← Book details Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 211

Sashe 8

Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Fitowar Ammee ne ya katse su gaba 'daya inda Jas ta tashi da gudu ta nufi Ammee ta 'kan'kame ta tana dariya Ammee ma dariyar tayi tace ' 'yar tsohuwa an zo kenan".

" ni ba tsohuwa ba ce Ammee ai ni 'yan mata ce".
Jas ta bawa Ammee amsa tana 'dan turo baki.

" Iyeh lalle kuwa ai ban san kin zama 'yan mata ba sai yanzu".
Ammee ta fa'da tare da 'dago Jas 'din sama suka 'karasa shigowa.

Nan aka sake dasa wani sabon gaishe-gaishe daga nan Ammeee ta kawo musu ruwa daya ke ma dukkan su suka shigo har Sani so babu wata damuwar kai masa nasa ruwan duk anan kowa ya 'dan sha iya yanda yaga zai masa illah Noor ce ka'dai bata kai komai bakin ta ba.

Alhaji Baba ne ya fara mi'kewa ganin lokaci ya 'dan ja ka'dan, yaso iyanzu ace ya da'de cikin masallaci amma zuwan 'ya'yan nasa sai ya katse sa dan haka yanzun sai ya tusa su a gaba daga Deen har Sani driver suka tafi masallacin gaba 'daya.
Jas ma ta so bin su amma sai Deen ya hana ta tare da fa'din kar ta damu yanzu zasu dawo sallah kawai zasu yi.

'Kin yadda Jas tayi har taso ta 'dan fara yin rigima, Ammee ce tayi saurin janyo ta ta rungume tare da lallashi har ta nutsu.

Ganin ya rage su biyu ne yasa Ammee tambayar Noor yanayin zaman su da Deen da fatan baya cutar da ita.

Noor sai tace " Alhamdulillah babu matsalar komai Ammee".

Hamdala Ammee tayi a fili da zuci daga nan sai ta fara yi mata nasiha tare bata 'kara bata ha'kuri akan zaman auren nata inda tace taci gaba da addu'ah Allah yana tare da bayin sa nagartattu tace itama nan tana tayata insha Allahu komai zai dai-daita.

Noor cikin ranta tace " Allah yasa" yayin da a fili kuwa murmushi kawai tayi.

Ammee taso su 'dan ci wani abin mai 'dan nauyi kafin dawowar su Alhaji ganin cewa ita ka'dai ce bata saka komai a bakin ta ba tun 'dazun amma sam Noor ta'ki cin komai agaban Ammee.

Murmushi Ammee tayi tace " wai kin manta wace ni ko Hudah?, ni ce fa Ammeen ki nada 'din nan kike min irin wannan kunyar ko manta ni kika yi?"

Sunkuyar da kai kawai Noor tayi tare da 'dan sake fuskar ta, cikin ranta ta furta " ai da da yanzu ba 'daya bane Ammee, yanzu Noor nake mahaifiyar Jasmine....ba Huda da kika sani a baya ba".

Jas kam babu ruwan ta zagewa tayi ta ringa cin 'ya'yan itatuwan da aka kawo musu a hankali suna 'dan ta6a hira har lokacin sallah yayi sannan dukkan su suka su suka yi alwala suka gabatar da sallar azahar daga nan Ammee taja Jas suka tafi da fa'din zata watsa mata ruwa.

Hanyar 'daki sukayi tare da ro'kon Noor akan ta 'dan ta6a wani abu koka'dan ma dan ita bata san wannan salon ba'kuntan tagaji da shi".
cewar Ammee ta na 'dan dariya.

Ko bayan shigan Ammee ma ruwa kawai Noor ta iya sha daga nan bata iya 'kara cin komai ba.

*****
Su kuwa a can masallacin bayan sun idar da sallah suna wurin sanya takalma dan zuwa gida sai aka 'kira Sani driver cewar mahaifin sa babu lafiya suna asbiti ma har an kaishi amma yana ta ambatan Sani dan haka idan zai samu dama yazo ya duba shi da wuri.

Jin hakan ne yasa Alhaji Baba yace da shi maza ya tafi yaje ya duba mahaifin sa, ku'di masu 'dan nawi Deen ya bashi hakama Baba Alhaji ya bashi na shan ruwa daga nan ko gida bai koma ba suka yi sallama ya tafi da fatan Allah ya tsare hanya ya kuma bawa mahaifin sa lafiya.
(Ameen).

2:38pm suka dawo daga masallaci ganin su biyu ne yasa Ammee tambayar ina driver 'din kuma anan Alhaji Baba yayi mata bayanin meke faruwa itama da taji ta tausaya sosai sai ta bishi da addu'ah da fatan alkhairi.

Tun kafin su kammala cin abinci Jas ke damun Baba Alhaji akan zata je gidan gona.
Sai fa'di take " Baba Alhaji kayi sauri mu tafi da kai tunda Uncle Zaid baya nan".

Ai kuwa yana kammala cin abincin dole suka tafi, sallar la'asar ma a can suka yi ta.

Babban abinda yafi birge Jas a gidan gonan shine kaji da take ganin su da yawan anan na 'kwai (layers) da broillers, sosai suke birge ta idan tazo ta gansu, shiyasa a duk lokacin da ta zo garin to fa sai an kaita gidan gona nan tafi son zuwa yawo.

A baya idan tazo 'kannan mahaifin ta ne ke kaita idan suna gida kenan wato Saif ko Zaid, yanzu kuwa da duk basa nan sai ta ri'ke bawan Allah Alhaji Baba.

Ko da yamma da Deen zai kai Noor gidan mahaifin ta ma su biyu suka tafi cuz har a lokacin Jas bata dawo ba.

Tare suka shiga har cikin gidan Deen ya gaida Ummahn Noor sannan ya fita.

Deen bai wuce ba sai da ya aiko aka shish-shigo da tsaraba da kayan abincin da suka zo dashi, sai da aka shigo da komai kafin yaja motar yatafi bayan sunyi sallama da Noor kasancewar ita a gidan mahaifin ta zata kwana.

Sai kusan maghrib kafin Alhaji Baba da Jas suka dawo gida, Jas na hango Deen zaune a harabar gidan kuwa sai ta 'kwaci hannun ta daga ri'kon da Alhaji Baba yayi mata ta tafi da gudu tana fa'din
" Daddy oyoyo".

'Daga ta Deen yayi sama shima da fara'ar sa yace " my baby Jas oyoyo".

Tana dariya tace " Daddy na kawo maka mango".

Dariya Deen yayi ka'dan yace mata " ai ni bana cin mango mamana sai dai ki bawa Ammeen ki".

Yana maganar ne tare da nufan inda Alhaji Baba yake ta howa a hankali.

Barka da dawowa yayi masa sannan suka 'karasa cikin tare.

Dawowan sun ne Alhaji Baba ya samu labarin tafiyar Noor gida take sai ya tasa yaron sa da suka dawo tare daga gidan gonar da kayan lambu, k'wai da kaji biyar yace akai mata can gidan.

Baby Jas kam ko da ta dawo taga Noor bata nan bata wani 'daga musu hankali ba da yake tana ganin Deen a kusa, sai da dare yayi ne ma ta 'dan so tayi musu rigima amma daya 'kira Noor ya ha'da su a waya shikenan ba'a 'dau dogon lokaci ba tayi bacci.

Washe gari da safe da zaije can gidan sai ya sata a gaba suka tafi tare, inda anan ne Ummah ta samu daman yi masa godiyan 'dawainiyan da suke da ita daga na jiya har na baya.

Deen yace " ah haba Ummah ai bakomai"

Tare suka fito dukkan su Ummah ka'dai suka bari a gida sai Ummie wata jikar Ummah dake zama a wurin ta, lokacin da zai tafi Jas nata yi masa bye-bye har yayi nisa, ranar JASMINE tare da mahaifiyar ta ta wuni, inda suka je gidajen 'yan uwa da abokan arzi'ki yinin ranar kaf basu yita a wuri 'daya ba sai da yamma suka yada zango gidan su Deen ganin yanda ya matsa mata da waya cewa su dawo gida hakanan yawon ya isa.

Wata 'kawar Noor tun ta yarinta mai suna Binta datayi aure da jimawa yaran ta uku a lokacin, in ka ganta ma bazaka ta6a yin zaton sa'anni suke da Noor ba tsabar yanda rayuwa ke juyawa.....itace tayiwa Noor rakiya har gidan Alhaji sai wata 'yar sistern ta da ta biyo su tunda suka je gidansu itama take binsu da ita suka je ko'ina yarinyar batafi 7years ba, sai kuma Ummie da dama tare suka fito tun daga gida 'yar wani brothern Noor ne da ya rasu da jimawa, mahaifiyar ta ma already tayi aure a wani gidan ita kuma tana hannun Ummah ne.
Ummie yarinya ce 'yar kimanin shekaru goma sha biyu goye take da Jas suna 'yar fira.
Gidan Binta ne 'karshe da suka je shine tayi musu rakiya har gidan Alhaji Baban.

Koda suka je gidan kuwa Ammee ka'dai ce a gida itace ma ke sanar da su ai Deen 'din sun tafi gaisuwa da Alhaji Baba zuwa gidan Malam Barau.
Yayin da Ammee ta 'kara da fa'din " kin san har hanzu Alhaji ya kasa nutsuwa da abinda ya farun nan kullum damuwar sa Alhaji Barau".

"Hakane Ammee, hakan yanada kyau ai".

Daga nan shiru Noor tayi bata 'kara furta komai ba, ita kam sam bata son tuno da wasu abubuwan ma da ace 'dan Adam na iya shafe rayuwa da babu abinda zai hana ta binne rayuwar su ta baya tayi updating musu sabuwa fill, amma ba zai yiwu ba, dole idan wani abu ya faru abaya matu'kar mutane na raye to an dinga tunowa dashi kenan ko da kuwa an manta shi.

Binta bata wani da'de ba tayi musu sallama ta koma gidan ta dan maghrib ta gabato, ganin hakan ma yasa Noor ta sallami 'dayar yarinyar da ta biyo sun har ma da Ummie dan itama bata san lokacin da zata koma gida ba tunda Deen baya nan.
kar kuma ta ri'ke yarinyar mutane, dama gidan Ummah suke ne da babu damuwa tunda kakar tace, kuma ma itama Ummie ba mamaki Ummah ta nemi taimakon ta akan wani abin gashi sun wuni basa gida.

Zama sukayi da Ammee suna 'dan hira tare da 'karasa aikin abincin da Ammee ke yi.

Su Deen kam sai da suka yi sallar isha'i kafin suka dawo gidan, gaisuwa kawai sukayi da Alhaji Baba sai ya tambaya sun ci abinci ganin har Jas tayi bacci, Ammi ce ta bashi amsa da fa'din "ehh".
Take kuwa sai yace " Mu'inuddeen ka kaisu gida kaga dare yayi".

Ba tare da musun komai ba Deen ya tashi suka fita bai shiga motan ba sai da ya bu'de mata nata 6angaren ta shiga ya rufe kafin shima ya zaga ya shiga.

Hannun ta ya kamo cikin nasa yana murzawa a hankali tare da janyo ta zuwa jikin sa cikin ra'da ya furta " Nifa bansan ki tafi Nuree mu koma 'daki na mu kwana please".
Chapter 8 · 0% Book details