← Book details Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 141 OF 211

Sashe 141

Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

" Yauwa Uwata kuma banda zargi kinji? domin Zargi na da matu'kar muhimmanci wajen lalata darajar aure, komai da yafaru ya wuce kar ki saka cikin ranki balle ki tuno da shi har ya gur6ata miki tunani, kowa da kike gani.yana da nasan mugun.halin a 6oye bambancinnkawai na wani yafi na wani.ne shiyasa ba'a fiya gane wa ba".
Nace
" Hakane Ummah".
Sai ta cigaba da fa'din" Ma'u kam 'kaddara ya riga ya hau kanta sai dai muyi fatan Allah ya ji'kan ta da Rahama Allah ya tsare 'yan baya..ke ma kici gaba da Addu'ah ubangiji Allah ya kawo miki shiriya cikin gidan ki..wannan karon kam matu'kar naga da cutar wa bazan bari a salwantar min da rayuwar ki ba da kaina zan 'dau mataki, Ke de ki kwantar da hankalin ki, ki nutsu ki bi mijin ki kinji Uwata?".

Kuka na rushe da shi sosai tuno Ma'u da nayi, yanzu har abada wannan ba'kin fentin bazai barni ba, a kulluma za'a dinga kallona ne matsayin matar Deen wanda yayi sanadin ciki ga Ma'u daga 'karshe ma ta rasa ranta gaba 'daya..bana so in dinga yawan tuno wannan incidence 'din domin.gaba 'daya yake tunamin da dukkan rayuwar Yah Deen da na sani tun abaya har zuwa zama na da shi agidan sa, ji nake tamkar idan na 'kara cin karo da irin hakan daga gare shi mutuwa zanyi...cikin kukan na bawa Ummah ta tabbacin" Insha Allahu bazan bata kunya ba".

Sarai nasan gaskiya itama take fa'da min, amma Ummah bata san ni abinda na gani da idanu na ba cikin halayyar Yah Deen da na tabbata ba kowa ke da irin ta ba, ita kanta Ummah da tasani nasan da bazata fa'di wasu abubuwan ba, to ma ta ina zan fara gaya mata sam bazan iya ba..hakan yasa na 'kara sunkuyar da kaina kawai na cigaba da kuka na...rayuwar Yah Deen kacokam 'din ta wata iri ce, a yanda nake.jin zuciya ta ji.nake da ba Ammi bace ta haifi Yah Deen da ko Soyayyar shi zata yi ajali na ne da kuwa zan sadaukar da zuciya ta in mutu da in amince yin zaman aure da shi..amma ina Ammi da Alhaji Baba sunfi 'karfin hakan awaje na.

Jikin ummah na kwantar da kaina sai ta 'dago hannun ta ta 'dora saman kaina sannan tace" Allah ubangiji ya albarkaci rayuwar ki Uwata, Allah ya baki zaman lafiya da mijin ki, ya ha'de kanku ya kawar da shai'dan tsakanin ku".
Ban iya na amsa ta koda da kalma ba kawai na cigaba da aikin kuka na.

Ummah kam daga haka bata 'kara fa'din komai ba shiru muka zauna na tsawon lokaci, tana sake lallashi na ganin Ummie ta dawo daga gidan Yayah Usman da ta je ne ya sata fa'din maza inyi shiru in shiga ciki in huta kafin anjima dan kar Ummie ta fahimci yanayin da nake ciki.

Da yamma kafin azo 'dauka ta Ummah ta bani wani magani ha'di da kindirmo tace inshanye, haka na 'daga na sha ina 6ata raina na goge baki na.

Wata 'yar roba ta bani mai 'dauke da ha'din zuma tace insa cikin jaka ta sai mun tafi can Bauchin sai in ringa sha ka'dan-ka'dan nace to.

Ba'a jima ba sai aka zo 'dauka ta daga nan muka yi sallama da Ummah ta na tafi, banje gidan kowa bama hatta Addah Saudah banje nayi mata sallama ba haka ma gidan Yah Usman...duk na bari ajan zan 'kira su daga baya.

Wannan karan kam" ina yini" Nace da shi jin ya amsa sai na kawar da kaina, sau 'daya tak na kalle shi ban sake kallan inda yake ba, jikin sa rigar Jessy ce ja cikin wa'danda yake zuwa wasan ball da su sai ba'kin dogon wandon jeans da ya sanya, kansa sai tarin kwantacciyar suma da ya saba tarawa.

Gefen hanya na maida idanu na ina bi da kallo yayin da yake tu'kin cikin hankali tamkar ba shi da niyyan jan motar.
Kamar daga sama na tsinci muryar yana fa'din" Kinje kin ta yiwa Ummah kukan naki ko?"
Kallon sa nayi saurin yi batare da nayi niyyan bashi amsa ba, sai yace" Dubi yanda idanun ki suka yi ja dan Allah..baki son mu tafi taren ne?"

Jin tamabayar da yai min daga 'karshe yasa da sauri na 'dage kaina alamar" Erh" zato na ko zai ce to inyi zama na ne, ga mamaki na kuwa sai ji nayi yace" Toh ai sai ki kashe kanki kafin ranar tafiyar tunda ni cinye ki zanyi idan kin bini".

Shiru nayi ban ce da shi komai ba, cikin zuciya ta nake jinjina ba'kin hali irin na Yah Deen, shi dai a kullum bai canzawa halin sa na nan tare da shi sai mugun hali da ba'kar magana kawai ya iya tsarawa.

Kaina gefe nace" Ni dai kam bazan je ko'ina da kai ba".
" Wai saboda mene...ni in ba mutun bane da baza'a bini ba?"
Yayi maganar cike da murmushin mugunta.
Cikin shagwa6e murya nace dashi" Ai wasu mata kake kawowa gidan ka kullum kuma ance babu kyau".
Na fa'di hakan ne saboda abinda ke cikin raina yake cimin zuciya kenan.

Dariya ma maganar tawa ta bashi a yanayin da na yita tamkar yara 'yan goye, amma sai yayi murmushi madadin dariyar, bai kalle ni ba tunda na fa'di hakan, dama yasan dole har yanzu hakan na nan cikin raina bn manta ba, kallo na yayi sau 'daya sai kuma akayi sa'a nima 'din bashi nake kallo ba so ban ma san ya kalle nin ba, sai da ya maida idanun sa kan hanya sannan yace" Kar ki damu yanzu ke ka'dai ce bazan 'kara kawo kowa ba kinji". Fuskar sa ba yabo ba fallasa yayi maganar amma shi ka'dai yasan yanda yaji furucin nawa cikin zuciyar sa, abu ne wanda ya matu'kar girmi lissafin koma waye idan yaci karo da shi, wanda ko shi da kansa ma ba iya jura zai yi ba misali ace ya kama abokiyar zaman sa dumu-dumu cikin wancan halin, yasan Allah ne ka'dai yasan me ze faru da shi alokacin dan yana ga har kisa zai iya yi in ba Allah ya tsare shi ba, amma yarinyar nan ta gansa da idanun ta kuma tayivshiru ta rufe masa wannan sirrin duk da 'karancin shekaratun amma sosai ya jinjinawa bajintar da tayi.

Bazai 'karya ta zuciyar sa ba ya sani faruwar hakan shine babban dalilin da yasa shi tsintan kansa cikin zazzafan soyayyar ta da yayi, sau da dama ko yana school idan ya tuna sai ya dafe kansa, ko da shika'dai ne zaune amma haka kawai sai yaji ya tsinci kansa cikin matsanancin jin kunya haka kawai karma ace ya tuno da Hudah wannan kam sosai tunota yake tsuma zuciyar sa.

Bance da shi 'kala ba kawai na kawar da kaina gefe...

Sai can naji ya sake fa'din" In tambaye ki?"
Kallon sa nayi sai na kawar da kaina tamkar abokan gaba, cigaba yayi da fa'din" Kin gayawa Ummah ne cewa wata ta tazo gidan mu kwanaki?".
Kaina na girgiza masa alamar a a, sai yace" Ammi fa?"
Nan ma kaina na sake girgizawa sai naga yayi murmushi harda lumshe idanun sa sannan ya bu'de bai kalle ni ba yace" In ma kin fa'da cewa zanyi mafarki kika yi ba gaskiya bane".
Tunani yake cikin zuciyar sa cewa ai dama yasan matu'kar ban bada labari a lokacin da abin ya faru ba da 'kyar in sake iya furta galibi 'dan adam nada wannan halayyar.

Baki na ta6e ni kam 'kasa-'kasa nace" Ai Allah ya gani".
Ko da na fa'di hakan ma sau 'daya kawai ya kalle ni daga haka kuma bai sake kallo na kamar yadda bai 'kara fa'din komai ba har muka isa gida.

Da shigan mu gida kuwa ina yin arba da Ammi sai ta kama bakin ta tace" Ikon Allah..haba Mama na yanzu zuwa kika yi kika yini kuka wa Ummahn naki ko? Dan Allah dubi yanda idanun ki duk suka 'kan'kance kuma nasan duk kuka ne ya kawo hakan".

Shiru nayi bance da ita komai ba sai ta jijjiga kanta kawai ta shige ciki.

Washegari Ammi ta tura ni yin kitso da lalle tamkar wata sabuwar amarya..ma'kudan ku'da'de ta kashe wajen ganin an tsara ni yanda ya kamata, nikam ma anayi ina tura baki na har raina bana so.

Tun ranar da muka rabu bayan ya sau'ke ni daya 'dauko gidan Ummah shikenan babu abinda ya sake shiga tsakanin mu, baya shiga sabgata haka nima ban kuma da shi ba sam...mu kan gaisa dai idan mun ha'du da safe ko rana ko yamma sai in gaishe shi.

Ranar da yashigo bayan sallar azahar ya tarar ina waya da su Saif tsayawa yayi ya 'kare min kallo yanda nake fama walwala da sakin fuska baki ya ta6e ya shige ciki ni ban ma kula da shi ba, sai bayan kamar mintina sha biyar sai naji wayata na ringing sunan sa ya bayyana kan fuskar wayar kamar yanda nayi saving" YAH DEEN".
Sosai zuciya ta ta tsinke da ganin 'kiran cuz na jima banga hakan cikin wayata ba.

'Dauak nayi na kai wayar kunne na sai naji yace min" Kawo min wayar ki zan duba abu".

Baki na tura sannan na yanke 'kiran.

Ko da na kai masa wayar kar6a yayi yace inje zai kawo min.

Haka na fita ina 'kukkuni cikin zuciya ta.

Kamar wasa ranar wata laraba Ni da Yah Deen muka bar Shuwarin zuwa cikin garin Bauchi, da kansa yayi driven motar cikin 'daya daga cikin motocin gidan Alhaji Baba...tunda kuwa ya fara tafiyar babu ko kalma da ta ha'da mu, lokaci zuwa lokaci na kan goge hawaye na a haka har bacci yayi awan gaba dani.

Da yake ma baya bin mota da wasa hakan yasa bamu wani da'de ba muka isa.
Kafin lokacin ma na jima da farkawa domin baccin nawa bai wani yi nisa ba, sai da muka shigo cikin garin kafin ya tambayi me nake so nace da shi bakomai, bai tsaya ko'ina ba direct gida muka wuce.

Comment
Vote
Share

*Salmerh ce* 😍

💕 *NOORUL* 💕
      (Haske nah)

By
*Salmerh MD*

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*
Chapter 141 · 0% Book details