← Book details Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 211

Sashe 62

Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jikin ta ta janyo ni ta zauna gefen gado.." wai har yanzu kuka kike yi ne?"
Girgiza mata kai nayi sai tace " to ba na hana ki zama jikin su Saif ba...ba kya ji ko?"
" Ki yi ha'kuri Ammi".
Na fa'di da sanyin murya ta.
Sai tace " in kina son in ha'kura kar ki sake zama jikin su kinji, ke bakya ganin ke macece nd 'ya mace is a jewel kama kanta take yi bata ha'da jiki da maza kinji?"
Sai na 'daga kaina sama.
" Yauwa Hudah ta promise me bazaki sake ba".
Tayi maganar tana mi'ko min hannun ta...nima sai na 'daga nawa na sanya cikin nata.
" Good girl"!
Ta fa'di tana murmushi...nima sai na 'dan murmusa daga haka sai ta sa muka 'dauro alwala muka gabatar da isha'i.

Alhaji na dawowa daga raka likitan ya umarce su Saif ma da su wuce suyi sallah dan isha'i ta wuce tuntuni.

*Salmerh ce* 😍

💕 *NOORUL* 💕
      (Haske nah)

By
*Salmerh MD*

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

~This page is 4u *Nanerh, Nanah* and *Nusaibaty* 😍...ina yinku mutane na....Ubangiji Allah~ ~yai ta faranta muku har 'karshen rayuwar ku~ *AMEEN* 👏🏻

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

🅿 *32*

Lokacin da na tashi a bacci har gari yayi haske sosai dan haka sai da na yi sallah kafin na tafi kitchen neman Ammi, gaishe ta nayi ta amsa tana mai cigaba da ayyaukan ta, nima sai na matso na fara taya ta....fuskar ta cike da annuri tace da ni " baki tambayi jikin yayan ki ba"
Sai ma a lokocin ni kam na tuna da shi, cuz harga Allah kwata-kwata na manta da shi ma balle abinda ya faru,  maganar Ammi ce ta sani tunawa da wanzuwar sa, banyi 'karya wa Ammi ba nace mata " ai mantawa nayi ne Ammi".

  Shiru tayi min bata amsa ba illah murmushi....sai da tafara aikin kafin tace " har kin manta da shi bacin jiya har cikin bacci ajiyan zuciyan kuka kike yi kuma saboda shi?"
Bance komai ba dan bansan mai zance da ita ba tunda bansan da wannan batun ba ni, ganin da sakin fuska tayi maganar ya sanya ni nima murmusawa kawai na maida hankali na ga aikin da Ammi ta bani.

Ashe Ammi na jin da'din warwarewar 'dan ta ne, domin tun kafin sallahr Asubah ya tashi, ba laifi garau ya tashi sai 'dan abinda ba'a rasa ba na daga ciwon kai da kuma 'kirjin sa dake 'dan yi masa nauyi ka'dan, sanin da yayi cewa bai yi sallahr isha'i bane ya sanya bai ko bi ta kan ciwukan da yake ji ba ya tashi ya 'dauro alwala ya fara gabatar da sallar isha'in wanda yana tada sallar Alhaji Baba ya bayyana bakin 'kofar 'dakin nasa...ganin.yana tsaye yana sallah cikin narsuwa ne ya sanya Alhaji Baba sakin hamdala da bai san lokacin da ta fito fili ba ma..... wannan shine karo na biyar kenan da yazo duba shi daga dare da wannan lokacin.

Bai iya ya tafi ba dan farin cikin ganin yanda ya tashi da kansa batare da taimakon kowa ba, hakan ka'dai ya tabbatar ma da Alhaji Baba  cewa jikin nasa da sau'ki babau laifi, abinda yake gudu cikin zuciyar tasa bai faru ba...dama tsoron tashin ciwon sa yake yi amma tunda Allah ya ta'kaita ai hikenan.

Yana tsaye a wurin har Yah Deen ya idar da sallah yana sallamewa kuwa ya waigo ya kalle shi...dan tun 'dazun ya san da tsayuwar sa a wurin sanadin hamdalar da ya furta a fili.

   " Ya jikin naka?"
Alhaji Baba ya tambaya yana mai tahowa kusa da shi.
Sai da ya saki ajiyan zuciya ya shafa fuskar sa da hannun sa 'daya kafin ya amsa da fa'din " Alhamdulillah....banjin komai yanzu".

" masha Allah haka ake so ai...Allah ya 'kara afuwa..ubangiji ya sa daga hakan shikenan".
" Amin" yace a 'kasan ma'koshi.

Alhaji Baba juyawa yayi ya fara tafiya jin 'kiran sallah na tashi daga masallaci...yana tafiyar yace " bari inyi shirin masallaci ko".

Yah Deen bai amsa shi ba har ya bar 'dakin...cigaba yayi da zama a wurin yana addu'ah tare da istigafari da salatin annabin tsira {SAW} har sai da yaji motsin su suna shirin fita kafin shima ya yun'kura ya tashi ya tare su inda suka ha'du cikin babban parlour n da ya hada duka 6nagarorin gidan.

" Zaka iya zuwa  ne?"
Alhaji Baba ya tamabaye shi yana duban sa da kulawa.
Yah Deen sai ya gya'da kansa alamar " erh"....." jiri fa baka ji?"
Alhaji Baba ya sake tambayar sa, cikin dakiya ya amsa da fa'din " ban jin komai Alhaji".

Daga haka yayi gaba dan baya son wata tambayar kuma, suma sai suka rufa masa baya inda suka 'karasa fita gaba 'daya.

Koda ya dawo daga masallacin ma kwanciya ya 'kara yi yana tunani  ahaka Ammi tazo ta same shi, sai dai bata wani jima wurin sa ba ta fita ganin kamar bacci yake son yi, bai fito fili ya fa'da ba amma cikin.muryar sa ta fahimci yanayin da yake ciki.
   Fitan ta keda wuya kuwa wani baccin ya sake  'daukan shi...har kuma muka tafi makaranta bai tashi ba wanda hakan ya sanya ban ha'du da shi ba wannan da safiyar.

Da fitan mu likita ya dawo ya duba shi da yake zai wuce wurin aikin sa ne so bai wani jima ba ya wuce ganin jikin yayi normal dan haka sai ya bayar da wasu magunguna kawai yace idan ya tashi ya sha su na sati guda ne maganin, amma kala uku ne, yana bawa Alhaji Baba sai yayi tafiyar sa da fatan Allah ya bashi lafiya.

Ko bayan fitar likitan ma 'karfi da yaji ya tilastawa kansa sake yin bacci saboda baya son ya dinga yawan tunanin abinda bashi da ikon canza shi...
    'Karfe 10am ya tashi a baccin, kansa sosai yayi masa nauyi haka ma yake jin kirjin sa har sai da ya zauna bakin gado ya dafe kan, gudun kar jiri ya kwashe shi, idanun sa sun firfirto, ya ko'de yayi fayau da shi.

Ko yanzun ma da yake dafe da kan nasa tunani yake yi, wani lokaci sai yaji tamkar 'karya ne Aminan sa nan da ranta bata rasu ba, but idan ya tuna cewa mutuwa ta Allah ce, ka kan rasa ranka a duk lokacin da Allah ya ga damar rabaka da ita sai yaji cewa babu mamaki da gaske ne Nanne ta rasu, tunda yasan mahaifan sa baza su ta6a yi masa 'karya da mutuwar ta ba.

Ammi ce ta shigo ta same shi a haka, bai 'dago ya kalle ta ba duk cewa ya ji muryar ta ya kuma san itace ta shigo, amma shi sam yanzu a halin nan da yake ciki bai son hayaniya sam....bai son ma kowa ya ringa kusantar sa ka'daici yake bu'kata sosai...in da hali ma kar kowa yazo inda yake da hakan yafi masa...sai dai ya san samun hakan abu ne mai wahalar gaske tunda ya san irin son da iyayen nasa ke masa, bazasu iya 'daukan lokaci batare da sunji halin da ya ke ciki ba.
Ko da Asuba ma da yaji Alhaji Baba ya zo duba shi, ba 'karamin tausayin sa ne ya kamashi ba, dan ya san babu mamaki ko baccin kirki bai samu yi cikin daren ba saboda shi.

Kusa da shi Ammi ta isa ta zauna gami da ta6a hannun san da ya dafe kansa da shi, yana jin haka sai ya 'dage hannayen san gami da 'dago idanun sa ya kalle ta.

" Barka da safiya Ammi?"
Yace cikin raunanniyar muryar sa.

Ammi bata amsa shi ba sai tace " Muhammad ba zaka daina damun kanka game da wannan abin ba ko..look at your self mana...zaka ja da yin Allah ne?"

Ido ya lumshe cike da damuwa ya kuma bu'de su nan take ya sau'ke su kan fuskar Ammi sannan cikin sanyi yace
" Ya zanyi Ammi?
ke ma kin san dole ne in damu sosai..."
Take sai hawaye suka cika cikin idanun sa....Bai damu ba ya cigaba da fa'din " Burina itace Ammi, komai na, farin cikina da damuwa na duk itace Ammi...na sa ta a raina sosai, me yasa tun lokacin rasuwar ta baku gaya min ba Ammi?, Wallahi da ko ma miye agaba na zan bari inzo ayi jana'izar ta dani inyi mata addu'a da kaina Ammi..."
Sai hawayen sa suka 'karasa gangarowa.

Take yayi 'kasa da kansa yana mai dafewa da hannun sa 'daya.

Ammi kam jikin ta sanyi yayi sosai ita kam mamaki yake bata, ada bata 'dauki abin da zafi ba sai yanzu da ta ga yana 'ko'karin illata zuciyar sa sannan ta tabbatar da abin nasa da gaske ne, tausayin sa sai ya cika mata zuciya....saurin kawar da tunanin tayi, ta sa hannu ta 'dago kansa tana share mai hawayen  cikin kwantar da murya tace da shi "...kayi ha'kuri Muhammad, Alhaji ne yace bazai iya sanar da kai ba kuma kaga ni lokacin ma banda labari sai daga baya yake sanar da ni...kuma inajin duk abinda Alhaji ya aika ta akan hakan ai yayi ne saboda kai, saboda farin cikin ka, i'm sure badan ya 6ata maka bane ya sa bai sanar da kai ba, shi kansa abin ya dame shi sosai ina da tabbacin da zai iya dakatar da mutuwa daga 'daukan ran Amina da zai yi alokacin koda kuwa cewa zai fansar da nasa ran ne saboda kawai kai kayi farin ciki, amma kasan hakan ba mai yiyuwa bane, Amina kam ta riga mu gidan gaskiya kuma ko yanzun ma zaka iya yi mata addu'ah ba laifi bane, shima tafi bu'kata daga gareka a halin yanzu".

Bai ce da Ammi komai ba kawai ya kwantar da kansa akafa'dar ta ya lumshe idanu a hankali yace...." Allah ya ji'kan ta yayi mata Rahma, Allah ya sanya ta cikin Aljannar sa may daukakiya, Allah ya....sai kuma yayi shiru.
Murmushi Ammi tayi tace " ....Allah yasa ku ha'du a Aljannah ko?"
Murmushin shima yayi take sai ya mi'ke ya wuce bathroom.
Chapter 62 · 0% Book details