← Book details Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 155 OF 211

Sashe 155

Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ba 'karamin gajiya nayi da zama ni ka'dai a gidan ba, kewar su nake ji sosai musamman ma shi, domin yanzu na warke sumul kamar ba ni ba, da kaina kuma na zauna nayi tunanin abubuwan da nake yi masa da rashin dacewar su, ko ba komai ai yanzu ya kamata ace na girmi hakan shekaru kusan uku da auren mu.

Duk fa wasu dabarun zama da miji na sansu amma ban san me yake hana ni sakin jiki da su ba, ina matu'kar 'kaunar miji na da ya kamata ace zuwa yanzu yasan hakan musamman da nake da tabbacin cewa baya tare da kowa a yanzun sai ni.

Ganin kamar basu da niyyan dawowa ne ranan kwanan su na goma da ya 'kira ni da safe muka gaisa yana shirin datse 'kiran nayi saurin dakatar da shi da ambatan sunan sa.

Sai yace" Ya akayi?"
Marairaice murya nayi nace" Dan Allah yaya ku dawo gida i missed u all, ko tausayi na ma bakwa ji ni ka'dai ce a gidan Yayah".
A dake ya bani amsa da fa'din" 'kilan bamu da tausayin ne shiyasa Nuree".

" am serious Yah Deen dan Allah ku dawo haka nan, wallahi sosai nayi kewar ku, bana jin da'din zama ni ka'dai 'din nan..".
Sai ce min yayi" Bamu gama hutun mu ba ai sai nan da 1 week kafin mu dawo".
Yace
" Yah Deen aikin ka fa?"
" Wannan matsala ta ce ai ba taki ba".
Sosai na lan'kwasa murya ta kalar tausayi nace
" Yanzu Yah Deen ko dan ni bazaka dawo ba?"
Yace
" Ai baki damu da ni ba balle in dawo saboda ke, nima ki barni in huta a inda ba'a sani ba'kin ciki".

" Yah Deen...".
Rasa me zan sake ce da shi nayi, nan take sai hawaye ya fara tsiyayowa daga idanu na.
Bansan ta ya zai fahimci halin da nake ciki ba, dagsake kenan saboda ni yayi wannan doguwar tafiyar? hankali na duk ya tashi sai nake jin tankar in bu'di idanu in ganni gaban sa, ashe haka yake ji idan nayi masa abin 6acin rai?...in kuwa hakane ya zame min dole in bashi ha'kuri, amma yanzu damuwa ta bai wuci ta yanda zan shawo kansa ya dawo Bauchi ba, ban san yadda zan yi ba sam.

Bance da shi komai ba kawai na yanke 'kiran, take ya 'kira ni amma ban 'daga ba, kuka na ci son raina ranar sosai nayi nadaman halayyar da nake yi masa, domin a 'yan kwanakin wallahi da kaina nake jin kewar sa a kusa dani, kewar tarairaiyar da yake min touches 'din sa da sauran su, abinda tun zama na da shi ban ta6a ji ba kenan...yinin ranar haka wayata ta yini akashe.

Ashe Yah Deen yayi ta gwadawa bai samu ba har zuwa dare, shima kuwa zuwa lokacin hankalin sa sosai ya tashi, ba nufin sa ya 6ata min ba, burin sa ya bani sarari ne tunda ya fahimci bana bu'katan su kusa da ni.

Alhamdulillah domin yanzu ya fahimci hakan da yayin ya taimaka sosai tunda gashi da kaina na 'kira shi da irin kalaman da be ta6a ji daga baki na ba koda wasa...ya kuma fahimci babu 'karya a ciki direct daga zuciya ta suka fito..amma me yasa zan kashe waya ta kuma.

Har megadin gidan mu ya 'kira wai yaji ko gidan lafiya me gadi yace masa lafiya 'kalau, yanzun ma ya 'dakko abincin sa.

Hankalin sa sam duk da haka bai kwanta ba domin ya fahimci abin da shi nake yi, fatan sa Allah yasa Nuree da gaske take yi, Allah yasa ta gane rashin dacewar abinda take yi masa su gyara rayuwar auren su kamar kowa, yayi al'kawarin nuna min so na zahiri duk soyayya ta da yake ri'ke da ita cikin zuciyar sa sanadiyyan abubuwan da nake yi masa duk zai bayyana min matu'kar ya tabbatar da gaske nake yi nayi kewar sa.

Be iya ya sake kwana acan ba domin washegari da sassafe suka kamo hanya tafiya ba ko shiri, Ammi na fa'da tayi masa har tace su bari mana ko zuwa gobe ma amma irin wannan tafiyar ai ba'a son ta, Yah Deen sai cewa yayi ai wurin aiki ne  aka neme shi.

'Bangare na ni kuwa ban sake kula wayar tawa, cikin raina na yanke shawarar bazan sake 'kiran sa haka kuma bazan kunna wayar ba balle nashi 'kiran ya samu daman shigowa in yaso idan ya gama iya hutun da zaiyi ya dawo sai in basho ha'kurin.

Washegari da na rasa abin yi kawai sai na fara  aiki a gidan, tun safe ban zauna ba, na gyara ko'ina tsaf-tsaf lungu da sa'ko cikin gidan na tsaftace kaya na.

Kana isowa sai 'kamshi kawai zaka ji yana tashi, bayan na kammala nima nayi wanka na na shirya cikin doguwar riga na yane kaina da mayafi.

Ko ba komai ni ma zanji nutsuwa tunda sun guje ni, haka na ayyana cikin raina badan Mai gadi bama da ko girki bazan yi ba saboda gajiyar da na yi, amma dole na sai da nayi girki na ajiye masa nasan a inda nasan ya saba 'dauka.
Ragowar kuwa juye ta cikin foodflask 'daya.

Bacci ne sosai yake damu na dan haka sai na kashe komai na wuce bedroom, rigar jiki na kawai na iya cirewa ya saura min saura under wear da bra a hakan nayi kwanciya ta sanin da nayi cewa ni ka'dai ce cikin gidan babu mai shigo min 'daki.

Tun jiyan kuma har yau ban kunna wayata ba, nima haka kawai naji in barta akashen 'kilan ta hakan zai fahimci irin damuwar da na yi da rashin su kusa da ni.

Cikin bacci naji ana shafa min fuska ta tamkar cikin mafarki, ko da na bu'de idanu na sai na ganshi kwance gefe na ya 'dora kansa gefen kafa'da ta.

Da idanun bacci nake duban sa batare da nayi motsin kirki ba dan duk zato na mafarki nake yi...tashin farko na lura da 'yar ramar da yayi wanda ba kowa ne zai fahimci hakan ba sai wanda ya san shi sosai...ko.motsin kirki bana so inyi saboda kar mafarki na ya yanke so nake in ta kallan sa a haka batare da na tashi abaccin ba.

Hakan yasa na zuba masa idanu ina kallon fuskar sa yayin da shima ta 6angaren sa hakan ne ya kasance.

Ganin kamar bazan ce komai bane ya sa shi fa'din" Nuree na".
Yayi magamar cike da shau'ki yana 'dan murmushi

  Idanu na na lumshe sanadiyyan yanda muryar sa ya ratsa min har cikin zuciya ta, take  na kuma bu'de na sau'ke su kan fuskar sa...Alhamdulillah na fa'di cikin zuciya ta bayan fahimtar da nayi cewa ba mafarki nake ba...dagaske shine kusa da ni.
" Yah Deen".
Nace a hankali ta yadda la66ana ne ka'dai suka yi motsi in ma ba kallo na kake ba bazaka da na ambaci sunan mutun ba.

Amsa ni naji yayi da fa'din" Na'am Nureen Deen".
Tambaya na sake jefa masa ina duban sa nace
" Ka daina fushi da ni yanzu?"
Sai yace
" Dole na ai Nuree, ke ma kinsan bazan iya fushi dake ba har na tsawon lokaci ba, amma kullum sai kin 6ata raina sam baki damu da damuwa ta ba Nuree...idan nace zan cigaba da zama kusa dake watarana 'kirji na fashewa zaiyi zuciya ta fa'do...'kilan ma mutuwa ta riske ni batare da kin fahimci halin da na shiga a dalilin ki ba...."
Saurin yun'kura nayi na rufe mai baki da hannu na wanda hakan dole ya tilasta masa yin shiru, kallon cikin idanu na ya tsaya yi wanda a hankali hawaye ya fara gangaro min saman kunci na yana 'diga a kan fuskar sa.

Sai da ya lumshe idanun sa sannan ya 'dago hannayen sa duk biyu ya sa ya rungumo ni da shi yana jin wani shau'ki na 'diban sa, nima 'din kaina na kwantar bisa 'kirjin sa na cigaba da zubda hawaye na.

Gaba 'daya jina nayi na karaya da maganganun sa, ha'ki'ka ban yiwa kaina da miji na adalci ba, ban yiwa rayuwar aure na kyakkyawar runguma ba shiyasa a kullum nake cikin rashin natsuwa, a kullum damuwa ta 'kara yawaita take yi amma taurin kaina ya hana ni tsayawa in fuskanci gaskiya.
Kuka na cigaba da yi wanda ke fitowa tun daga cikin zuciya ta, da kaina nasan bana kyauta masa  sam azaman auren mu da shi gashi har na kai shi ambatan mutuwa duk ta dalili na....
Da muryar kuka batare da na 'dago kaina ba nace da shi" Dan Allah Yayah Ka yafe min bazan sake 6ata maka rai ba...."
Ban kai ga 'karasa maganar tawa ba ya dakatar da ni da fa'din"  Shiii...Ya isa haka kiyi shiru kinji...?".

Shirun nayi kaina bisa bisa 'kirjin sa ina jin yanda zuciyar sa ke harbawa...Yah deen kam wani natsuwa yake jin yana ratsa shi, bai ta6a zaton akwai irin wannan ranar ba da Noor zata yi nadaman irin zaman da suke yi da shi, tayi nadaman abubuwan da take aikata masa duk dama yasan da laifin sa amma sosai ya gaji da irin zaman da suke yi a gidan, ba 'karamin 'kosawa yayi da yanda har yau ta kasa sakin jiki sosai da shi ba, abin na matu'kar ba'kanta ransa musamman idan ya ci karo da ma'auratan da ke rayuwa kushiyar ta gidan sa, Safwan ka'dai ma babban misali ne amma haka ya basarwa baya bayyana sirrin nashi gidan, Allah ne ka'dai yasan yanda abin ke yi masa suya a zuci.

Bai ta6a tsammanin ranar zata zo haka kwana kusa ba,...yau 'din sai yake jin sa kamar ba shi ba, ji yake yau tamkar ya zama wani mutun ne cikakke wanda ya jima yana rayuwa da 6arin jiki..wani 6angaren kuwa tamkar basarake yake jin kansa saboda tsananin farin cikin da zuciyar sa ta shiga.
" _Alhamdulillah_ "
Ya furta cikin zuciyar sa while a zahiri kuma yana murmushi.
Chapter 155 · 0% Book details