutuwar tata ba na barwa zuciya ta..na kuma san ko Ammi ma da 'kyar ne ta sanar da su ainahin labarin.

Zuwan su Saif sosai ya 'debe kaso mafi girma daga cikin damuwa ta, yayin da farin ciki ya lullu6e ni gaba 'daya, sam na manta da batun Yah Deen na watsar da lamarin sa, sau tari sai dai idan cikin hira ake tuno min da shi ko kuma idan naje bacci wasu lokutan yake zuwa raina  har nayi bacci.

Satin su biyu da dawowa shima ya zo gida kuma gidan Ammi ya sau'ka dagaske...shiyasa naga an 'kara gyare 6angaren nasa an canza tsarin komai.

Sosai naga ya canza min ya sake zama babban mutum da shi ga kyau da ya 'kara komin sa tsaf, gashin kansa sai shai'ki yake yi sosai naji ya birge ni amma ban nuna a fili ba na cigaba da sha'a ni na.
Shima bai damu da ni ba duk da kuwa cikin ransa ba haka bane, amma ya basar...ko bayan isowar sa ban yi niyyan gaida shi ba amma da yake muna zaune ne da Ammi a lokacin dole na daure ba'kin hali na na gaida shi, sau 'daya ya kalle ni ya amsa da" Lafiya"
A ta'kaice.
Sanye nake da ba'kin Hijab akaina 'dan madaidaici cikin wa'danda nake zaman gida da su, hannaye na duk na daga ciki illah 'kafata, da yake ma ba'ki ne hijab 'din sai ya 'kara fito min da haske na sosai, da yake ma kwanaki biyu kenan da Ammi ta sa aka zo akayi min kitso har gida tace ayi min harda jan lalle ma mai zanen flower ya kuwa yi kyau sosai ni kaina ya birge ni...a lokacin ban san dalilin da yasa akayi min lallen ba, kawai dai ji nayi Ammi nata 'korafin wai na da'de banyi lalle ba sai kace ba mace ba, ni idan ba'a inyi ba da kaina bazan yi tunanin inyi ba...zato na ko haka kawai ne ta sa akayi min sai daga baya na fahimci ashe dan zuwan Yah Deen ne.

Tashin hankali na ya fara ne lokacin da Ammi ta zo da batun na daina kwana anan 'dakin daga yau lokacin ina shirin bacci na tace da ni in shirya in wuce wurin mijina ba anan zan kwana ba.

Take na marairaice fuska na fara yi mata kuka amma Ammi ko kula ni bata yi ba, sai ma zaman jiran in kammala shiryawar da tayi...tana fa'din ai Alhaji Baba ne yace ba ita ba idan kuma zanja da maganar sa ne to sai taje ta sanar da shi.

Jin sunan Alhaji cikin maganar ne ya sani yin shirin dole ba dan naso ba ina yi ina share hawaye na.

Duk yanda naso in nuna mata ni banson zuwa wajen sa amma Ammi fir ta'ki yadda a gaba ta tisani har parlour ta zauna tace maza in wuce tana kallo na, na kuskura na yi wani abin kuma ita da ni ne kuma sai ta gayawa Alhaji Baba.

Nasan zaman Ammi nan wurin babbar alama ce ta bayyana kafiyar ta akan zuwa na wurin nasa hakan yasa dole na wuce raina ba'ki 'kirin ina share hawaye.

Ammi kam murmushi kawai tayi da taga na wuce cikin ranta ta furta" Ja'ira abubuwa nata faruwa amma still hankalin ta bai kai ko'ina ba, haka kawai ta jefa sunan Alhaji cikin maganar saboda tasan shi 'din ina jin nauyin sa sosai ba kamar ita ba.

Lokacin kusan 'karfe goma ne na dare dan tara ra wuce tuntuni, zato na zan samu ma yayi bacci shiyasa da na isa sai da na tura 'kofar kafin nayi sallama ta ciki-ciki...ina saka 'kafata sai hoton sa da Husna ya dawo raina da sauri na tsaya cak sannan na 'daga idanu na kallo shi.

Zaune yake daga bakin bed yana duba cikin system 'din sa inda ya bada dukjan hankalin sa akai,  ban ji ya amsa sallamar da nayi ba sai dai kawai naga ya 'dago ya kalle ni, fuskar sa ba yabo ba fallasa haka muka tsaya kallon kallo inayi ina ha'de gira ta dan abinda ke cikin raina daban yake.

'Kasa yayi da kansa bayan ya gama 'kare min kallo sama da 'kasa, cigaba da abinda yake yi yayi batare da ya furta min komai ba.

Ganin hakan yasa ni jin wani sabon takaicin ya sake kamani, kawai sai na saki kuka harda sheshshe'ka.

'Dago kansa da kuma rufe system 'din nasa duk lokaci guda yayi su sannan ya mi'ke tsaye a fusace yana tambayar" na miki wani abu ne? Ko cewa nayi kizo ki dame ni?"

Ganin yana nufo inda nake ya sanya ni jan baya ka'dan tare da girgiza kaina alamar a a.

Cak ya tsaya, hannun sa 'daya ya shafo gashin kansa da shi sannan ya dube ni, zaiyi magana nai saurin taran sa da fa'din" Ammi ce tace in zo in yi bacci anan.."

" To kukan fa?"
Yayai tambayar yana kallo na.
" Ni banso".
Nace cikin muryar kuka.
Sai yace
" To na ri'ke ki ne? ki koma abinki mana".
Nace
" Ammi ai ta hana ni".

Yatsan 'daya ya 'daga ya nuna bed 'din sa dashi sannan yace" Wuce to ki kwanta bance ki dame ni da kuka da wannan daren ba".

'Kin motsawa nayi na cigaba da tsayuwa ta a wurin ina murza idanu, tsaki ya tsaki na takaici gami da 'kun'kunin yarinya kullum sai shirme.

Juyawa yayi ya shige bayi abin sa wanda ganin hakan yasa ni saurin 'karasawa gadon na haye na du'kun'kuna cikin hijabi na.

Kafin ya fito kuwa har nayi bacci, sau 'daya kawai ya dube ni sai ya 'dauke idanun sa haka ya gama shirin baccin sa ya kwanta gefe na ban ma sani ba.

Ko da safe kafin in tashi har ya tashi bama zaka ga wata alamar da zata bayyana maka cewa a gefe na ya kwana ba.

Inayin sallah kuwa na fice daga 'dakin nasa kamar wata marar gaskiya.

Kamar wasa tun daga ranar Ammi bata 'kara bari na na kwana a wani 'dakin ba sai a wurin sa, tun bana sakin jiki na har na zo na saba abin ya daina damuna.

Da nazo idan na gaida shi sai nayi kwanciya ta ko hira bata ha'da ni da shi.

'Bangaren Yah Deen kuwa shima 'din da farko bai wani damu da zuwan nawa ba, amma yau da gobe sai yake jin wani sabon yanayi na 'darsuwa masa a zuciya  game da ni.
Chapter 131 · 0% Book details