← Book details Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 151 OF 211

Sashe 151

Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ni kam bance da shi komai ba, a hankali ya kwantar da kansa saman kafa'da ta, ya lumshe idanu sannan yace" Kin gama min komai Nuree, yau kin bani farin ciki, kin sada ni da sanyin idaniya ta..ubangiji Allah ya bamu ikon tarbiyantar da ita cikin muslunci bisa sunnar ma'aiki (S A W).."
Da" Ameeen" na amsa 'kasan ma'koshi na dan ni ka'dai nasan abinda nake ji a lokacin.

'Daga kansa yayi daga jikina sai yasa hannun sa 'daya ya bu'de fuskan babyn" Masha Allah"!
Ya furta a fili.
Sannan ya sake fa'din
" Allah nagode maka, yau gani ga jini na.."
'Dagowa yayi ya kalle ni yace" Kinsan sunan ta?"
Girgiza kaina nayi ina kallon sa, sai yace min" Sunan ta Aishatul Amin, my Jasmine.."
Murmushi nayi masa cikin jin da'di nace" Allah ya raya ta".
Raina fari 'kal dan nasan sunan Ammi na yake son sanyawa Babyn.

Motsi tayi tana 'dan mimmi'kewa cikin kayan ta Pink da aka sanya mata, Yah Deen yatsan sa yayi saurin sanyawa cikin hannun ta ai kuwa take ta ri'ke gagam kamar an ce mata ta aiakata hakan ne.

Comment
Vote
Share

*Salmerhn ku ce* 😍
💕 *NOORUL* 💕
      (Haske nah)

By
*Salmerh MD*

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

_This page is specially dedicated to my luvly sis...Zainab Kabir Ingawa_ 😍 _Godiya nake 'kwarai da gaske._

_*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

🅿 *71*

A fili ya bayyana murmshin sa cike da jin da'di ya 'dagota ya sumbaci goshin ta" I luv u ".
Ya furta a hankali.

Wayar sa ya ciro ya 'dauke ta pics kala-kala sannan ya maida wayar cikin aljihun sa, ni kam kallon sa kawai nake yi, da gama 'daukan pics 'din sai ya kwantar da ita a hankali kamar 'kwai ya sake lullu6e ta.

Gareni ya dawo ya sumbaci goshi na..fuskar sa daf da tawa ya tsaya kallon cikin idanu na.
Yi nayi kamar zanyi kuka sai yayi saurin tambaya ta" Me kike so?"
" Ni bakomai".
Na bashi cike da shagwa6a in kwa6a fuska ta.
Girgiza min kai yayi yace"  Ban yadda ba".

Shiru nayi ni kam nayi 'kasa da idanu na zuwa kan hannu na.
Shima nan ya maida idanun nasa, batare da 6ata lokaci ba ya kai hannun sa kan nawa.

Yatsu na ya sanya cikin nashi ya sarke su, a hankali ta yadda ni ka'dai zan jishi yace" Ji nake kamar dukkanin farin cikin rayuwa ta yana tare da ke ne Nuree please tell me what u want".

Ban bashi amsa ba sai na girgiza mai kaina.
Hannun nawa ya sake ya dube ni da kyau sannan yace" To bazaki kwanta ki huta ba zaman yafi miki?"

Da yake dama na gaji da zaman, da jin abinda ya fa'di sai na sake mi'ka masa hannu na 'daya, shine ya gyara min kwanciya ta yanda zan dinga hango babyn, kusa da kaina ta yadda ni.ka'dai yanzun ma ya kawo kansa a hankali ya furta" Nuree bacci ki huta kinji?"
Da kai na amsa shi.
Sai ya sake fa'din" Zan fita amma bazan da'de ba...Mummy ma na nan in kina bu'katan wani abu ki gaya mata kinji?".
" To" nace da shi murya ta 'kasa-'kasa.
Sai da ya shafi fuska ta sannan daga haka ya fice daga 'dakin.

Anty Zainab, Ishaq, Saif da kuma Zaidu su yayiwa  forwarding photon Babyn kowa 'da'd'daya...yana gama turawa kuwa ya danna flight mode a wayar sa.

Saif na kan WhatsApp a lokacin so shi a take ya ga sa'ko daga Yah Deen, ko da ya bu'de kuwa photon Baby ya gani 'kasan an rubuta _My Diamond_ ai da sauri ya mi'ke ya nufi 'dakin 'dan uwan sa, Zaid na baccin sa kawai yaji an 'daka masa duka gami da fa'din" Zaid tashi kaga ikon Allah....".
Saif ya fa'di cike da 'kaguwa.

Tsaki Zaidu yaja ya juya 'daya 6angaren yana 'kun'kunin Saif zai dame shi da wannan lokacin.

Ganin hakan yasa Saif bar masa 'dakin ya ja 'kofan, direct wurin Ammi ya tafi, yana isa wajen ta kawai ya mi'ka mata wayar sa yana murmushi yace" Ammi guess what?"

Kallan wayar tayi tace" Me ya faru? Kamar Baby nake gani ko?"
Tayi maganar tana mai kar6ana wayar daga hannun sa.

Hannu Saif ya 'daga yana murmushi yace" Ammi Yaya ne ya tura min yanzun nan, ina jin mun samu little pumpkin ne a gidan nan".
Ya 'karashe maganar da tsananin farin ciki kan fuskar sa.

Ammi da mamaki ta kalle shi sannan tace" Kar dai 'yata ce har ta haihu? shine Mu'een ko.sanar da ni bazai yi ba? me ta haifa kuma ikon Allah"

Saif cewa yayi" Nima ban sani ba Ammi kawai 'kira mana Yayan muji daga bakin sa".
Mi'ka min wayata a can ta fa'di tana me 'kara kallon wayar Saif 'din tana murmushin jin da'di.

Cikin rashin sa'a kuma ko da ta 'kira sai wayar tasa bata shiga ba, duk layukan sa ma a rufe suke abin sai ya 'daure mata kai gaba 'daya.

Tama cikin Jimantawa sai ga 'kiran Anty Zee ya shigo wayar ta wanda itama complain 'din ta kenan cewa taga pic 'din Baby but bata samun sa a waya kuma.

Ammi baki ta kama tace" Ikon Allah! Wallahi Mu'een Ja'iri ne, wannan wani irin abu ne haka? Muma nan kinga abinda muke kai kenan duk layukan sa basa tafiya..."

" Allah dai yasa lafiya".
Cewar Anty Zainab, yayin da Ammi ta 'kara da fa'din" Ni lafiyan yarinya ta ma nake son ji duk hankali na ya kasa kwanciya..."
Tana cikin fa'din hakan sai ga Zaidu ya shigo cikin 'daurewar fuska, gefen Ammi ya isa ya zauna yana fa'din" Me ke faruwa ne wai yau a gidan..? ina bacci na fa Saif yaje ya tada ni har da buga min mari a hannu na... sai kace nace ya dame ni...mtheew".
Ya 'karashe da jan tsaki.

Ammi ce ta bashi amsa da fa'din" Photon Baby yayan ku ya turo shine muke zaton ko matar sa ce ta haihu".
Duk mugun halin Zaidu a lokacin washe baki yayi shima take ya nemi ba'kin cikin sa ya rasa.
Da fara'ar sa yace" Haba dai Ammi dagaske?"
" Gashi muma haka muka gani, kuma kowa na ta 'kiran sa baya tafiya, yanzu ma muka gama waya da Antyn ku".

Kar6an wayar yayi yana dubawa hadda zooming pic 'din yana murmushi yace" Ammi wannan kam da gani jinin gidan mu ne, baki ga kamar da suke yi da Yaya ba?"

Ammi sai tace" Ni ina zan gane wani kama anan abu cikin waya".
Zaidu kam ko 'dagowa bai yi ba still yana kallon Babyn yace" Kai Masha Allah...wannan Allah yasa tayi kyan Yayah wallahi....".

Saif ne yayi saurin taran sa da fa'din" Ka jishi kamar ance da shi macece har yana wani lissafi".
Ya 'karashe yana 'dan hararan sa.

Zaid kuwa cewa yayi" Sai kayi ai 'dan 'kauye kai baka ganin yanayin dressing 'din ne, the Baby with pink mostly are baby girl while blue kuma for boys, mutane 'kalilan ke caku'da colours 'din"

Saif saurin kar6a yayi yana sake dubawa yake fa'din" Haba dai ai ni ban ma sani ba".

Ammi kam da idanu kawai take bin su tana murmushi da shirmen nasu...cikin ranta tace" Zaid sarkin tsari".

Zaidu ne ya tashi shima yaje ya 'dauko wayar sa, ai kuwa yana dubawa yaga an tura masa shima.

Nan take ya danna pic 'din a status da kalamai masu da'di a 'kasan na nuna tsananin 'kauna farin ciki....Ni kaina sai da Zaidu ya bani mamaki.

Wayar Yah Deen bata tashi shiga ba har sai kusan la'asar, Kafin lokacin kuwa Ammi tuni ta fara shirin ta na tafiya duk dama bata ji daga bakin sa ba har a lokacin bata tabbatar ba amma dai hakan bai sa ta fasa shirin tafiyar ba.

Haka ta yini neman layin sa amma baya tafiya, da la'asar bayan ya fito daga Sallah sannan ya bu'de wayar sa yana murmushin mugunta dan yasan duk ya 'daga musu hankali zuwa lokacin.

Ishaq ne mutun na farko da 'kiran sa ya fara shigowa da yake shima akai-akai yake fama gwada layin nasa.

Ai kuwa sai da yayi masa masifan kashe wayar kafin nan yayi masa sam barka da samun 'karuwar da yayi, yana cikin magana da Ishaq 'kiran Ammi ya shigo ganin hakan yasa ya sanar da Ishaq sannan ya 'kira Ammin bayan sun yi sallama da shi.

Ammi na 'dagawa ta 'kundumawa Uban sa zagi da yaren su, sannan ta 'kara da fa'din" Ina wasa da kai ko Mu'een?"

Dariya yayi mata yace" Sorry Ammi kaina 'kasa...".
Tace
" Where is my daughter?"
Yace" Ammi yarinyar ki ta haihu lafiya ta sami Baby girl".
Ammi sai tace" Shine kuma ka kasa sanar dani ko Mu'een, 'karshe ma kashe wayar ka kayi...ai kasan dole hankali na zai tashi..kuma hadda na ta duk baya tafiya".
Cikin ladabi yace
" Afuwan Ammi wallahi abubuwa ne suka yi min yawa shiyasa na kashe wayar saboda in samu natsuwa".

Ammi bata bi ta kan maganar tasa sai tace" Bani ita to inji ya jikin nata?"

" Ammi ai bana gida yanzu amma idan na koma zan 'kira ki".
Sai tace
" Ita da waye ka barta?..ka san fa..."
Tun ma kafin ta kai aya yayi saurin taranta da fa'din" Karki damu Ammi, Mummyn Safwan na tare da su".
Hankalin Ammi kwantawa yayi take ta 'dan ji sanyi cikin ranta,
" Ok shikenan idan ka koma karka manta ka 'kira ni".
Abinda kawai tace da shi kenan kuma shine 'karshen maganar su, daga haka suka yanke 'kiran yana mai bata tabbacin cewa da ya isa gida zai ha'da su.

Ammi bata ajiye wayar ba sai da ta 'kira Anty Zainab ta gaya mata cewar sunyi waya da shi yanzu tace Baby girl ta samu...kuma duk suna lafiya.

Murnar Anty Zee ninkuwa yayi akan na baya saboda yanzu ne ta tabbatar Babyn ko na waye, Mu'een 'din ta ne yau yake matsayin uba, Allah sarki rayuwa.. ubangiji Allah ya raya mana Baby.
Chapter 151 · 0% Book details