← Book details Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 117 OF 211

Sashe 117

Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Take sai taji wani iri fargaba mai tsanani ya shige ta, sarai tasan halin Mu'een bashi da da'di ta kuma san salon muguntar sa shiyasa take matu'kar tsoron ha'duwa da shi balle har su ke6ance, tun bayan auren ta ta yiwa kanta al'kawarin tsare mutuncin ta.

Ai kuwa suna ha'da idanu da shi sai ya bar bakin 'kofar a hankali ya 'karaso ciki tare da maida 'kofar ya rufe fuskar sa 'dauke da murmushi.

Nesa ka'dan da ita ya tsaya tare da cusa hannun sa 'daya cikin aljihun wandon jeans dake jikin sa yana kallon fuskar ta yace" Me yasa ki kai masa 'karya?"

Bata tanka shi ba kawai ta tafi ga mayafin ta ta 'dauka da niyyar sanyawa amma sai taji ya fisge daga hannun ta ya rataya shi saman shouldern sa sannan cike da gadara ya sake fa'din" Tambayar ki nake yi baki bani amsa ba".

Husnah kam hankalin ta sosai ya fara tashi, dan haka tuni jikin ta yayi sanyi...a hankali ta bashi amsa da fa'din" Waya ta bata da ala'ka da kai Mu'een so please respect ur self".

Murmushi ya saki yana mai sake binta da idanu " Hus...nah".
Ya ja sunan ta tare da 'dan matsawa kusa da ita...da sauri ta matsa baya...tana ha'de gira cike da 6acin rai.

" Husnah kin raina ni...yanzu dan zaki zo inda nake shine sai kin nemo wani ya rako ki? cinye ki zanyi ne ko me?...Husnah gaskiya kin 6ata raina...ni ne fa ba wani ba me yasa 'karara zaki nuna min irin wannan 'kyamar?"

Tace" Darajar aure na nake karewa".
" I see...yanzu ina auren to?..tunanin ki zan iya ha'kura dake ne?"

" Ni dai Please kayi ha'kuri badan hali na ba".
Tayi maganar da muryar kuka...ita harga Allah yanzun tsoro yake bata ma, mutun tamkar ba'a ta6a 'diga masa ruwan imani a zuci ba.

Baya ta sake yi ta koma gefe tana mai tsiyayar da hawayen takaici.

Bai damu ba ya cigaba da binta har takai bango wanda ya sanya dole ta tsaya cak da 'dan 'karfi tace" Wai meke damun ka ne Mu'een da aure fa akaina".

" Nasani ai, amma ai kin lura ba ni ne na biki ba kece kika biyo ni gida na so miye laifi na dan na more ki? Wannan abinda ya saki tahowa har muhalli na shi ka'dai zan cire miki and nothing else".

Kuka ta sanya mai zuciya ji take da ace akwai wani abin kusa da ita da babu abinda zai hana ta maka mai aka ko dan ta samu ta tsira da mutuncin ta...amma yanzu da ya kasance babu komai so itama bata da coice than ta ro'ke shi ya bar ta, tasan duk abinda ya fa'di gaskiyar sa ne, itace ta zo koma me yafaru kuma laifin ta za'a gani ba nasa ba...hannun ta 'daga duka biyu ta ha'de su wuri guda idanun ta cike da hawaye ta fara ro'kon sa akan dan Allah yayi ha'kuri ya bar ta ta tafi tayi masa al'kawarin bazata sake zuwa masa gida ba, ya taimake yaji 'kan igiyar auren dake kanta".

Shiru yayi bai ce da ita 'kala ba idan ka gansa a lokacin zaka yi tunanin ko maganar da tayin ta shiga kansa ne, hakan yasa itama bata sake magana ba kawai ta cigaba da rera kukan ta gwanin tausayi.

Tsawon mintina shida suna a haka har ta daina kukan tayi shiru duk ta sake rai cewa ya ha'kura zai barta ta tafi ganin yanda ya tsaya shiru sai dai me tmkar wani 'kanin fir'auna bu'dan bakin sa sai cewa yayi"..saboda kin samu wani banzan shine ni kike shirin guje min ko Husnah?"

Shiru tayi masa bata bashi amsa ba ganin yanda yayi mata katanga...tsoro duk ya bi ya sake cika mata zuciya.

Zai sake magana tayi saurin taran sa da fa'din
" Dan Allah Mu'een kayi ha'kuri kasan fa yanzu ala'kata da kai haramcin ta yafi muni fiye da baya".

" Me kike nufi kenan Husnah?"
Yayi maganar yana me 'ko'karin ha'da jikin sa da nata.

Surin gocewa tayi tana fa'din" Let me go please Mu'een kai wani irin mutun ne dan Allah?".

Murmushi yayi da jin abinda ta fa'di wai shi wani irin mutun ne..
" Husnah so kike kisan ni 'din wani iri ne?...ni mayen ki ne kawai..kuma da kike so in barki ki tafin ya kike so inyi da tarin 'kaunar ki da ke cike a zuciya ta Husnah?"

Da muryar kuka tace tace" 'Karya kake yi wallahi baka 'kauna ta ko ka'dan..."
Inda ta 'karashe maganar hawaye na gangaro mata.

Cikin nuna rashin damuwa da kukan da take yi yace" Ki bari in gwada miki zaki fahimta..."
Tunkan ma ya rufe bakin sa tace" Ban so..ni ka 'kyale ni..Allah yayi min tsari da kai mayaudari, azzalimi wallahi har abada bazan ta6a yafe maka ba...".

" Really?"
Ya fa'di yana zare idanu cuz sosai ransa ya 6aci da zagin da tai masa idanun sa har canza kala suka fara...bata kula shi ba ta cigaba da kukan ta duk da kuwa ta fahimci ransa ya 6aci sosai da ita...Hijabin ta dake hannun sa yayi jifa da shi gefe sannan ya sake tunkarar gaban ta, yatsa ya 'dago ya nuno ta da shi da jajayen idanun sa cike da 6acin rai ya furta" In dai har haka kika ce Husnah nima bazan ta6a fasa abinda nayi niyya ba tunda cewa kika yi har abada bazaki yafe min ba...kuma ki sani daga yau duk lokacin da na bu'kaci ganin ki u must come to me dolen ki, kuma bazan kar6i excuse ba, in bahaka ba kuwa zan baki mamaki..."

A firgice ta 'daga kai ta kalle shi da mamaki idanun ta na tsiyayar da hawaye tace" Mu'een da auren nawa kake fa'din haka?".

A tsawace ya bata amsa da
" To hell with ur auren...ko ma uban wa kike aure i don't bloody care ni dai na gaya miki.."

'Kasa tayi da gwiwar ta tare da sau'kar da murya take ro'kon sa hannayen ta biyu ta 'dago
" Kayi ha'kuri wallahi na yafe maka komai dan Allah kar ka tozarta min aure Mu'een".

" Ki ri'ke yafiyar ki ban so...kuma ki sani duk lokacin da kika yi kuskuren yi min taurin kai wallahi ki tabbatar labarin rayuwar ki na nan Jigawa zai isa ga mahaifan ki da mijin da kike tutiyan auren sa akakin duk cikin sa'o'i 'kalilan kin san zan iya ko?".

Hannu tasa aka ta rusa kuka tamkar ance da ita mahaifiyar ta ta rasu ne a dai-dai lokacin.

Tayi danasanin ha'da ala'ka da Mu'een yafi sau 'dari abaya lokacin da ya nuna mata 'kyama bayan tasowar maganar auren su but na yau 'din tana jin nadamar da take yi tamkar bazata sake yin irirn sa ba har abada....bata san Mu'een bashi da ko 'digon imani cikin zuciyar sa ba sai yau...kuka ta sha son ranta wanda sam shi hakan bai dame shi ba...duk yadda ta so ta hana shi aikata abinda ya yi niyya kasa wa tayi yayin da ya ringa yi mata komai cike da rashin imani da mugunta.

Husnah kam ita da kanta sai taji ta sani kanta ta tsani rayuwar ta, tayi Allah wadai da rayuwar ta gaba 'daya, bata san me zuwa Jigawa ya 'kare ta da shi ba face ba'kin ciki da takaici.

Bazata manta ranar da Hisham ya fara kusantar ta ba kafin tafiyar sa...duk da ba laifi ta 'dan yi amfani da wasu abubuwa na gyaran jiki amma duk da haka bai hana Hisham fahimtar cewa ba cikakkiya ya aura ba...Hisham mutum ne mai nagarta da sanin ya kamata, shiyasa bai wani nuna mata rashin jin da'din sa afili ba, duk wani abinda ya dace da yayi mata a lokacin sai da yayi har tana tunanin ko bai gane bane.

Amma daga baya cikin natsuwa sai yake tambayar ta abinda ya faru da ita da yasa ta rasa pride 'din ta.

Nan take tayi masa musu ta nuna masa ita ba abinda ya ta6a faruwa da ita...sannan in ba shi ba babu wanda ya ta6a kasantar ta, a zahiri ita kanta tasan ba gaskiya ta fa'da masa ba wanda tunanin ta wai kar idan yasan gaskiyar ya tozarta ta shiyasa ta 6oye masa.

Bawan Allah Hisham kam ganin yanda ta dage ne yasa take ya amince da batun ta kuma bai sake tada zancen ba.

Shiyasa tayi al'kawarin kame kanta ta ri'ki mijinta tayi masa biyayya sakamakon rufin asirin da yayi mata.

To yau idan akace labarin ala'kar ta da Mu'een ya isa kunnen sa da wani idanu zata dube shi? Sannan mummyn ta ma wani irin kallo zatayi mata?"

Tana hawaye ta koma gida da kayan ta cikin jaka, hatta 'dan sahun da ya 'dauko yakan waiga ya kallo ta lokaci zuwa lokaci ganin yanda take ta share hawaye.

Ko wanka ba ta tsaya tayi a gidan sa ba sai da ta koma gidan ta kafin tayi shi idan ka ganta duk ta fita hayyacin ta, da 'kyar ta samu hawayen ta tsaya amma haushi da ciwon abinda Mu'een yayi mata bai bar zuciyar ta da wuri ba.

Da dare da Hisham ya 'kira ta ya so ya fahimci yanayin da take ciki daga muryar ta saboda ya ji ta duk tayi sanyi sarai ya fahimci akwai abinda ke daminta, amma sai ta ce da shi ba komai...ita kawai garin ne ya isheta tace makarantar ma ta gaji da shi gida zata koma ita kam.

Lalla6an ta ya ringa yi akan ta daure ta 'karasar tunda watanni 'kalilan ne suka rage musu ai kamar yau ne...bata san me zata ce da shi da zai sa shi aminta da 'kudurin ta ba indai ba kanta zata tonawa asiri ba, hakan yasa dole ta ha'kuran kamar yadda ya bu'kata sai dai tasan rayuwar da zatayi a Jigawa yanzu zai kasance ne mafi muni daga cikin rayuwar ta na duniya, bata jin zata sake yin farin ciki kuma matu'kar ta kasance cikin garin Dutse tare da Mu'een.

Husnah har 'yar rama tayi saboda damuwa...sai dai cikin sa'a Mu'een bai sake tuntu6ar ta da batun ba kusan kwanaki goma sha 'daya da zuwan ta gidan sa, wanda cikin hakan har Hisham ya zo yayi weekend wurin ta ya koma Abuja.
Chapter 117 · 0% Book details