← Book details Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 93 OF 211

Sashe 93

Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tun daga ranar da aka sace Husnah iyayen ta basu sake natsuwa ba har yau da Husnah ta dawo gida hannun su, ko jiya ma sai da mahaifin ta yaje station wurin Nasiru driver yana kuka yana ro'kon sa kan cewa idan shine ya taimake shi ya sanar dashi inda Husnah take, yace shi ko duk dukiyar sa suke so duk zai basu amma dan Allah kar su ta6a masa lafiyar 'yar sa, kar su lalata mata rayuwa matsauin ta na ya mace matashiya su rufa masa asiri...amma Nasiru kuka kawai ya ringa yi bai iya ya furta komai ga mahaifin Husnah ba ya riga ya mi'ka ma Allah kansa bashi da wata mafita...dan shi yawan ku'din da yaji mahaifin Husnah yace anne ma a wurin sa ma ka'dai sun 'daga hankalin sa duk dama dai yasan Alhajin zai iya bafawa amma sosai hakan zai na'kasa tattalin arzi'kin sa...yana kukan yake ro'kon Allah ya tsare al'ummar musulmi daga dukkan azzalumai da masu sharri...to shi me zai sashi yincwannan 'danyen aikin da banda 'diban alhaki babu komai cikin sa, duk mummunan yanayin da yake ciki hakan bai sa ya kasa tausaya wa yanayin da Alhaji Hamza ya koma saboda 6acewar 'yar sa ba duk ya zama wani iri da shi ya fita hayyacin sa, hakan ma shine da yake matsayin namiji to inga mahaifiyar ta?
Tausayin ahalin ne ya sake ratsa shi...hakan yasa cikin ransa yake addu'ar" ALLAH ya bayyana ki Asma'u, Allah ya tona asirin duk wanda ya zalunce ki ya raba ki da iyayen ki, yarinya mai hankali da natsuwa abin alfaharin ko wani irin mutun, Allah ya tsare miki mutuncin ki kamar yanda mahaifin ki yake fata".

Haka har Alhajin ya bar inda yake bai furta komai agare shi ba...da ikon Allah kuma yau sai ga Husnah cikin gidan mahaifin ta cikin 'koshin lafiya.

Mummyn Husnah kam banda hamdala babu abinda take yi, godewa Allah kawai ta ringa yi da dawowar 'yar tata duk da kuwa zuwa lokacin hankalin ta ya kasu gida biyu ne amma a hakan ta basar farin cikin ya rinjayi tunanin inda mahaifin Husnah ya tsaya...ta bari akan cewa duk inda yake ai soon zai dawo ta sani.

Sai da suka gama koke-koken su kafin ta Husnah ta shiga wanka yayin da take jin tamkar ta shiga bayin ta yi mata wankan da kanta saboda so, wani zazzafan 'kaunar 'yar tata ne ya ninku mata cikin zuciya da yasa bata so ko nan da can ace Husnah ta matsa batare da ita ba, tun shigar Husnah wankan Mummyn ta bata zauna ba, ta gyara nan, ta kimtsa can duk sai ta rasa takamamman abinda ya kamata tayi ma gaba 'daya.

Sai dai duk da haka tunanin ta bai kauce kan binciken ingancin lafiyar Husnah ba, farin cikin da shiga bai sa ta mance hakan ba, tsoro take ji kar sunyi mata wani abin, sai dai ta bari cikin ranta da niyyar sai Husnah ta huta kafin su tattauna.

Tuni ta fitar mata wata doguwar riga mai kyan gaske da duk abubuwan da tasan zata bu'kata wurin shirya kanta.

Koda Husnah ta fito daga bayin Mummyn ta da kanta tai mata drying na gashin ta da hand dryer sannan ta bata dama ta shirya cikin doguwar rigar da ta ciro mata, kafin hakan sai ta wuce kitchen dan samar mata abinda za ta ci.

Mintina 'kasa da talatin ne suka 'dauke ta shirya abincin ta kawo mata.

Wannan karan a palour suka zauna dukkan su da sauran mutanen da ke cikin gidan tare da su.

Kowa yayi matu'kar farin ciki da bayyanar Husnahn, haka aka zauna ana maida zance ana kuma tuno ire-iren abinda ya fari da Husnahn ana bada misalai da su, yayin da Husnah ke cin abincin ta cikin natsuwa tana sauraren su...tana kuma sake tunanin irin rayuwar da tayi acan da mutanen da bata sani ba.

Ko mutun 'daya bazata ce ga kalar fuskar sa cuz basu ta6a gangancin zuwa inda take babu face mask ba wanda hakan ya kasance umarnin Alhaji Mamman ne, basu ta6a cutar da ita ko da wasa ba, dan ko bakin farcen ta babu wanda ya ta6a mata sam cikin su babu wanda yayi gigin kusanta kansa gareta, sun bata damar yin sallah sannan basu 'daure ta ba kawai 'dakin da take ciki ne kullum ba'a barin sa a bu'de, daga an kawo mata abinci da ruwa sai a sake datsewa ta waje...sau 'daya magana ya ta6a ha'da ta da wani shine ranar da aka ha'da ta da mahaifin ta cikin waya ranar ne ta san dalilin kama ta da suka yi, domin a lokacin taji mahaifin ta na fa'din ko nawane zai bayar shi dai su taimaka su sakar masa ita ta dawo gida...ranar kusan kwana tayi tana kuka da tausayin iyayen ta, shiyasa ma ta ringa addu'ar Allah ya kawo sanadin da zata bar hannun si cikin sau'ki...sai gashi kuwa da kansu sun 'dauko ta sun dawo da ita gida batare da sun yi mata komai ba.

Wannan tunanin da tayin ne ya sanya ta tunowa da mahaifin ta lokaci guda dan haka sai ta dubi mahaifiyar ta tace" Mummy ki 'kira Daddy na awaya mana kice masa na dawo ya daina nema na".

Take sai Mummyn Husnah ta 'dago wayar ta bayan ta jinjinawa Husnahn kai alamar gamsuwa da maganar ta.

'Kiran sa tayi da niyyar taji inda ya tsaya duk da ma dai tasan inda aka tura shi kaiwan ku'din da nisa sosai cuz can wajen gari ne amma ai tunda Husnah har ta dawo gida shima 'din kama ta yayi ace ya iso.

Sai dai ko tayi 'kiran sa sai bai 'daga wayar ba, missedcall uku ta jera masa ganin bai 'daga ba ya san ya ta tura masa text 'din albishir cewa Husnah ta dawo...ashe ma wayar tasa bata jikin sa tana cikin motar sa dake gidan Alhaji Mamman.

A fili tace da Husnah" Na 'kira bai 'daga ba, amma na tura masa text".

Shiru Husnah tayi yayin da sauran suka cigaba da hira bayan sun bata 'kwarin gwiwar cewa" Hakan ma yayi idan ya ga text din ma zai 'kira ko kuma yayi hanzarin dawowa ma gaba 'daya...".

Duk abincin taji tafi ce kanta shiru kawai tayi komai ya kwance mata.

Mahaifiyar ta ne ta lura da daina cin abincin da tayi sai tace" Eat mana Husnah..ki kwantar da hankalin ki kinji very soon zaki ganshi ya dawo da yardar rabbi".

"..To Mummy..Allah ya kawo shi lafiya, amma ni na 'koshi da abincin ne".

Kafin Mummyn Husnah ta sake fa'sldin wani abu sai wayar ta ta 'dauki 'kara, lokaci mintina takwas ne da 'kiran da tayi masa, da sauri ta 'dago wayar da tunanin ko shine ya 'kira amma sai ta ga sunan Hajiya Kareema ke yawo kan fuskar wayar.

Nan take kowa dake palourn suka yi tsit kamar 'daukewan ruwan sama suka baza kunnawa suna kallon Mummy da son jin abinda ke tafe da 'kiran wayar da akayin.

Afili Mummyn Husnah ta furta" Hajiya Kareema ce ta 'kira, ta fa'di hakan ne dan su san cewa ba wanda ake tsammanin bane.

Nan Hajiya Kareema take gaya mata cewa ai Alhaji 'Karami is unconscious yana asbiti ma yanzu haka....ta 'karashe maganar da sanar mata sunan asbitin da suke.

A rikice mummyn Husnah ta sa hannu aka tana sakin salati at same time tana kuka da hawaye wanda ya janyo hankalin Husnah da sauran izuwa gare ta...
Tsaye Husnah ta mi'ke a rikice tana fa'din" Mummy lafiya me ya faru kuma?"
Tayi maganar tana mai tahowa inda mahaifiyar tan take 'karara fuskar ta ta nuna alamun damuwa...Sauran ma tambayar da suka jefa mata kenan irin ta Husnah.

Tana cikin kukan tace da su" Wai bashi da lafiya yana asbiti".
Take palourn ya ru'de da salallamin jajantawa.

Mummyn Husnah kam cewa tayi" Wanda zashi ya shirya da sauri mu tafi...waiyo Allah na sun illata min shi".
Ta 'karashe da fa'din hakan tana nufar 'kofan fita.

Su hu'du suka tafi asbitin ciki harda Husnah, isar su asbitin ke da wuya sai ta sake 'kiran Hajiya Kareema ta kwatanta musu inda suke take suka nufi wurin sai dai likita ya hana su shiga saboda gudun hayaniya kuma wai zasu yi yawa a 'adakin.

A rikice Mummy tace" Doctor iyalan sa ne mu fa dan Allah karka yi mana haka...ki bar mu mu ganshi please bazamu yi hayaniya ba".

Tana hawaye tayi maganar, Husnah kam kuka harda sheshshe'ka take yi bata iya fa'din komai ba, sauran matan ma sai suka shiga ro'kon likitan amma ya kafe shi sam a a.

Hajiya Kareema na jin dramar tasu tana daga ciki ta fito da yake itan babbar likita ce a hospital 'din sai tace da likitan ya bar su su shiga 'kilan ganin 'yar san zai sanyaya masa rai duk dama tun zuwan su bai bu'de idanun sa ba, amma halin da yake cikin ya tsananta sosai...ga mutuwar gangar jiki saboda hawan jini sannan ga heart attack abin ba sau'ki gaskiya dole atausaya mai...bata iya ta bayyana farin cikin ta afili da ganin Husnah ba illah kawai ta janyo ta ta rungume ta tale kuma sai ta sake ta ta bata damar zuwa ta gana da mahaifin ta...daga haka ta wuce ta nufi office 'din ta.

Duk da Hajiya Kareemah tayi magana amma sai yace baza su shiga dukkan su ba dole sai dai da bibbiyu tunda su hu'du ne.

Nan sauran suka ce to Husnah ta shiga tare da mahaifiyar ta in yaso su 'din sa shiga daga baya.
Chapter 93 · 0% Book details