← Book details Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 153 OF 211

Sashe 153

Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dukkan su dariya suka sanya cike da jin da'din yanda abokin su ya fara canzawa har ana jin abinda ke cikin ransa game da wani.

Kafin tafiyar su kuwa Ishaq kamar da wasa yake yiwa Yah Deen maganar" Wai tunda yanzu an girma kamata yayi arage wasu abubuwan ko dan saboda 'yan baya ma".

Ko be tambaya shi da kansa ya fahimci me Ishaq ke nufi da fa'din hakan, kuma shi da kansa ma dama burin sa kenan, dan haka sai ya bawa Ishaq tabbaci da fa'din" Insha Allah komai ya wuce aboki na".

Comment
Vote
Share

*Salmerh ce*😍

💕 *NOORUL* 💕
      (Haske nah)

By
*Salmerh MD*

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

_*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

🅿 *72*

Watan mu uku a gida kafin muka koma Bauchi, nan Yah Deen ya 'dora daga inda ya tsaya, soyayyar sa ga 'yar sa sai abinda yayi gaba, lokuta da dama ni sai dai in zame musu 'yar kallo dan matu'kar yana gida to kuwa Jasmine bata zama da ni har sai dai in shayar da ita zanyi.

Sha'kuwar sa da ita sosai ya ninka nawa, yarinya ce 'karama amma har zakiyi mamakin irin wayon da take da shi, ba 'karamin farin sani ta yiwa mahaifin ta ba, tun kafin ta cika shekara guda ya fara fita da ita unguwa da yake ma tayi tafiya tun tana 9months ne.

In kinga shirgin kayan wasan da ya tarawa Baby abin har zai baki dariya m, dan kuwa wasun sam bata da wayon da zata gane amfanin su a lokacin sai daia kawai ta lalata su, shi kam duk ya ha'da ya tara mata.

Ni dai bazan iya ce ga takamammen matsayi na a wurin sa ba cuz tunda ya samu Jasmine shikenan na kasa gane masa kuma, hankalin sa da tunanin sa gami da kulawar sa duk gareta ya mayar.

Akan Jamsine har masifa yake yi min wani lokacin, wanda da kansa kuma daga baya zaki ga ya dawo ya ban ha'kuri da yake yasan be kyauta ba, sai yace dani kawai ransa ne ya 6aci a lokacin shiyasa har yamin masifan amma nima indai na yawan saka ta kuka.
       Domin yakan yawaita yi min fa'dan ne musamman idan ya ji tana kuka.

Ni kam bana ta6a tanka shi kan hakan saboda ban ma san me zance da shi ba kwata-kwata da zai iya yadda dani indai akan Jasmine, domin yarinyar akwai shegen son kuka, ko abu be kai na kuka bane ita kam sai tayi, shi kuma kar yaji hakan take zaki ga ya 'dorawa mutun laifi, kuma fa da kansa ma yasan halin kayan sa amma baya ta6a ganin laifin ta ko me kuwa zata aikata.

Yah Deen sam baya 'kaunar yaji muryar 'yar sa da sunan kuka, ko wanka zan mata idan bana so tayi kuka sai dai muyi ta wasa a haka har wankan ya kammala kuma zaki ga sai mun 6ata lokaci sosai, randa kuma naga bani da wannan lokacin to wankan kawai nake yi mata ranar kuwa kuka zata tayi kamar wacce aka doka.

Idan yaji hakan sai kiga ya fara yi min masifa wai bana binta a hankali ne shiyasa har take kuka, take zaki ga ya kar6i abinsa ya shirya ta sai dai inji muryar su suna dariya.

Sallah ce ka'dai yake 'daga min 'kafa idan ya tarar ina yi while Baby na kuka, baya ga haka kam ko ni kaina bazan iya gaya miki so nawa nasha masifa akan 'yar da na haifa da ciki na ba.

A kullum kuma sai dai bata ga na sa hijab ina sallah ba kuka zakiga tana yi tana jan hijabin nawa har na idar ko kuma kiga ta shige gaba na ta rungumo 'kafafu na ita adole sai dai in 'daga ta, da 'kyar da dabara nake samu in idar da sallar tawa, tana idar kuma sai in 'dauke ta in rungumi ajiki na wani sa'in rikita ni ma take yi in kasa yin azkar 'di na, idan ta ban haushi kuwa share ta nake yi dan ban laifi Baby akwai rigima gaskiya sau da dama ma.zaki ga ko na idar da sallan na 'dauke ta bata daina kukan, gata bata jin lallami sai dai in Yah Deen na kusa, idan ta ban haushi sai in share ta in cigba da yin abinda ke gaba na.
Shikuwa kar yaga hakan ttake zakiga ya nuna miki 6acin ransa a fili.

Abin sosai ya ke min suya a zuci amma bani da yadda zanyi tunda ni na haifi kaya na.

Sau da dama wankan ma idan ta fitine ni 'kyale ta nake yi da ruwan tayi ta wasan ta domin ita Allah ya zuba mata masifan son wasan ruwa kamar kifi, tafi so idan na sata a ruwa kar a cire ta kuma kar ace za'a goga mata abu ajiki nan ne bazaku shirya ba...idan na 'kyale tan baya damuwa sai kiga ya zo ya 'karasa yi mata wankan yana jan ta da wasa har ya shirya ta...wani lokaci har ficewa suke yi daga gidan ma ni ban sani ba.
Gashi dama ba wani damuwa tayi da shan mama ba sai su yini a waje bata damu ba.

Abu 'daya da har yau bai canza min ba shine suna" _Nuree_ " da yake 'kira na da shi ko da wasa bai ta6a canzawa ba.

Yah Deen da ya zauna da ni a gida yayi hira ya 'kwammaci ya 'dauki 'yar sa su fita harabar gida ko kuma su wuce yawon su cikin gari.

Babban amfani na yana zuwa masa ne idan bu'katar sa ta taso, wannan kam baya min iyayi akai zaki ga ya kwantar da kansa domin cimma burin sa.

Ni kuwa duk ranar da ya 6atan rai 'kin amince masa nake yi dan a gani na wannan ne ka'dai hanyar da zanbi in rama abinda yake yi min.

Sosai kuwa ransa ke 6aci amma baya takura ni kamar yadda baya sake kula ni kan maganar balle ya ro'ke ni sai dai kawai kiga ya juya min baya yayi baccin sa.

Irin hakan ya sha faruwa tsakani na da shi dan bazan iya lissafa adadin ranakun ba.

        Ban ta6a yin tunanin  ko wannan dalilin ne ya sanya baya shayin yi min masifa a duk lokacin da ya ga dama ba musamman ma idan abin ya ha'da da 'yar sa, dan da ba haka yake min ba.

Tun a lokacin na so fara karatu, a lokacin Watannin Baby Goma Sha biyar amma ya hana ni wai sai ta 'kara girma...idan na fara fita yanzu wa ye zai dinga kula masa da Baby, dole na na ha'kura na cigaba da zama a gida badan raina ya so ba.

Bazan manta ba akwai watarana lokacin kaina ciwo sosai yake min da 'kyar nake iya 'daga kaina, mura ce ke damuna kuma abin kamar na neman baki kan nawa bai fara ciwon ba sai da ya fita, ni kuma ban 'kira na gaya masa ba saboda a gani na da nasha paracetamol shikenan, ko da na sha 'din ma kuwa sai bai daina ba, ko idanu na bana iya bu'dewa da kyau saboda tsananin ciwon kan, a hakan Baby tazo tana ta yimin rigima wai sai na goya ta.

Janyo ta nayi jiki na na rungume ta ina llalshi amma a banza na bata mama ta'ki ansa sai kuka, bakin ta har ja ya yi saboda yanda da dami kanta da kuka, dole na daure na bu'di baki na nace" Ki bari idan Daddy ya dawo ya goya ki ko Mama na?"
Take ta 'daga kafa'da ita wai a a ta cigaba da kukan ta.

Allah ya sani ni abinda zan iya yi mata kenan a lokacin amma duk ta 'ki...duk nima sai ta 'kara hautsina min hankali na, na ratsa me ma ya kamata inyi.

Hawaye kawai naji yana gangaro min saman kunci na, duk yadda nayi da Baby 'kin amincewa tayi ta cigaba da rigimar ta, sau'ke ta nayi daga jiki na ina sake share hawayen da ya gangaro min.
Kinsan rigimar yara yanda take da cin rai sosai.

Jamsine kuwa sai ta sake dawowa jiki na tana 'kara sakin wani kukan, kaina naji tamkar zai rabe gida biyu bansan lokacin da na matsar da ita ba azuciye ina fa'din" wallahi mari zan miki idan kika 'kara damuna..."
ban.kai ga rufe baki ba sai na hango shi kamar an daga sama ya shigo...wallahi sai da zuciya ta ta tsinke take ciwon kan nawa ya 'karu...saboda sanin hali, ga shi da turewan da na mata da tsawan duk akan idanun sa suka faru.

Take nayi 'kasa da idanu na ina goge hawayen fuska ta.

'Bangaren Yah Deen kuwa sosai 6acin rai ya bayyana kan fuskar sa, a hankali ya 'karaso kusa da ita ya rungume abin sa batare da ya furta komai agare ni ba.

Sai da ya tabbatar ta yi shiru tana sau'ke ajiyan zuciya sannan ya 'dago jajayen idanun sa ya dube ni, koka'dan ba bu ko alamun fara'a tattare da fuskar sa...ban damu ba cuz dama nasan yau kam dole sai yamin masifa.

Bai yi min magana ba sai ya kai hannu bayan rigar Baby yana bu'de zip 'din bayan rigar ta ta yace" Har abada Nuree bazaki canza ba, wallahi da ace ba ke kika haifi yarinyar nan da ban san kuma me ze faru bayan wanda na sani ba...amma ki sani ko da wasa bazan lamunci irin hakan ba".

Da muryar kuka nace da shi" Damuna fa tayi da kuka kuma ni kaina ciwo yake yi sosai".
A fusace yace
" Shine dan baki da tunani zaki doke ta?
Yarinyar nan fisabilillahi me ta sani da har zaki yi mata irin wannan hukuncin? Kuma ma lokacin da zan fita kin sanar da ni cewa baki jin dad'i ne da har zaki zo kina dukan min yarinya akai, ke kullum baki iya kiyi abu irin na masu tunani ba sai yaushe zaki girma to?"

Kuka na na cigaba da yi har ya 'kara shi masifar sa yayi shiru 'karshe 'daukan abinsa yayi suka yi ciki.
Chapter 153 · 0% Book details