Sashe 111
Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ishaq Babbar rigar jikin sa ya cire ya ajiye agefen sa sannan yace" Ai ka bari kawai mutanen nan 'kananun 'yan gabas ne wallahi...sai da fa muka gama shiri mun baza kunnuwa zamu ji an 'daura auren ka kawai sai ji akayi ya wakilci auren Husnah da wani daban, ashe ma wai wancen Hisham 'din 'dan sa ne na cikin sa, in ba rainin hankali ba yau ne yasan da zaman 'dan nasa da bai yi tunanin aura masa ita tun farko ba sai da ya bada ta ga wani ?...abin takaici ma wai sai daga baya bacin har an gama komai kafin ya zo yana bawa su Alhaji ha'kuri...a lokacin ji nayi tamkar in mare sa..."
Anas ne ya tare maganar tashi da fa'din.." Ai Alhaji ba 'karamin birge ni yayi ba, kai baka ga yanda ya nuna masa bai damu ba, sai ma wata kwantacciyar fara'a da fuskar sa ke haskawa...jikin Mutanen ai har sai da yayi sanyi 'yan rainin sense..".
Baki Yah Deen ya ta6e, cikin nuna halin ko in kula da batun ya furta" can musu su suka sani...ni dai Alhamdulillah kawai zance tunda an raba ni da ita".
Babu wanda ya ko kwatanta sanar da shi cewa an sake 'daura masa auren da wata kawai suka bar shi da murnar sa na bai auri Husnah ba.
*****
'Bangaren Husnah kam tunda taji cewa da Hisham aka 'daura auren ta bada Mu'een ba sai ta ringa kuka gwanin tausayi idan ka ganta, hawayen ta sam ya kasa tsayuwa, sai dai ita kanta bata san ainahin me take yiwa kukan ba, shin kukan an raba ta da Deeni ne ko kuwa kukan auren da akayi mata da Hisham?
A yanzu baza ta ce akwai soyayyar Mu'een cikin zuciyar ta ba balle tace taji haushin rabuwa da shi, sannan ta san Hisahm 'dan uwanta kuma mai 'kaunar ta amma me yasa ta kasa jin farin ciki da jin labarin aure tsakanin su? Ta riga ta shiryawa zama da Mu'een tuntuni, ta yiwa kanta al'kawarin zama da shi cikin ko wani irin hali.
Mahaifiyar ta kam jikin ta sanyi yayi da jin wani juyin da aka kuma yi, sam ta rasa me yake damun Alhaji Mamman a dauniyar nan, tsananin son kansa ya fiye masa yawa, wancan karon da ya bada auren Husnah batare da neman yardar ta ba ta yi masa uzuri da tunanin ko abokan sa ne iyayen yaron shiyasa amma duk da haka hankalin ta bai kwanta ba, wanda bata samu natsuwa ba sam har sai da ta tabbatar da cewa Husnah na son yaron sannan hankalin ta ya kwanta da auren, yanzu kuma bacin sun gama kwantar da hankalin su kan hakan sun kar6i auren sai ya kuma 6ullowa da wata sabuwar zance...wai auren Hisham da Husnah...she is totally speechless kan hakan
Husnah kam kukan ta na 'kara yawaita ne a duk lokacin da ta tuno da mahaifin ta, tasan da ace yana raye da duk hakan ba zai faru da ita ba, ta san da babu wanda ya isa ya ringa juya mata rayuwa batare da yardar ta ba, balle irin wannan juyi irin na rashin mutunci da 'kas'kanci 'karara hatta mahaifiyar ta ba'a bawa darajar da za'a shawara da ita ba, tasan ba kowa ne zai iya 'daukan hakan ba duk kuwa rashin gatan mutum.
Yini ta yi tana kuka, yayin da kanta ke tsananin yi mata ciwo amma sam bata damu ba, kafin maghrib kuwa ko motsin kirki bata iya yi da jikin ta saboda yanda kanta ke sarawa, idanun ta ma nawi sosai suka yi mata.
Lokacin da Mummyn ta fahimci halin da Husnah take ciki kuka ta sanya kawai itama, gani take kamar bata kula da maraicin Husnah ba, a 'yan kwanakin nan Husnah tayi kukan da be kamata ace tayi sa ba duba da yanayin shekarun ta, gani take kamar Allah zai tambaye ta akan hakan, haka ta zauna gefen Husnahn tana faman sheshshe'ka itama, wata 'yar uwar tace dake tsaye dafe da kafa'dar ta take bata baki akan taya Husnah kukan bashi da amfani sam, bata ce da ita komai ba illah ro'kon ta da tayi akan ta 'dauko mata wayar ta.
Family Doctor 'din su ta 'kira inda ta sanar da ita abinda ke faruwa da Husnah cikin rawar murya.
Husnah kam hawaye ta gefe da gefen idanun ta yake sau'ka, ko iya bu'de idanun da kyau ma bata yi yanzu, tana kyautata zaton Allah ne kawai yake jarabtan ta kan abinda ta aikata abaya, shiyasa yake ha'dawa da abubuwan 'daga hankali a duk sa'in da yaga dama batare da ta zata ba, a hankali ta furta" Mummy...mutuwa zanyi ko?"
Saurin kamo hannun ta mahaifiyar ta tayi ta ri'ke cikin nata tana girgiza kanta idanun ta hawaye tace" Bazaki mutu ba Husnah, idan kika tafi ni da wa zan zaki barni a duniyar nan...?"
Husnah rintse idanu tayi tana jin ciwo a 'kirjin ta, ga kunyar mummyn ta da yabi ya cika mata zuciya, tasan babu wanda zai so yaji cewa 'dansa ya aikata irin abinda ita ta aikata, amma duk da haka tana ganin dole ne ta sanar da mahaifiyar ta, dole ne ta gaya mata rayuwar da tayi bayan idanunta, 'kila idan mahaifiyar ta yafe mata Allah ma zai ji 'kanta ya yafe mata, gani take duk abin nan dake faruwa da ita alhakin mahaifiyar ta ne yake binta...she have to end it here kar abin ya zarce haka, da jimawa farin ciki yayi mata 'kaura, rayuwar ta shiga garari ne tun lokacin da batun auren ta da Mu'een ya fara, yanzu kuma ga yadda abin ya kasance.
Idan tace haka zata cigaba bata san agaba me kuma zai sake faruwa da ita ba...idanun ta a rintsen wani hawayen ya sake gangaro mata mai matu'kar 'dumi....a hankali cikin sanyin murya ta furta" Mummy ki yafe min...na ci amanar ki..naci amanar tarbiyar da kika da'de kina bani mummy..."
Kuka take yi mai tsuma zuciya mai ha'de da shashshe'ka..bata iya bu'de idanu ta ha'da ido da Mummyn nata ba a lokacin.
Yayin da Mummyn ta tsura mata idanu tana kallon fuskar ta zuciyar ta duk ta karaya, bata son tana kukan nan, tana so ta dakatar da ita haka nan amma sam ta kasa sai ma taji ta karaya gaba 'daya musamman da taji irin kalaman nata da mamakin ta tsaya kallon ta.
Husnah kam tana cikin kukan tayi tunanin rashin sanar da Mummyn yafi saboda gudun halin da itama zata shiga sanadin hakan, take sai tayi ma'am da wannan batun dan haka ko da ta bu'di baki dan cigaba da ro'kon Mummyn sai tace
" Mummy...dan Allah ki yafe min insha Allahu bazan sake 'daga hankali na ba...nayi al'kawarin zan zauna da Yah Hisham da amana....nasan 'kaddara ce ta ha'da aure na da shi auren mu ha'din Allah ne..dan haka na amince Mummy.."
Ta 'karashe da sheshshe'ka, sam ba haka ta so fa'di ba amma nawin maganar yasa ta kasa furtawa mummyn ta, ta ya za'ayi ta dubi tsabar idanun Mummy tace da ita ta aikata zina sau ba adadi a rayuwar ta, sannan daga 'karshe wanda ta yadda da shi ta mallaka masa jikin tan shine kuma yazo ya nuna mata tsana mafi muni a rayuwar ta?...Tasan jin hakan ba komai zai haifar ba face 'dagawa mahaifiyar ta hankali fiye da tunanin ta..."
Mummy kam bata iya tace mata komai ba ganin kukan da take yi, hannun ta kawai ta sake ri'kewa ga gam tana jin so da 'kaunar 'yar ta na sake ratsa ta, dama tasan Husnah me biyayya ce bazata ta6a cewa bata so ba...da yake bata wani fahimci maganar da Husnahn ta 'dauko da farko ba dan haka bata yi ko tunani akai ba.
Bata da damuwa ta 6angaren Hisham dan tasan bashi da matsala shi, kuma dama asalima yana matu'kar 'kaunar Husnah tasan ko yanzun ma ba zai 'ki auren ta ba.
Tana cikin tunanin nan likita ta iso inda take bayan gaisuwa sai kawai tafara aikin da ya kawo ta.
Ba'a 'dauki dogon lokaci ba Husnah ta samu bacci sannan likitar ta tafi bayan ta basu shawarwarin da suka dace wanda hakan yasa suka fita suka bar ta dan ta huta illah mummyn ta suka bari dake zaune gaban ta ta zuba uban tagumi tana kallon ta tana kuma juya maganganun da ta gama furtawa, tausayin Husnah take ji sosai, da kuma tausayin maraicin ta, ba 'karamin da'di taji ba da taji cewa Husnah ta kar6i 'kaddarar ta hannu bibbiyu, ta amince da auren Hisham, ita kanta Mummy zata fison hakan saboda Hisham nagartacce ne, abu 'daya ya rage mata a yanzu shine..kare daraja da martabar 'yar ta, dole ne ta tashi tsaye ta sake shiri tunda Allah ya riga ya ha'da auren.
Can gidan Alhaji Mamman kuwa zaune yake kan kujera shi da amaryar sa bayan sallar maghrib...dawowar sa kenan daga masjid sai ya tarar da ita zaune tana jiran dawowar sa, hirar su suke yi cike da raha tana 'kara ziga shi akan auren da tasa ya ha'da shi batare da shiri ba wanda har alokacin labarin auren bai isa kunnen shi wanda akayiwa auren ba.
Hajiya Kareema ma tunda taji batun auren hankalin ta ya tashi sosai, tayi mamakin dalilin faruwar hakan, tunda la'asar ta baro gidan bikin ta dawo gida batayi zancen da kowa duk da kuwa abin ya dame ta sosai, musamman da taga yanda Husnah ke faman rusa kuka duk saboda jin cewa da Hisham aka 'daura mata aure, duk itama sai ta ji ta kasa natsuwa sai dai bata tattauna zancen da kowa ba, burin ta kawai Alhaji Mamman ne, so take taji daga gare shi menene dalilin wannan sauyin bazata da yayin.