← Book details Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 125 OF 211

Sashe 125

Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hawaye na naji ya 'kara gudu ban iya na 'daga ko hannu na ba kuwa domin sharewa ba...kuma har a lokacin ban juya na kalle shi ba...kenan wannan shine auren?
Na gaida shi da safe shima garga'di kawaicya sake yi min, haka zan 'kare kullum cikin garga'di...badan kalaman Ummah ta da na tunobba da babu abinda zai hana ni fita da gudu in bar gidan nan.

Bai damu da yanayin da nake ciki ba sai naji yana fa'din" 'Dauko plates a kitchen ki kawo min".

Tamkar dama jiran maganr tasa nake yi sai kawai na yi waje da sauri na da yake nasan kitchen 'din a varanda yake...sai a lokacin ma na tuna da shi cuz ko 'dazu da na fito ban tuna na le'ka ba.

Tura 'kofar nayi na shiga ciki..ban yi abinda ya kawo ni ba kawai na tsaya na shar6i kuka na son raina sannan na tari ruwa a tap 'din saman sink na wanke fuska ta.

Plates 'din na 'dauko da spoon na 'dauraye sannan kawo masa..da fitowa ta sai na tarar da shi ya sauko saman carpet 'din tsakiyar 'dakin da kulolin abincin agaban sa, nima gaban sa nazo na zo na ajiye plates 'din tare da mi'kewa, idanun sa na hannu na har ajiye bai kalle ni ba naji yace" Je ki
'karo wani".

Kitchen 'din na koma na 'dauko wani plates 'din na dawo..zan ajiye yace" Zauna".

Dole na zauna..ina sake share hawaye na.

Da kansa ya zuba abincin cikin duka plates 'din..abinda ban ta6a gani yayi da kansa ba kenan shine serving abinci.

Gaba na ya tura min batare da yayi magana ba.

Ban kula ba har sai da yayi kusan spoon uku a nashi sannan ganin ban da niyya ne kafin ya kalle ni umarni ya min da fa'din maza in daina wannan kukan in cire hijabin kaina inci abinci...da nutsatstsiyar murya yaci gaba da fa'din" ke baki da wayo ne? Kin ta6a ganin inda mace ta fita washegarin auren ta ne ko kuwa so kike ke ki bar abin fa'di a gari?"

Shiru nayi kawai nayi 'kasa da kaina batare da na cire hijabin ba a hankali na kai hannu na 'dauki spoon na fara wasa da abincin kamar zanci nan kuwa ni koka'dan banji zan iya cin abinci a gaban sa ba.

Shima 'din kuwa bai sake kulani ba har ya kammala ya tashi ya shige bathroom...shirun da naji ne ya sani tunanin cewa bazai kuma fitowa ba.

Tattare kayan nayi kaf na mayar kitchen wanda zuwa lokacin na daina kukan tuntuni musamman ma da naji ya min magana cikin natsuwa sai na 'dan ji damuwata ta ragu.

A lokacin ne kuma na tsaya ina kallon 'kauye a kitchen 'din da ya amsa suna nawa...ni Noorul Hudah wai matar Yah Deen abin fa na matu'kar bani mamaki sosai, wannan 'dan 'kwalisan nan shine wai yau mijina...murmushi nayi mai sanyi har cikin zuciya ta naji da'di ganin komai da nasan ana amfani da shi a cikin kitchen to akwai shi a wannan kitchen 'din Ammi bata rage komai ba..yayin da aka sanya kalolin komai iri 'daya wato kalar lemon green da fari, 'dazu da nazo sam ban kula da kyau ba.

Sosai kitchen 'din ya haska yayi wani kyau da shi duk wani abin da ya kasance cikin kalolin sa babu lemon green to sai aka sanya fari...sosai komai ya 'dauki hankali na na rin'ka jin da'di...nasan ko bama ni ba duk wanda zai ga kitchen 'din dole zai birge shi... _harda su hajiya Nusee ma_.

Farin cikin da na shiga har ya kasa 6oyuwa a saman fuska ta...
Hijabin dake kaina na cire na ajiye shi saman counter na cigaba da sha'ani na....sai bu'de-bu'de nake yi ina sake kallon kayan dake kitchen 'din...duk babu wanda zai ban wahala wurin amfani da shi saboda duk nasan kaf kayan elctronics a gidan Ammi.

Duk yadda akayi 'ko'kari wajen tsara parlourn gidan amma sam banji ya birge ni kamar yadda kitchen ya shiga raina ba.

Ina nan ban sani ba na shagala a kitchen ashe har Zaidu ya kawo aikan da aka yi masa ya sake komawa.

Sai da na gama iya shirme na na fito da hijab 'dina a hannu na kafin muka ci karo da Yah Deen da jikin sa ke faman tashin 'kamshi.

Yasha kwalliya cikin manyan kaya da hula...hanya na bashi ya wuce abinsa cuz naga alamar fita zaiyi.

Ciki na shiga nan na tadda jakunkunan kayan sa a cikin bedroom wanda na tabbatar sune wanda yace Zaidu ya kawo masa.

Sosai naji haushi da har Zaidu ya iya zuwa gidan har ya tafi bai min sallama ba, na tabbata da Saif ne bazai ta6a yi min hakan ba cike da jin haushi nace" Banza mai ba'kin hali". 

Ranar rasa abinda zanyi nayi wallahi gidan duk babu da'di, gashi Yah Deen ma bai dawo ba har sai bayan la'asar sannan ya dawo wannan 'din ma yana zuwa yayi shirin fita ball ya sake ficewa daga ruwa babu abinda ya sha agidan.

Haka na yi ta zama ni ka'dai kewar su Ammi sosai ya dame ni, na kanji sanyi idan naga Ammi ta aiko mana da abinci hakan na tabbatar min da cewa bata manta da ni ba, abin haushin kawai shine da ake aiko wannan 'dan ra'ayin wato Zaidu, maganar arzi'ki ma bata shiga tsakani na da shi kuma da yazo yake komawa...ban san me yake hana Saif zuwa ba..in shi 'din ne kuwa nasan zama zai yi musha hirar mu da shi.

Ummah ta ma sosai nayi kewar ta sai da nasan in ba wani ikon Allah ba zan jima ban ganta ba cuz a tun zama na da ita ban ta6a ganin ta fita zuwa gidn 'ya'yan ta ba sai dai in da wani dalili 'kwa'k'kwara..so na kuwa san a kaina bazata fara ba, gashi nima banga alamun fita ta kwana kusa ba.

Tsakani na da Yah Deen gaisuwa ce kawai dan yanzu ko abinci bamu ci tare, tunda ya fahimci ban sakewa a gaban sa sai ya daina takura ni, a kullum sai ya gama nasa cin abincin sannan nake zuwa inci nawa, sau da dama kuwa cikin kitchen nake cin nawa kamar wata munafuka.

Ni ke yin aikin gidan kaf babu mai tayani, gashi shi sam bai san ganin koda 'dis 'din stain ne a muhallin sa...kullum kazo zaka samu ko'ina tsaf sai 'kamshi da ke tashi a koda yaushe.

Haka kuma bamu ta6a ha'da wurin bacci da shi ba, kullun kan kujera nake kwana shi kuwa yana cikin bedroom abinsa...sallah wannan bai ta6a janmu tare ba kuma gida yake yin har sallahr asubah amma bai ta6a tunanin tashi na in bishi sallah ba, nashi yake yi inyi nawa daban.

Duk da banjin da'din gidan amma rashin kyara da yake min ya sanya hankali na kwantawa...balle yanzu ni da kaina nake yi mana abinci...da farko ma idan nayi baya ko kulawa amma tun ranar da muka yi brekafast tare shikenan daga baya da kansa ma yake zama yace in zuba masa yaci.

Inaso in je gida wurin su Ummah ta da Ammi amma tsoron fa'di nake yi gashi banda waya balle in tambayi Ammi.

Zamana shirun ne yasa na fara jin matsanancin son ri'ke waya ya a hannu na ya kamani..sai dai dole na ha'kura saboda bansan ya zanyi in samu ba ban manta ba da Ammi tace min idan na kwantar da hankali na da kanta zata sa ya siya min waya...to gashi na kwantar da hankalin nawa amma bansan ta yadda zan yi in sanar da Ammi ba.

Abin haushi har su Saif suka koma makaranta ban sani ba...ranar wata laraba lokacin satina biyu agidan sa muka je da shi wai zan kwaso kayan makaranta ta anan na samu labarin tafiyar su Saif makaranta.

Ai kuwa na ringa yiwa Ammi kuka harda shahshe'ka...sosai naji haushin tafiyar tasu batare da mun sake ha'duwa da Saif ba.

Cikin lallashi Ammi ke bani bakin cewa ai Saif kam 'kin zuwa yayi amma ko ita tace da shi suje suyi min sallama kafin tafiyar su amma ya 'ki Zaidu kam dama shi ba damuwar sa bane...Saif kuwa cewa yayi ba yanzu zai je ba bata kuma san dalilin sa na yanke wannan hukuncin ba.

Haka muka 'debo kayan makarantar tawa muka kamo hanyar gida still ina share hawaye na...tun a hanya kuwa na daina kukan da Yah Deen ya banka min wata uwar  harara.

Abinda ya 'kara kwantar min da hankali na shine komawa ta makaranta, tunda na samu ina fita school shikenan na 'dan samu natsuwa...walwala ta ta 'dan dawo.

Sai dai komawa ta makarantar sai batun Ma'u ya dawo sabo, kullum sai anyi gulmar ta musamman ma ni da ake tunanin agidan su Yahvm Deen nake maganrctake zuwa akai-akai, sai wasu na tambaya ta wai dagaske ne 'dan gidan mu ne yayiwa Ma'u ciki?.

Wannan tambayar na matu'kar 'kona min raina amma haka nake daurewa na bada amsa da fa'din" nima ban sani ba.."

Tausayin Ma'u nake ji sosai musamman idan kana jin labarin irin halin da take ciki.

Nasan koma menene ita kanta cikin 'kunci take a yanzu, gashi ina so inje in ganta amma babu dama.

Abakin mutane nake jin labarin wai cikin yazo mata ne da matsala kullum bata da lafiya ta rame sai haske da tayi.

Ji nayi kamar in zubda hawaye na...jikina sanyi 'kalau ranar na koma gida inda na tadda shi a palour yana bacci...da shiga ta ya farka sai na gida shi.

Idanun sa ya sake rufewa bayan ya amsa, ban wuce ba sai nace " Yayah".

Hannun san ya 'dage ya kalle ni sai nayi 'kasa da idanu na a hankali nace " 'kawata ce bata da lafiya dan Allah inaso in je in gaida ta".

" Wacece 'kawar ta ki?"
" Ma'u"
Na bashi amsa"..me yasa meta?"
Ya sake tambaya ta yana sake ruef fuskar sa da hannun sa.

Shiru nayi na rasa abinda zan ce da shi...sai naga ya juya zai gyara kwanciyar sa ganin da yayi bani da niyyar magana, ai da sauri na furta" 'kawata fa Ma'u na gidan Malam Barau".

Fasa juyawan yayi ya tsaya kallon idanu na yana wani tattare goshin sa.
Chapter 125 · 0% Book details