Sashe 35
Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Gaba 'daya tayi kaca-kaca da 'dakin amma bata ga komai ba kuma tana da tabbacin a 'dakin suke bai kai su ko'ina ba dan haka sai ta cigaba da dubawa da fatan Allah ya taimake ta can su....kamar daga sama kawai ta ganshi tsaye a bakin 'kofa dan ko motsin shigowar sa ma bataji ba tsaban yanda hankalin ta ya tafi.
Suna ha'da idanu da shi sai ta diririce abinda ke hannun ta ya fa'di 'kasa, batayi zaton zai dawo yanzu ba dan kuwa division yaje yin signing shiyasa ma ta saki ranta take binciken cikin kwanciyar hankali ko zata gansu tunda ya hanata ta da'din rai gara ta 'dauka tayi abinda ya dace dasu...ina amfanin ba'di ba rai" acewar ta kenan......
Da rawar murya tace dashi " har...ka....da wo?".
Sai yace
" Ke ma 'din na miki satan ne?"
ya tambaya a tsare batare da yabata amsar tambayar ta ba wanda daga jin yanayin muryar sa ma zaka san cewa ransa a 6ace yake.
Sai ta jijjiga kanta a hankali alamar " ah ah"
"So...?" Yace da ita da 'dagaggen gira 'daya.
Kwa6a fuska tayi kamar zatayi kuka gani da watsa hannayen ta tace dashi " please Taheer give me the documents i want use them...me yasa kake hakane wai?"
Cikin 'dakin ya 'karaso a hankali cike da 6acin rai ya nuna mata hanyar waje gami da fa'din " leave this room please"!
Tsayuwa taci gaba dayi cikin karya wuya da niyyan sake ro'kon sa amma kafin tayi magana sai ya daka mata tsawan " i said leave from here now"!
Fita tayi a hankali tana matse 'kwallan takaici.....yayin da Taheer ya rakata da jajayen idanun sa har ta fita.
Tana fita ya koma ya zauna bakin gado tare da dafe kansa, tunanin inda ya kamata ya 6oye takaddun kawai yake yi amma ya rasa, kuma baya so ya bawa kowa ajiya saboda gudun kar labari ya sake maimaita kansa...kar asake yi musu irin na Lawyer.
Sosai ya zurfafa tunanin har ya gano abinda ya kamata yayi....dan haka washe gari ya faki idanun ta tana kitchen yaje cikin 'dakin ta ya 6oye su inda yasan tunanin ta bazai ta6a zuwa wurin kwana kusa ba.
Ko bayan hakan ma tasha zuwa a 6oye tana bincikawa amma bata ta6a sa'ar ganin koda 'daya daga cikin documents 'din ba, har sai da ya kasance cikin 'dakin babu abinda bata 'daga shi ta canza masa mazauni ba saboda neman takaddun amma tarasa bata gansu ba.
Rashin sani ya sa bata ta6a ko kawowa cikin ranta cewa kullum tare take rayuwa dasu cikin 'dakin ta ba, shima dan yasan tunanin ta ba zai zo nan 'din bane shiyasa ya kawo su kusa da ita duk da hakan amma yakan saci jiki kullum ya je ya duba lafiyar su batare da ta kula da hakan ba.
*****
Kwanakin shiga kotu na 'kara 'karatowa yayin da abubuwa ke 'Kara shan kansu gaba 'daya, Addu'ah sukeyi ba dare ba rana... Hatta Ja'afar ba'a barshi abaya ba kamar yadda ya 'dau
al'kawari ga kuma tunanin inda zasu iya kammala ku'di mash uban yawa har haka sosai abun ke adamun sa.
'Bangaren Ammi kuwa sai take ganin kamar shi har yanzun bai wani damu da lamarin ba dan ko lawyern da Ja'afar ya nema musu ma 'kin bashi ha'din kai yayi acewar sa koma me zasuyi ba nasara zasuyi ba tunda bashi da proof ko 'daya da zai kare kansa dashi, dan haka su bari kawai ayanke masa duk hukuncin da suke ganin yayi musu he ll definitely accept it"
Cike da 6acin rai Ja'afar yace " haba Alhaji dan Allah...wai kai baka tunanin future 'din iyalan ka ne?"
Sai ya bashi amsa da fa'din...
" Duk wanda yake da 'dan uwa irin ka Ja'afar ai bashi da damuwar komai, na tabbata Mu'een bazai ta6a yin maraicin uba ba har abada matu'kar kana raye a duniya".
" ita kuma matar ka fa ya zakayi da ita... baka tausayin halin da zata shiga dalilin hakan ne?.... Me yasa ba zaka tausayawa maraicin ta ba?"
Ja'afar ya sake tambayar sa.
Kafin ya bu'di baki yayi magana sai Ammi ta taho da gudu ta rungume shi tana kuka gami da bugun 'kirjin sa tana fa'din " kawai ka kashe ni Taheer ka kashe ni ka huta dan Allah...wai ya kake so inyi ne fisabilillahi...baka son gani na ina farin ciki ko Taheer....?
'Kasa ta sulale tana kuka mai cin zuciya, haushin abubuwan nan da yake yi take ji, bata san manufar sa akan hakan ba, sam ta rasa wani irin zuciya ce da shi da har zai yi saurin yanke 'kauna da farin ciki so soon haka, me yasa ba zai bari su yi abinda ya dace ba, ko dama ya gaji da rayuwa da su ne shiyasa ko tausayin su baya ji zai bawa ma'kiyan sa daman cin galaba akan sa?"
Jikin Ja'afar sanyi yayi sosai dan haka sai yasa kai ya fice a 'dakin ya barsu su biyu.
'Kasan shima ya dur'kusa akan gwiwoin sa a hankali ya furta " Aisha.."
'Dago jajayen idanun ta tayi ta kalle sa da su sannan ta kawar da kanta gefe yana mai cigaba da zubar da hawaye.
Kai ya girgiza gami da fa'din " ke kina ganin tamkar duk abinda nake yi dan kaina nake yin sa ko Aisha? Idan kowa bai fahimce ni ba ai ke ya kamata ki fahimce ni, me yasa zan tauye miki hakkin ki in salwantar miki da dukiyar ki bacin bani da tabbacin cewa zan samu hanyar da zan biyaki abinki koda na rayu? Ke kina ganin hakan dai-dai ne idan na amince da batun ki?"
A fusace tace " ni nace maka zaka biyani ne?"
Murmushi ta'kaitacce yayi gami da mi'kewa tsaye tare da fa'din" bazaki gane bane Aisha, banfa saci abin kowa ba kuma sai in yadda naki dukiyar ya salwan ta saboda wasu can marasa tsoron Allah? kin sanni kin san hali na Aisha kinsan cewa bana saka kaina cikin abinda bai shafeni ba... ban nawa kaina magana tun farko, duk abinda kika ga ya faru dani to daga Allah ne, bance kince zan biyaki ba yanzu ba amma bazan 6oye miki ba wallahi har abada bazan ta6a iya cin dukiyar ki wai dan ni na rayu cikin farin ciki ba......"
Juyowa tayi ta kalleshi bai damu ba sai yaci gaba da fa'din ".....karki damu kinji...baki na yimin addu'ah kullum ba, nima kuma kinga inayi, kijira kiga ikon Allah tunda sharri ne ba gaskiya bane na tabbata Allah na tare da mu, in kinga ban tsallake wannan lamarin ba to 'kaddara wannan babban 'kaddara ce daga cikin babin rayuwa ta kuma dukkan mu ya kamata mu kar6e shi....duk abinda aka riga aka fawwalawa Allah shi to sanya wa ranki salama domin zai isar miki koma menene ".
Ammi sai tace
" What about the court...."
'Kyale su ni ba wani Lawyer da zamu 'dauka su suka sani...domin babu wani taimako da Lawyern zai mana sai dai ma cuta abanza".
Ammi bata 'kara magana ba illa binsa da idanu da take yi, sosai take jinjinawa taurin kai da kafiya irin nasa, yau ne ta yadda cewa lallai mijin ta mai tsantsan taurin kai ne, bata ta6a fahimtar hakan ba sai yanzu da wannan abin ya faru.
Haka ta ha'kura ta zubawa sarautar Allah idanu ba Wai dan task jakan ba... bata dai fasa addu'ah ba haka kuma zancen case 'din babu abinda ya canza.
Ana jibi za'a shiga kotun ne Manager da kansa ya 'kirashi ya sanar dashi cewa an janye maganar saboda an samo inda ku'din fuel 'din sukayi dan haka yayi ha'kuri.
Bai ce dashi komai ba illah lumshe idanu da yayi gami da fa'din Alhamdulillah cikin zuciyar sa tare da yanke 'kiran gaba 'daya.
Hawaye kawai yaji ya gangaro masa masu sanyi, tun fitar sa daga station bai 'kara zubda hawayen sa ba sai yau 'din da yake yiwa Allah godiya bisa ga babban taimakon da ya yiwa rayuwar sa.
Batare da ya sanar da Ammi ba ya shirya ya tafi Division 'din inda suka sake yi masa bayani gami da neman saka hannun sa na 'karshe tare da ban ha'kurin tuhuma inda suka 'karashe da fa'din " haka aikin mu ya gada ka gafarce mu visa abubuwan da suka faru.
Bai damu da wannan ba shi dai kawai fatan sa ya isa gidan sa ya sanar wa da Ammi wannan babban abin farin cikin da ya same su a yau.
Tunowa da yayi cewa jiya-jiya Ja'afar ya wuce Azare da niyyar gobe zai dawo a shiga court 'din dashi sai taji matu'kar tausayin 'kanin NASA..... dan sau'ka'ka masa tafiya sai yana fita daga ofishin 'yan sandan ya doka masa 'kira gami da fa'din " albishirin ka lil bro".
"Goro fari 'kal Alhaji...amma duk girmana mana 'kiranka Lil ai sai Mu'een ya min dariya..... nd kuma irin wannan albishir da kake min Allah yasa dai ku'dine suka bayyana"!
" Kusan hakane 'dan uwa domin kuwa an kori wannan case 'din i'm free now ba sai kazo goben ba".
Washe baki Ja'afar yayi gami da hamdala daga 'dayan 6angaren sannan ya 'kara da fa'din " ai zuwa dole ne Yayah, dole inzo muyi murnar tare...insha Allahu gobe ina hanya...kai masha Allah..... Allah ka 'kara rufa mana asiri".
Amin yace tare da yanke 'kiran.
Yana shiga palour da Mu'een ya fara cin karo sai yayi saurin 'daga shi da murnar sa yana dariya.
Shima Mu'een dariyar yake yi ganin mahaifin sa da ya jima baiga dariyar sa ba yau yanayi dan haka shima da 'karfin gwiwar sa yake darawa.
Hayaniyar sune ya fito da Ammi daga 'daki inda ta 'karaso da bu'd'den bakin mamaki tana kallon sa, fara'ar da take gani yau 'din direct take hango shi har cikin zuciyar sa domin kwata-kwata bai yi kala da na ya'ke ba.
Ganin kallon da take yi musu ne ya sanya ya shi sau'ke Mu'een gami da fa'din je kawo min ruwa insha kaji".
Da gudu yaron ya tafi yayin da Taheer yayi saurin tunkarar Ammi ya ha'de musu fuska gami da fa'din " ur husby is free now an kori shari'ar mu gaba 'daya".