← Book details Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 206 OF 211

Sashe 206

Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yanzu Mummyn Husnah da Hajiya Kareemah mahaifiyar Hisham suna rayuwa ne tamkar 'yan uwa babu ruwan su da wani batun dukiya ko kishi da junan su, sun ha'de kansu suna kasuwan cin su a tare balle ma da yake Hajiya Kareema ma'aikaciyar gwamnati ce shikenan sai Mummyn Husnah ke yi musu jagoranci haka komai yake tafiya musu dai-dai.

Babban damuwan Husnah a yanzu bakomai bane face rashin haihuwa..daga ita har Hisham 'din duk sun damu, banda ma iyayen su da kullum ke taya su addu'a ko za'a dace.

Ita kam Husnah wasu lokutan sai dai ta zauna tayi ta shar6an kuka, domin tasan musabbabin da yakawo mata hakan bakomai bane illah alluran da ta tayi lokacin da take tare da Mu'een shiyasa har yau bata yadda taje asbiti tare da Hisham ba gudun kar asirin ta ya tonu a idanun sa...sau da dama shike sake bata baki akan tayi tawakkali, haihuwa da rashi duk na Allah ne, kuma idan bai nufe su da samu ba ko ma me zasu aikata haka zasu ta wahalar da kansu bazai basu ba, idan kuwa ya nufe su da samu haka nan ma zasu tsinci kansu sun zama iyaye batare da sun wahalar da rayuwar su ko dukiyar su ba.

Sosai take jin da'din halayyar Hisham tana kuma godewa Allah daya ha'da ta da mutun irin sa..taje Umrah taje Hajji kusan sau uku tana ro'kon Allah akan haihuwa amma har yanzu shiru babu labarin komai.

Da kanta ta fara bawa Hisham shawaran yayi aure amma ya'ki, itan ma ba wai tana so yayi auren bane amma a ganin ta rashin adalci ne tayi idan tace da shi bazai yi aure ba tun da tasan matsalar daga gare ta ne.

Hisham 'kin amincewa yayi yace ai a wurin Allah suke nema ba mutun ba, idan kuma ya 6ata lokacin sa yayi auren kuma itama matar bata zo ta haihu ba fa me akayi kenan.

Cike da marairaita Husnah tace
" Duk da hakan dai ka gwada dan Allah, Familyn mu ya yi shiru da yawa Hisham ya kamata kayi wani abin kaima.".

Sai ce mata yayi" Ai ban isa inyi abinda Allah be nufa ba dan haka kima daina 6ata lokacin ki, ni babu wani aure da zanyi".

Da ta ga dagaske yake bazai amince ba sai ta kai 'karar sa wajen iyayen su.

Mummyn tace tafi 'karfafa zancen dan haka dole ta tilastawa Hisham fara neman aure...cikin kwanciyar hankali kuwa ya samu wata yarinya anan Azare ya aura, yarinya ce 'karama dan sacondary school kawai ta kammala aka bashi ita.

Sai a lokacin da kusanci yarinyar sannan ya fahimci akwai bambam mai tarin yawa tsakanin Husnah da yarinyar sai dai hakan bai yasa ya canzawa Husnah fuska ko kuma cin zarafin ta ba, balle ma shi ba gwanin dawo da abinda ya riga ya wuce bane.

Ya dai yi 'ko'kari wajen ganin ya daidaita tsakanin Husnah dayarinyar be yadda ya tauyewa kowa hakki ba kasancewar kowaccen su nada nata kalan muhimmancin a zuciyar sa.

Allah cikin ikon sa kuwa shekarar farko da auren su ta cika shi ne da 'dan ta namiji da Allah ya azurta ta da samun sa, yaro mai kama da ita...murna a wurin wannan familyn ba'a cewa komai...Husnah sam bata yi ba'kin ciki da haihuwar ba amma haka take shiga 'daki ta risgi kuka son ranta dan tasan itace ta cuci kanta abaya, da ace bata biyewa Mu'een ba da duk hakan bai faru ba...kusan kullum sai ta tuna lokacin da ya zubar mata da ciki ashe da rabon bazata sake ganin 'kwanta a duniya ba.

Hakan ka'dai idan ta tuna shi yafi komai 'kona mata zuciya haka ya dinga sawa ana 'dirka mata allurai ba bisa 'ka'ida ba.

Ta kanyi dana sani fin a irga a kullum gashi Allah ya ha'da ta zama da yarinya fitsararriya, duk ta raina ta bata kuma san dalili ba, takan yawaita yi mata habaicin marar haihuwa ko kuma komai a gida sai ta nuna tamkar mallakin 'dan ta ne shi ka'dai, Husnah bata ta6a biye mata ba amma Hisham kansa ya gaji da halin yarinyar.

Duk yadda yaso ta bawa Husnah girman ta abin ya faskara..gani take kamar dan ita ta haihu to bazai ta6a iya yi mata abinda ba shine ba.

Abin ma ya 'kara nin kuwa ne lokacin da aka sake yi mata gwajin ciki akaro na biyu, 'dan ta na da wata takwas ta 'kara samun wani cikin, iskanci, fi'ili da rainin hankali kuwa sai abinda yayi gaba..shab ta manta da cewa Allah ne ke bada haihuwa ba dabara ko kuma isar mutum ba.

Shekaran sa 'daya da wata biyar ta haifi wata yarinyar kyakkyawa da ita mai kama da Hisham sak, yarinyar ne ma Hisham ya so su dam'kata a hannun Husnah amma uwar ta'ki sam, tace bata isa ita da shan bugu gardiya da cin moriya ba.

Akan wannan kalmar Hisham har sakin yarinyar yayi dan sosai ta tayar masa da rigima cikin gida, Husnah ce ma ta 'kara tilasta shi ya dawo da ita 'dakin ta..amma zaman ya kasa yiyuwa dan tana yawan ciwa Husnah fuska shi kuma ya kasa jure hakan kwata-kwata...Bambam cin yarinyar da Husnah kenan dan ita Husnah sam ba ta iya hayaniya ba..tun zaman sa da ita bata ta6a yi masa abinda ya sosa zuciya kamar na Ikilimah amaryar sa ba.

Daga 'karshe auren ya raba gaba 'daya ta hanyar sauwa'ke mata ya cike sakin uku gaba 'daya dan baya so su sake takura shi akan ya maido da ita...dan fitinan yarinyar duk ya ishesa a gidan sam bata 'kaunar a zauna lafiya da ita ba zai iya kullum yana cikin kwantar da murya yana mata nasiha amma a banza ba.

Shi ba me son a 'daga masa hankali bane, zuwan tane duk tasa shi yawan surutai kullum cikin yi mata fa'da yake amma a banza.

'Ya'yan sa duk ya amshe ya bawa Husnah ta kuwa ri'ke su hannu bibbiyu, sosai take kula da su tamkar ita ta haifa, gefe guda kuma tana Addu'ar itama Allah ya ji'kan ta ya bata nata 'dan kafin mutuwar ta, Hisham ne a kullum yake saka mata ran cewa itama da iznin Allah zata haifa masa 'ya'ya hakan yasa itama ta 'dora ranta akan hakan sosai.

*****
Safwan ma yaran sa uku ne yanzu dan Hafsat ta sake haifa masa 'yan biyu mace da namiji suna rayuwar cikin kwanciyar hankali da 'kaunar juna.

'Bangaren Sani kuwa aure ya kasa yiwuwa masa 'yan matan garin su duk gudun sa suke yi suna nuna masa 'kyama, hakan yasa ya ha'kura shima kawai ya cigaba da 'yan sana'oin sa yana kulawa da mahaifiyar sa, sam baya ganin laifin su, a hakan ma yana da ya'kinin basu san abinda ya aikata bane da ko kallon arziki bazai samu daga wurin kowa ba.

Ya dai riga ya sa aransa cewar duk lokacin da Allah ya nufe shi da yin aure ya kuma azurta shi da samun 'yarsa sai ya sa mata suna Aisha..dan Jasmine bata ta6a barin ransa ba..murmushin ta kullum yana nan zane a allon kansa baya mantawa da ita...Addu'ar sa kullum ga iyayen ta shine Allah ubangiji ya basu madadin ta badan halin mu na yan Adam ba sai dan cikar mulkin sa.

*****
Mu'een kam jiki yanzu Alhamdulillahi dan komai yayi sau'ki..watan sa guda a asbitin aka sallame shi wanda kafin hakan sosai idanun sa suka 'kagu da sake son ganin Noor amma shiru shi kuma bai bu'di baki ya tambayi kowa ba, duk da yanzu ya riga ya tabbatar da cewa matsayin miji yake agare ta dagaske amma sam bai nuna za'kewar ba...hakan ma ka'dai idan ya tuna sosai yake jin natsuwa na ratsa shi, yasan Allah ne kawai ya sake bashi wannan damar ba kowa ba, ya kuma yi al'kawarin cika rayuwar Noor da duk wani farin cikin da ta rasa abaya saboda shi.

Yanzu babu abinda ke damun sa illah rashin 'karfin jiki da kuma ciwon da yake ji zuciyar sa nayi masa lokaci zuwa lokaci wannan kuwa inda sabo ya riga ya saba da hakan tun da jimawa so baya damun sa sosai.

Lokacin da suka koma gida Alhaji Baba sai ya tara su ya nemi shawarar yanda ya kamata ayi da sdkiyar Ammi cos har yau 'din ba'a ta6a komai daga cikin ta ba.

Ita Ammi already ma ta sanar da Alhaji cewa ya kakkasa ya warewa kowa nashi kowa yasan kalar sana'ar da zai yi da shi.

Koda Alhaji Baba ya sake neman shawarar ta su ma still Ammi abinda ta sake maimaitawa kenan tace bata so abari wuri guda saboda gudun wani ibtila'in kuma duk dama ba za'a yi fatan hakamn b..
...sauran kam shiru suka yi koda Alhaji Baba ya nemi shawarar Uncle Ja'afar kuwa shi cewa yayi kawai a bu'de gidan mai da shi in yaso abinda ya rage sai asaka jari da shi da izinin Allah babu abinda zai faru.

Da jin hakan kowa yayi na'am da wannan shawaran dan haka Alhaji Baba ya fara shirye-shirye.

Safwan da iyalan sa musamnan suka zo tun daga Bauchi dukkan su dan duba jikin Mu'een kwanan su biyu kafin suka koma da uban tsarabar da su Ammi suka ha'da su da shi dan ba 'karamin da'di take ji ba idan taga mutane na nunawa yaranta 'kauna, haka ta dinga nan -nan da yaran Safwan musamman 'yan biyun nan tana tunawa da lokacin da ta raini nata itama.

'Bangaren Ishaq ma Alhamdulillah yanzu komai normal yake tafiya masa domin ya sake samun wata matar ma nan cikin Maiduguri ya kuma kawo wa Alhaji Baba invitation 'din auren inda yayi murna da faruwan hakan 'kwarai da gaske fatan samun nasara ya bishi da shi.

comment
Vote
Share

*Salmerh ce* 😍💕 *NOORUL* 💕
(Haske nah)

By
*Salmerh MD*

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

_*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

🅿 *93*

Satikai da dama suka shu'de har ya kasance yanzu wata guda kacal ya rage wa Noor ta kammala makaranta, yayin da Yah Deen har yanzu ke hutu be koma bakin aikin sa ba.
Chapter 206 · 0% Book details