← Book details Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 78 OF 211

Sashe 78

Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zaune suke kan Dinning daga shi sai ita da yake dama babu kowa gidan, Ammi ce da Alhaji da ni, Alhaji Baba kuwa tuni ya fita, ni kuwa ina 'daki ina bacci, shi ma 'din breakfast yazo yi shine suke zaune tare da Ammi, abinda yayi sosai yake bata haushi amma dan takaici ma sai ta tarasa me zata ce da shi...sai dai ko ba'a fa'da masa komai ba shi kansa yasan sakin fuskar da take yi masa kaso mafi yawa daga ciki babu shi yanzu, hatta gaisuwar sa a yatsine take amsawa kuma daga gaisuwar bata 'kara wani hira mai tsayi da shi sai dai be san dalilin faruwar hakan ba sam kuma bai tambaye ta ba.

Yah Deen ya saci kallon inda take a 'kalla kusan sau uku amma ya kasa furta abinda ke ransa, musamman dan ganin yanayin da fuskar ta yake ma...sai ana hu'dun ne kafin ya iya dauriyan 'kiran sunan ta cikin tsohuwar shagwa6ar da jima bai yi mata ba.

Da idanu kawai ta iya kallon shi sai ta kuma sau'ke idanun batare da ta furta komai ba.

Ganin hakan ya sanya shi yin gyaran muryfa tare da gyara zaman sa da kyau ya wani buga uban tagumi sannan yace" Dan wai ni Ammi laifin me nayi kwata-kwata yanzu bakya 'kauna ta..ko dan na daina zama a gidan nan ne?"

Ammi bata kula shi ba kawai ta cigaba da abinda takeyi koma kallon inda yake bata sake yi ba.

Bai 'dau abin wani serious ba dan iya tunanin sa bai hango laifin da yayi mata ba, hakan yasa yayi saurin kauda wancan zancen da fa'din" Ba ma wannan ba Ammi ni kwana biyu ban ganin 'yar kin nan ko tayi tafiya ne?"
Kamar ba zata yi magana ba sai can kuma tace" Wace 'yar ta wa kenan?"

Yah Deen cire tagumin yayi jin ta kula shi, har da 'dan ha'de gira as if tilasta shi akayi yin maganar yace..."..Nu..Noor ce wai ko ya ma sunan ne na manta".
Ya 'karashe da yatsina fuskar sa.
Cikin kwantar da murya Ammi tace" Baka gaji da bautar min da ita ba kenan?"
Tayi magnaar tana ajiye spoon 'din da ke hannun ta tare da gyara zaman ta.

Yah Deen kam ido ya zaro da mamaki yace " Ni kuma Ammi?"
" a a Ubanka...!"
"Toh ni Ammi wani irin bautar da ita zanyi?"
" Ka fini sani ai.. ko in ba hakan ba me yasa ka tambayar ta...ko kashe tan kazo yi har gida kamar yadda ka yi niyya?"
'Dan 6ata rai yayi dan ya fahimci inda zancen ya dosa a hankali yace
" Nifa Ammi ba haka bane...kawai danna tambaye ta laifi ne?"
"....Babba ma kuwa!....kai yanzu ko kunya baka ji sai kasa yarinya 'karama irin wannan agaba bacin kasan lokacin zuwa makaranta ce kai haka akayi maka?"
Shiru yayi ya 'dan lumshe idanu yana sauraran ta.
A tsawace tace " I'm asking haka akayi maka?"
Bu'de idanun nasa yayi da tuni har sun canza launi zuwa ja bai kalle ta ba kawai ya zubawa table 'din dake gaban sa idanu.
Yayin da Ammi ta cigaba da fa'din"...kai me yasa ka koma can gidan ba cewa kayi dan kayi karatu bane...shine dan iskanci ita kake 'ko'karin hanata nata zuwa nata makarantar karatu yafi karatu ne?...ko kuwa tsabar ka raina ni ne yasa hakan?"
Ta 'karashe maganar tana kallon sa.
A hankali ya 'daga idanu ya kalle ta tare da fa'din
"...Dan Allah Ammi kiyi ha'kuri..nifa ba nufi na kenan ba".
Kwafa tayi gami da fa'din
" Ohh nufin ka 6ata raina ko?"
" Haba Ammi?"
" Yi min shiru da Allah, me kuma zaka sake fa'da min tunda duk girman baka san kayi abinda ya dace da kanka ba har sai an tunatar da kai, and this is my last warning Mu'een wallahi ka kiyaye ni, idan ka kuskura na sake jin abu makamancin hakan ya faru zaka sha mamaki na, ni da kaina zan 'dauki mataki tunda ba kai ka kawo ta gidan ba, kaje kayi rayuwar ka acan babu ruwan ka da yarinya ta, ka bar min ita sha iska, ai kaima babu wanda ya takuraka dan haka ka ka bar min yarinya ba ita ta turaka can 'din ba so babu dalilin da zaka 'daura mata nauyin da ko ni ban 'daura mata ba ..."
Taran ta yayi da fa'din"..Ni dai kiyi ha'kuri Ammi.."
" Sai yanzu kasan da ha'kurin ai...kwanan yarinyar nawa ba lafiya amma baka ta6a tambayar ta ba sai yau da kake so tayi maka bauta kafin ka iya tambayar ta har ka bada ha'kuri ko..?..i thought ni dai muka rufe zancen tun da 'da'dewa..dan munafurci shine ka zagaya da yake isheshshe ne kai shiyasa ka nuna min ban isa ba, jibi yanda yarinyan duk ta 'kare ta lalace, ko tausaya mata baka yi dan mugunta....".

Murmushin dole ya 'ka'kalo ya sanyawa fuskar sa, dan ya fahimci masifar Ammin ba mai 'karewa bane...in dai akan wanna 'yar ne Ammi gwana ce wurin masifa...balle shi da ta kama dumu-dumu da laifin da acewar ta bautar mata da 'ya yake yi..." ko itan ba mace bace oho.." Yayi maganar cikin ransa.

A fili kuwa cewa yayi
"...Ai ban sani bane Ammi shiyasa...ina take in duba ta".
Tsaki Ammi taja ta kawar da kanta gefe, Yah Deen kam wani murmushin ne ua kubce masa sai ya mi'ke ya nufi 'dakin Ammin....tura 'kofar yayi a hankali sai ya hango ni zaune ina shirin sau'ka daga kan bed.

Tsaye yayi a 'kofa yana 'kare min kallo, koka'dan baiyi regretting abinda ya aikata ba, bai ma ji cikin ransa cewa laifi ya aikata ba in ka 'dauke abu 'daya shine lattin schhol da nake yi bayaga haka kuwa zuciyar sa fes.

Ni kam ina ganin sa sai zuciya ta ta tsinke da 'karfi take nayi narai-narai da idanu tamkar zanyi kuka..jiki na ya fara 6ari.

Sai da ya kuma waigawa ya kallo baya bansan abinda yake dubawa ba kafin a hankali ya 'karaso ciki ya iso gaba na ya tsaya yana kallon duk yanayin da na shiga.

Ni kam tausayin kaina ya sani zubda hawaye ina sunkuyar da idanu na 'kasa..farar shimi ce a jikina da wani skirt 'yar kanti da Ammi ta siya min, kaina ba ko hula sai tsefaffen gashi na da jinyar da nake yi ya hana ai min kitso har ranar.

Sai da ya gama 'kare min kallo wai ko zai hango ramar da yaji Ammi tace nayi amma shi kam bai fahimta ba ko dan bai san yanayin jiki na kafin faruwar hakan bane oho, iya abinda ya sani game da jikina tun farko dama shine banda wani jiki, to ko yau din ma iya abinda zai iya fa'di kenan bai ga sauyi ba, yana folding hannun sa a 'kirji yace
" Miye hakan kuma ?"
In da yayi maganar cikin natsuwa..sai na 'dago kaina na kalle shi..take kuma na sake yin 'kasa da kaina hawaye na gangaro min.
Sau'ke hannun yayi a 'kirjin sa ya cusa cikin aljihun wandon sa kafin yace
"... Ba cin kin riga ki fa'da har ta yi min masifan kuma miye na kuka? ko zazza6in ne ya tashi da gani na?"
Girgiza mai kai nayi alamar a a.
" To ya akayi?"
Ya sake tambaya ta.
Da muryar kuka nace
"..Dan Allah Yaya kayi ha'kuri kar ka kashe ni..ba zan sake ba, bazan sake gaya mata ba"!
Bai bi ta kan wancan maganar tawa ba kawai yace
" Me ke damun ki wai?"

Kafin nayi magana naga yayi saurin zama gefe na wanda sai da ga zauna 'din kafin nima na jiyo takun tafiya, take kuwa sai naji da'di har cikin raina dan nasan Ammi bazata bari ya cutar da ni ba kamar yadda take fa'da min kusan kullum.

Yah Deen kam harda kama hannu na tare da maimaita tambayar da ya min da farko kafin ya zauna...inda ya sake yin tambayar yana ta6a jiki na zuwa wuya na.

Ganin haka yasa nayi saurin bashi amsa da fa'din
"..Zazza6i"!
" Sannu.." Yace dai-dai sallamar Ammi da shigowar ta cuz batare da ta jira an amsa ba kawai ta 'karaso ciki.

Yah Deen kuwa har shigowar Ammi bai saki hannu na ba shi nan adole ya nuna mata cewa he cares for me..but ni ka'dai na san me yake min da hannun nawa, palm 'dina ya ri'ke cikin nashi dan haka sai ya cusa yatsan sa 'daya cikin tsakiyar hannu na a hankali yake yawo da shi wanda babu ta yadda mutun zai fahimci hakan in ba ni da shi da muke zaune ba..cuz ko Ammi da ta shigo bata lura da hakan ba idanun ta kan fuska ta batare da ta ko kalli inda yake ba ma tace " Kin tashi ko?"
Kaina na 'daga mata sama sai tace " To ki samu ki watsa ruwa sai ki same ni can parlour...magungunan ki basu 'kare ba..idan kin yi breakfast sai ki sha ko?"
Kai na 'daga mata ina marairaice fuska.
Wayar ta wuce zata 'dauka acan gaban mirror ganin haka yasa nayi yun'kuri nima da niyyar tashi cuz Allah-Allah nake ya bar inda nake, sai dai wani kallo da ya watsa min ya sanya nayi saurin komawa na zauna kamar yadda nake da farko still kuma bai saki hannun nawa ba bansani ba ko mancewa yayi da ni 'din wacece.

Har Ammi ta 'daukp wayar ta juya bai ce da ita komai ba haka nima, ganin tana shirin fita bata tanka shi ba ne yasa shi tambayar " Ammi wai meke damun ta ne?"
" Ka tambaye ta mana gata gaban ka ai".
Ta bashi amsa batare da ta ko kalle shi ba kawai tayi waje abin ta.

Murmushi ya saki batare da damuwar komai ba, dama ya san ba amsa mai kyau Ammi zata bashi ba kawai ya tambaya ne dan rasa abin fa'da shi a dole kar tace bai damu da jinyar tawa bane dagaske.
Chapter 78 · 0% Book details