Sashe 160
Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Dariya ma ya bani dan haka sai nayi murmushi kawai.
Sosai na gamsu da baya nan sa amma ina damuwar dake cikin zuciyata ta ishe ni ta hana ni bada hankali na akan 'ya ta, ni kaina yanzu ba walwalar nake da ita ba balle in iya dawo da farin cikin Baby da take neman rasawa.
Bazan manta ba wani hutu da su Baby suka yi a lokacin na so in dawo da jigilar Baby hannu na saboda na fahimci Sani ba mutunci ne da shi ba musamman da naga yanda yake yawan takurawa yarinyar da ke taya ni aikace-aikace abin sosai yake bani haushi, ga kuma baya dawo min da Baby gida akan lokaci 'karshe ma wai sai ya fara bata kyautar ku'di, wa'dannan dalilan su suka 'kara cire min shi a raina har na sanar da Yah Deen bayan wata tafiya da yayi Jos jinyar mahaifin sa, amma Yah Deen ya 'ki ya goya min baya dole Sani ya cigaba da aikin sa badan raina ya so ba.
Haka muka cigaba da rayuwar mu kowa baida walwalar kirki, har a lokacin Addu'ah ta be wuce Allah yasa 'karamar ala'ka ce tsakanin miji na da wannan Jiddahn ba, kuma na sani ko ba'a fa'da min ba nasan acan Abuja suka ha'du, kuma ai ina jin yanda ake labarin 'yam matan Abuja shiyasa tsoro da fargaba kullum 'kara hauhawa suke min cikin zuciya ta.
Kwatsam watarana ina zaune sai gashi an 'kira ni da wata new number kamar bazan 'dauka ba ma sai kuma na 'daga, sallamar kirki bata yi min ba kawai ta hau yi min tuhuma akan miji na, wai sai na gaya mata dalilin da ya sa Mu'een yake ikirarin ni ka'dai na ishesa rayuwa har mutuwar sa, tace wani irin ri'ko nayi masa har haka da ko bayan idanu na ma baya iya kushe ni".
Sosai naji haushin wannan rainin hankalin nata dan haka sai na nace da ita ta tambaye sa mana tunda saurayin ta ne ai zai gaya mata dalilin.
Daga haka na yanke 'kiran ban 'kara sauraren komai ba daga gare ta.
Allah ya sani naji babu da'di har raina dan har na fara tunanin bakin su 'day ne da shi, amma yanda ta bayyana min irin yanda nake da muhimmanci a wurin Yah Deen shi yafi komai yi min da'di har ma sai ya wanki takaicin 'kiran da ta yi min..kusan kowacce mace naso ta samu irin wannan matsayi wurin mijin ta, abu 'daya ne ni 'din na rasa shine cikakkiyar 'kaunar sa daya kasa bani ni ka'dai, sannan kafar da ya bari har wasu matan ke samun daman shiga tsakani na da shi shima yana bani haushi.
Duk da haka ban bar 'kiran da Jiddah ta yimin ya zauna cikin raina ba dan ko da wasa ma ban sanar da shi ba, da kansa ya dawo yake bani ha'kuri akan maganar tare da yimin bayanin ala'kar dake tsakanin su, ban gamsu ba da bayanan sa ba sam domin nasan indai ba tana da wani marsayi a wurin sa ba da bazata ta6a samun daman ta6a wayar sa ba balle har ta bincika ta 'dauki pin 'dina ta kuma samu guts 'din 'kira na ta tuhume ni akan sa ba, dole akwai wani abu da nasan ba zai iya sanar da ni ba... amma dole na sawa raina yadda da miji na na watsar da waccen batun.
Cikin sa'a sai na ga duk ya dawo da hankalin sa wurin mu, ya kan 6ata lokaci sosai fiye da baya yana hira da ni, ya kan kuma dawo akai-akai ba kamar baya ba da yake 'daukan wata guda be zo ba, kuma ma sai na daina ganin 'kiran Jiddahn ko da yazo gida, sosai na saki raina na watsar da komai kawai na ri'ki karatu na kullum cikin raina da kuma salloli na nake addu'ar Allah ya kare min miji na ya shirya min shi ya dawo da hankalin sa gare ni.
Sai gashi kwatsam rana tsaka ban zata ba ban yi tsammani ba kawai naci karo da wani mummunan abu cikin waya ta, Hafsat mijina yana aikata zina da wata macen da ban ma santa ba kuma aka 'dauka aka tura min dan na gani.
Ya kike ganin zan 'dauki wannan lamarin Hafsat? Yah Deen da na 'dauki soyayyar duniya na 'dora masa na 'dauki duk wata kulawa ta na bashi amma da abinda ya saka min kenan ya munafurce ni ya 'dauki hankali na da kalaman sa 'karya ya kautar da tunani na akan halayyar sa ta hanyar nuna min zallar soyayya.
Lokaci guda na fahimci Yah Deen ba zai ta6a canzawa ba, banga alamun zai iya canza halayyar sa ba, hakan yasa na yanke shawarar tafiya in barshi tafiya ta har abada, na riga na gama ji cikin raina cewar bazan ta6a samun cikakken farin ciki tare da shi ba illah ba'kin ciki a koda wani lokaci, yaushe zan rayu a kullum idanuwa na na cin karo da abinda hankali na ba zai iya 'dauka ba kuma akan mijina, wallahi koda ace bana jin 'kaunar sa cikin raina dole zanji zafi ballantana Hafsat ina matu'kar son shi, ni da kaina bazan iya misalta miki irin 'kaunar sa dake raina ba.
Na gama yanke shawaran rabuwa da shi, tun a jiyan na so inyi tafiya ta domin lokaci yayi da zan fuskanci rayuwa ta in daina yaudarar kaina da sunan ina zaman soyayya da miji na, ko da rabuwa da shi zai illah tani na gwammaci hakan da acecin zauna hallayar sa ta yi sanadin kumburin zuciya ta, amma sai aka samu akasi Baby bata dawo gida da wuri ba, hankali na gida-gida ya kasu, wanda ganin lokaci ya tafi sosai ne na nemi mayafi na na tafi har makarnatar neman ta amma babu labari, na yi tafiyar da tunda mahaifiya ta ta haife ban ta6a yin irin ta ba, nayi kuka kukan da ko lokacin mutuwar mahaifina ban yi irin ta ba Hafsat, da wanne zanji, na rasa farin ciki na tako wani fanni, bayan 'kuncin dake zuciya ta akan Yah Deen sai gashi wani babban al'amarin ya sake faruwa na rasa inda zanga Baby.
Tamkar wata mahaukaciya haka nake jin kaina a lokacin, ta ya zan iya rayuwa babu Yah Deen babu Baby, Jasmine itace sanyin idaniya ta, na gama shirya mana yanda zamu rayu bayan bashi amma ko'ina naje bana samun cikakken bayanin inda zanga 'ya ta.
Hankali na sosai ya tashi fiye da zaton ki Hafsat, ban ta6a sanin yanda ake jin zafin 'da a zuci ba sai jiya da na ga alamun rasa Baby zan yi, domin kaf na bincika amma ba Sani ba labarin su shi da Jasmine...babu tunanin da bai zo raina ba dan gani nake tamkar Sani saida min yarinya yaje yayi.
Daga 'karshe da wannan mummunan labarin naci karo Baby kwance wai ba lafiya a gadon asbiti.
Hankali na ya 'dan kwanta da na ganta, saboda bata ji wani mummunan rauni ba kuma ganin nata koda cikin wani hali ne yafiye min ace ban ganta ba kwata-kwata.
Abin takaici abin ba'kin ciki wai sai Safwan ke sanar da mu abinda ya so waka na koma ince ya faru, Sani ya raping min yarinya...
Kuka sosai ta fashe da shi a wannan ga6ar yayin da tausayin ta duk ya mamayi zuciyar Hafsat.
Hafsat bata ce da ita komai ba, domin abin kuka ne ya same ta da ya kamata ace ta zubda hawayen ta, ko case 'din Jiddah ka'dai ma ya kamata abarta tayi kuka akai ballantana abinda aka yiwa 'yar ta kuma Allah da ikon sa abin duk sai yazo mata cikin rana guda, ha'ki'ka wannan ba 'karamin tada hankalin ta zai yi ba.
Da 'dauki tsawon mintina uku tana kukan kafin ta fara magana.
" Zuciya ta tafasa take yi Hafsat duk da nasan da kaina ina da laifi cikin lamarin cuz da na bawa Jas cikakakken lokaci da natsuwar da zan zauna inji damuwar ta nasan da baza'a kawo wannan lokacin ba za'ayiwa tufkar hanci, amma duk da hakan nasan nawa laifin ragagge when it comes to halin Yah Deen, zato na komai ya wuce abaya, duk da nasan yana tare da Jiddah ahalin yanzun amma ban sawa raina cewar mummunan ala'ka ke tsakanin su ba sau da dama koran wannan tunanin nake yi cikin raina, ashe yaudaran kaina kawai nake yi, yau gashi da kansu suka tabbatar min da abinda suke aikatawa wanda nake da ya'kinin shine ya so faruwa da Baby.
'Kwalla ne masu zafi suka sake gangaro mata...ta sa hannu ta share su da wuri sannan ta cigaba da fa'din" Da kaina nake jin cewar rayuwa ta tazo 'karshe dan bazan iya da halin sa ba Hafsat, yaushe zan cigaba da rayuwa while ina ganin Baby da wani mummunan tabon da na tabbatar sakayyar halin mahaifin ta ce? Bazan iya ba sam, bani da hakkin kowa, in akwai ma sai dai ta Baby ka'dai amma rayuwar Yah Deen cike take da tarin abubuwan Allah wadai wanda nasan a duk lokacin da na kalli Baby sai na tuno da su, duk 'yammatan sa sai da yayi lalata da su daga 'karshe kuma ya guje su...Na tabbata da Yah Deen bai lalata rayuwar 'ya'yan wasu ba da 'kila Allah zai ji 'kaina ba zai 'dora min wannan abin ba, wata 'kil da Allah zai bawa Baby kariya amma kinga da yake alhaki ne sai da aka lalata ta aka 'daura mata wannan mummunar 'kaddarar...taya kike tuanin bazan yanke ala'kar da ke tsakanin sa da Baby ba? ta ya kike tuanin zan bar Baby ta cigaba da kallon sa matsayin mahaifin ta?
Idan na yi hakan sam ban yiwa rayuwar Baby adalci ba...ta 'karashe da shashshe'ka mai cin zuciya.