← Book details Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 150 OF 211

Sashe 150

Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ko ita kanta Noor in kamata yayi ace bai karya al'kawarin da 'daukan ma kansa na rabuwa da Kowa ba dalililn ta, alokacin da ta yi masa halacci, amma sai gashi tun ba'aje ko'ina ba ya rusa komai, yayi 'ko'karin koyar da ita zama da shi yavwatsar da komai da na rayuwar sa na baya musamman da yake yanzu yana da iyali ba kamar da ba,  amma sai yaaka rashin sa'a domin da kansa ya fahimci itan she is not ready at all hakan yasa ya 'kyale ta kawai.

Hudah yarinyace mai ha'kuri, kawaici da kuma sanyin hali, amma a 6oye taurin kai ne da ita matsananci, ga kuma nuna halin ko in kula akan komai, sau da dama yana gudun tunkaran ta ma da wasu bu'katun nasa saboda sanin halin ta da yayi yanzu sai ta nuna bata so kuma shi bazai iya tilastata ba musamman ma saboda kashedin da Ammi tayi masa akan 6ata mata rai da suka yi babu wanda ya sani daga shi sai ita Ammin.

Hakan yasa ko cikin gidan sa ba sosai yake sakin jikin sa ba saboda ance yawan zama shike yawan kawo sa6ani har ya kai ga 6acin rai, Ammi kuwa cewa tayi matu'kar hawaye ya sau'ko a idanun Noor sanadin.6acin rai wallahi bata yafe masa ba, shiyasa yake binta da duk yanda yaga take ra'ayi a kullum 'ko'karin sa bai wuce yaga ya faranta mata ba ko da ka'dan ne duk da itan bata bayyana jin da'din ta afili.

A mafi yawancin lokuta idan yayi mata abu godiya ka'dai ke raba su bata ta6a nuna jin da'din ta har shima ya fahimci irin abinda yafi zama mata arai, wannan halayya ta Noor yasan ba kowa ya sanshi ba, sai ma yake ganin kamar shi ka'dai take yiwa hakan cuz da ba haka take ba, yasan ko da ya fa'dawa Ammi ba yadda zatayi da shi ba dalilin kenan da ya sanya shima ya fita harkar ta, duk yadda take ha'da masa zafi amma baya damuwa da duk wani abinda zatayi masa kuma baya ta6a nuna mata cewa abin na damin sa.

Shiyasa ma ko lokacin da yaga Yusrah batare da 6ata lokaci ba ta shiga ransa har ya nemi ha'da ala'ka da ita, da kansa yasan da wuya ne ya iya daina kula wasu matan matu'kar zaman nasu ya mi'ke a haka da ita......

Bai ce da ni 'kala ba nima ban damu ba dayake dama a haka ya saba lallashi na lokuta da dama idan ina kuka.

Ko yanzun ma da na gaji da kuka na da kaina nayi shiru ni dai abu 'daya da na sani kawai shine bani ba wancan gidan har abada al'kawarin da na 'daukar wa kaina kenan tun abaya.

Tun daga ranar kuwa Yah Deen bai sake tada batun zuwa wancan gidan da ni ba har muka koma Bauchi...wanda sai bayan komawar mu ne kafin ya samu damar kasancewa dani sai da kuwa ya tabbatar min da cewa duk rigimar da na tayi masa abaya bashi na 'daukam ma kaina.

Haka na cigaba da rainon ciki na har ya shiga wata tara...Yah Deen ma koka'dan bai rage 'kalilan daga cikin lokacin sa da yake bani ba, zuwa yanzun kuwa da sau'ki ba laifi dan har muna zama muyi hira da shi, wani sa'in ma har ina bacci da kaina bisa 'kafafun sa.

Idan ya dawo aiki kuma da kansa yake mammatsa min 'kafafu na wani sa'in kuma mu fita zagawa batare da mota ba...wai exercise amma da nace na gaji zai ce to ya isa mu kom gida.

*****
      Wata tafiya ce ta taso masa zuwa aiki a wani 'kauye dake 'kar'kashin jahar Bauchi domin, bai so tafiyar ba saboda ganin na shiga watan haihuwa ta amma sai ya kasance dole sai da shi tafiyar.

Ko kafin ya tafi yayi da ni akan in shirya ya kaini gidan Mummyn Safwan amma na 'ki amincewa,  duk yadda ya nuna damuwar sa 'ki nayi nace masa ai bakomai da naji wani abu zan 'kira ta.

Ai kuwa tunda ya tafi hankalin sa bai kwanta ba, wani iri yake jin ransa ya kasa sakewa, a koda yaushe 'kiran sa zaki gani yana shigowa wayata" Yah Deen". Kamar yadda yake arubuce.

Da yaji lafiya ta kuma shikenan, anjima ka'dan zaki sake ganin 'kiran sa, idan da wasu nake tare a gidan har haushi zasu ji a yanda yake damuwa da jin lafiya ta 'din.

Bayan tafiyar sa da kwana hu'du lokacin ma waya muke yi da shi sai na fara jina cikin wani yanayi baya na na suka na, ban ma zaci wani abu  babba ba ne amma kuma sai ban 6oye masa ba kamar wasa na gaya masa.

Ai kuwa take naga ya 'daga hankalin sa, ya ringa tambaya ta bayan hakan kuma me nake ji nace bakomai, duk da hakan ransa ya kasa sakewa yace bari ya 'kira Safwan gara inje asbiti aga halin da nake ciki ko kuma ya turo wata Nurse ta duba ni.

Kashe wayar da muka yi abin sai ya 'karu min kamar jira yake yi dama.

Nan na fara cije lips ina kwafa fuska ta, nan take kafin kice miye wallahi har na raina kaina, shi kuwa bayan 'kiran da yayi ya fa'dawa Safwan in sai ya sake 'kiran waya ta  amma ina ji na kasa 'dagawa, sai da ya sake 'kira kafin na 'daure na 'dauka wanda sai a lokacin naji ciwon ya 'dan lafa min ka'dan.

Yace
" Ya dai"
Nace masa
" Babu".
Sai yace" Na 'kira baki 'daga ba.."
Katse shi nayi da fa'din" Wayar ce ai ta fa'di ni kuma na kasa 'dagowa".
Murmushi yayi kawai sai ya tambaye ni yace min" har yanzu kina jin ciwon ko?"
Da sauri na bashi amsa da fa'din
" a a ka'dan-ka'dan ne".
Sai yace" 'karya..ai naji muryar ki ta canza ba kamar 'dazu ba".
Shiru nayi masa hannu na 'daya kan marata ina cize la66ana, jin.nayi shirun ne ya shi fa'din" Yanzun nan Hibbah zata zo ta duba ki, kar ki yi mata rigima kinji".

" Uhum".
Na amsa masa 'kasan ma'koshi na.

Sai yace" Yauwa Nuree na, kar fa ki 'daga hankalin ki idan kinji ciwo sosai sai kina addu'ah kinji".
" Uhum".
Na sake fa'di akaro na biyu.

Sai yace" barin in 'kira inji ko ta taho".
Ban ce komai ba yanzun kam har ya yanke 'kiran.

Ba'a 'dauki wani dogon lokaci ba da yin wayar tasa kuwa sai wata Nurse Hibbah ta zo gidan ta duba ni kamar yadda ya saba yi min idan naji wani canji ajiki na.

Nan tace ai wai haihuwa zanyi, ina jin haka na fara kuka ina 'kiran Ammi na.

Ganin yanda na rikice 'din ne yasa ta faki idanu na ta sanya wayata a silent wai dan kar hankali na ya tafi ga wayar ko da an 'kira ni.

Ina kukan 'kiran Ammi sai naji ciwo gadan-gadan ya taso min, take akalan kukan nawa ya canza na fara na gaskiya, Allah cikin ikon sa kuwa cikin 'kan 'kanin lokaci na haifo yarinya ta 'yar cukul da ita sai dai ace Masha Allah.

Nurse Hibbah ita tayi min komai ta gyara babyn tsaf yarinya sam barka mai kama da Yah Deen abinta.

Sai da ta kammala komai kafin ta ciro wayar ta nan taga tarin missed calls da yake natan ma silent ta saka shi, ni kam ma babu labarin tawa.

Yah Deen ne yayi ta 'kiran ta da dani da yaga duk bamu 'daga ba sai ya 'kira Safwan, shima yayi ta 'kiran Hibban amma ba response hakan yasa ya fito da niyyan zuwa gidan namu da kansa  musamman jin yanda hankalin abokin sa yake a tashe.

Har kuwa ya shiga mota sai yaga Hibbah ta 'kira shi yana 'dagawa kunnuwan sa suka cika  da albishir 'din haihuwa ta tana dariya.
Safwan "Alhamdulillah" ya furta a fili.

Suna gama wayar ya 'kira layin Yah Deen ya samba'da masa labarin shima, ai farin cikin Yah Deen kam abin ba'a cewa komai domin sam bazan iya misalta shi ba.

Hibbah na shirin 'kiran sa sai taga ya 'kira ta shima,  tana 'dagawa ya hau yi mata godiya da fa'din" Nagode Hibbah...Allah ya baki abinda kike so, yaya iyalai na hope duk suna lafiya ko?"
" Lafiya lau".
Nurse Hibbah tace da shi.
" Alhamdulillah" ya sake furtawa a fili sannan ya 'kara da fa'din wai Hibbah ta kula masa da mu kafin ya iso dan Allah.

Tace" Bakomai Dr.

Jiyake Tamkar yayi tsalle saboda murna, a ranar kowa da suke tare sai da suka san yana cikin farin ciki.

Kafin cikar awa biyu da rabi kuwa har ya iso gida, a lokacin ma Mummyn Safwan tazo itama tun zuwanta kuwa Hibbah ta koma asbiti, inda ta taho min abinci daga gidan ta har da kunun tsamiya.

Abincin kam ban iya naci ba saboda baki na babu da'di amma kunun tsamiyan na shashi ba laifi yayi min da'di ga  'kamshin kayan yaji da yaja hankali na.

Tashi na daga bacci kenan ina zaune bakin gado yayin da Baby ke ri'ke a hannun Mummy tana shirin kwantar da ita gefe na....jiki na ciwo yake min ina ta 'da'ddaure fuska ta Mummy kuma na tsaye tana min sannu sai muka ji sallamar sa.

Ko 'daga kaina ban yi ba ina wasa da yatsun hannu na, Mummy ce ta amsa sallamar tasa gami da yi masa barka da isowa, gaida ta yayi idanun sa na kaina, Mummy na amsa gaisuwar tasa take mi'ka masa Babyn, suna gama gaisuwar kuwa ta fita can palour ta zauna abinta.

Yah Deen kam a hankali ya 'karasa bakin bed 'din, gefe na ya zauna tare da mi'ka min hannun sa 'daya, hannun dama na na 'daga na sanya cikin nashi, sai yayi sama da  hannun zuwa bakin sa ya sumbaci hannu na sannan yace" Thank u so much Nuree Ubangiji Allah yayi miki albarka".

Daga yanayin muryar sa zaka fahimci tsananin farin cikin da yake 'dauke da shi.
Chapter 150 · 0% Book details