← Book details Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 148 OF 211

Sashe 148

Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin labarin da Yah Deen ya bashi ne ya fahimci har yanzu yana shakkan Alhaji Baba indai kan wancan batun ne shiyasa yayi saurin yi masa barazana da sunan sa ya kuwa yi sa'a Yah Deen ya janye dan gani yake tamkar Safwan zai iya aikata abinda ya fa'da musamman yanda yaga ya nuna 6acin ransa a fili shi kuwa ba zai sake kuskuren da Alhaji Baba zai zarge shi kan irin wancan rayuwar ba har abada, tsoron sake fuskantar fushin sa yake yi.

Comment
Vote
Share

*Salmerh ce*😍

💕 *NOORUL* 💕
      (Haske nah)

By
*Salmerh MD*

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

_*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

🅿 *70*

Tun zuwan mu kuwa har yau ban ta6a zuwa Shuwarin ba, Yah Deen shi ka'dai yake zuwa ya dawo abin sa, duk yanda nake nuna damuwa ta  akan son tafiyar amma baya kulani ya kan je ya kwana 'daya tak ya dawo.

Duk bayan tafiyar ta sa kuwa kuka nake yi sosai abu na saboda tsananin son zuwan da nake yi.

Gashi abin haushin ko yaje ya dawo bana samun jin wani labari daga bakin sa abinda yake gaban sa kawai yake cigaba da yi...

Duk yadda nake 'kaguwa inji yace min su Ammi sunce kaza, ko kuma Ummah tayi kaza...haka nake ha'kura domin Yah Deen baya bani labarin komai, ni kuma bana iya tamtayar sa.

*****
        Watannin mu takwas a garin Bauchi a lokacin mun yi nisa da fara zana SSCE, cikin 'dan hutun dake tsakanin Waec da Neco acikin sa  na fara fuskantan wasu sauyi tattare da lafiya ta.

Zazza6in dare, da kuma yawu da baki na ya fara yawan tarawa, abin sosai yake bani haushi har cikin zuciya ta...gashi bansan dalilin ba sam.

Da farko nayi tunanin Maleria ce ke damuna amm sai naga inba daren ba ba na sake jin alamun zazza6i ko wani abu sai dai ko yawun da yake 'dan takura ni wasu lokutan.

Da yake ba gida yake yini ba hakan yasa bai da labarin halin da nake ciki.

Ranar wata Juma'ah zai fita aiki da safe bayan har ya min sallama yana daf da fita daga parlour na 'kira sunan shi.
Cak ya tsaya sannan ya waigo, sai nace" Dan Allah idan zaka dawo ka siyomin magani kullum yawu damuna yake yi sai na nasa abu a baki na.

Kallo na ya tsaya yi batare da ya furta komai ba, yayin da cikin zuciya ta nake ayyana" Allah yasa dai ba 'kin siyomin zai yi ba".

Kawar da kansa yayi ka'dan daga kallona tamkar wani tunani a hankali kuma naga ya tako izuwa gaba na.

Fuska ta ya tsaya kallo kamar mai karantar wani abu.." Me ke damun ki?"
Ya sake tambaya ta as if bai ji me na fa'da da farkon ba.

Ban damu ba na sake maimaita masa cuz sosai nake so inga na daina wannan yawun.

" Bayan shi fa ba wani abu?"
Saurin girgiza kaina nayi.
Sai yace min" In 'dauko mayafina mutafi tare idan an duba ni sai in dawo gida".
Shi da kansa ma daman ya fahimci wani sauyi tattare da ni musamman na rashin sukuni a 'yan kwanakin kawai shiru yayi da tunanin in damuwa ce ke damuna ai da kaina zan fa'di.
               Sai kuma gashi hakan akayi, Yah Deen da kansa ya gwada ni bayan isarmu asbitin nasu.

Bayarwa yayi aka akai Lab shi kuma ya zauna tare da ni, kwata-kwata ma sai ya kasa yin aikin komai, har 'kiyastawa yake cikin ransa yanda zai ji idan hasashen ya zama gaskiya.

Ai kuwa sosai nayi mamakin sa, dan kuwa hauka ne ka'dai be yi ba ganin sakamakon gwajin da akayi min da abinda ke 'kunshe a ciki.
Wai ni Hudah ce ke 'dauke da ciki a jiki na.

Dama tunda yaji abinda na gaya masa da sukayi kama da symptoms in masu ciki sai zuciyar sa ta kasa natsuwa.

Lokacin da ya tabbatar cikin ne dagaske kuwa murna tamkar zai cinye ni, haka ya dinga bin jiki na kisses yana samin albarka da fara'ar sa...Alhamdulillah kawai yake ta faman maimaitawa cikin zuciyar sa.
Haka kawai bazata ya tsinci kansa cikin matsanancin son cikin jini da zuciyar sa.

A asbitin ne aka tabbatar mana da cewa cikin na watanni biyu ne kacal da 'yan kwanaki..godiya wa Allah ya ringa zubawa yana jin soyayyar cikin na 'kara ratsa shi.

Ni kaina naji da'di sosai duk dama ban ta6a kawowa a kaina cewar nima zan haihu cikin lokaci 'kan'kani irin haka ba, amma yanzu da ya kasance na samu cikin sai nake jin da'di har cikin jini na, a gani na ai ko ba komai zan samu abokin hira a gida.

*****
        Samun cikin da nayi shine nasara na farko da na fara samu cikin zama na da shi, da kaina wani lokacin na kanji farin ciki matsananci, har ma sai inyi tunanin ai da na san hakan zai canza min zaman 'kuncin da nake yi da shi da tun farkon dawowar mu garin Bauchi zan ringa ro'kon Allah ya bani kyautar ciki ko dan in samu farin ciki ma, amma ko yanzun ma Alhamdulillah kawai zance domin a yanzu ne na fahimci 6oyayyiyar soyayyar da Yah Deen ya da'de ya ke min wanda bani da masaniya akai koka'dan sai ta dalilin cikin, duk dama wasu lokutan na kanyi tunanin cewa Yah Deen cikin sa kawai yake wa son bani ba amma wasu lokutan da kaina nake sake 'karyata tunani na, domin a yanda nake ganin yanayin sa sai kuma inga kamar abin yafi 'karfin cikin dake jiki na ka'dai.

Kulawa ta musamman yake bani da ko a mafarki ban ta6a zaton samu daga gareshi ba.
Yah Deen har kitchen yana shiga da kansa musamman da safe lokacin breakfast abinda ban ta6a ganin yayi ba kenan a kaf 'din rayuwa ta.

Zallar soyayya da 'kauna mai sanyi gami da kulawa yake nuna min, sha'kuwa ce sosai ta shiga tsakani na da shi amma ta ba'dini, tun zaman mu da shi ko da wasa bai ta6a bayyana min abinda yake so game da ni ba, amma sai gashi yanzu da bakin sa yake irga min, yace babban abinda yafi 'kauna cikin halayya ta shine sanyi na...taurin kai na kuma baya 'kaunar sa sam.

Da bakin sa yake zayyano min 'dumbin 'kaunar da ya jima yake min cikin zuciyar sa wanda kafuwar hakan ya samo asali tun daga ranar da ya fahimci na rufe masa sirrin sa wurin Ammi.

Yace tun daga ranar ya ware min wani matsayi  daga cikin zuciyar sa wanda babu wanda ya kai gurin har gobe, ya bani muhimmanci fiye da kowa a zuciyar sa baya ga ahalin sa.

Ban yi mamaki ba ko da naji hakan daga bakin sa, duba da yanda ya jima yana sanya ni cikin tunani ya 'daure min 'kwa'kwalwa ta na kasa fahimtar takamamme ko shi 'din waye ne da kuma matsayin da nake da shi a wurin sa.

Da kaina yanzu idan na zauna na kanji natsuwa na ratsani, wasu lokutan ni ka'dai idan na zauna sai in ringa murmushi musamman idan na tuno kulawar da yake bani.

Yau ina Addah Maryam, ina Anty Zainab kuzo kuga yanda a rayuwa ta ta canza a gidan aure na, ni ma da kaina nasan ina son miji na, so kuwa mai tsananin gaske.

Yanzu ne na gane cewa miskilanci kawai a jinin Yah Deen yake, bawai yana min bane dan ya tsane ni ni ka'dai ko kuma wani abu daban.

Sai dai kuma duk da hakan har a lokacin ban iya na saki jiki da shi ba, gani nake kamar watarana zai 'kara yi min irin wancan abin, 'kila sai bayan yaga na saki raina da shi sai ya sake kawo wata macen kuma, bazata inzo inci karo da abinda zai iya yin sanadin rayauwa ta, cuz na tabbata a halin da nake ciki na tabbatar da 'kaunar da nasan nake yi masa, nasan matu'kar na sake cin karo da irin wancan abin 'kilan sai dai a 'dauki gawa ta.

Hakan yasa naji ban yadda da soyayyar da yace yake min ba, sai kuma na dawo da tunani na baya, da yake nasan yanzun ma dalili ne ya sanya shi furtawa ada bai ko ta6a nuna min ba, sai na barwa cikin da ke jiki na duk soyayyar da ya nuna min wanda na tabbatar har gobe bazai daina ba matu'kar cikin na nan kwance a jiki na...'kila da ba cikin ba zan ji komai daga gare shi da ya danganci so ba har abada.

Haka na maida kaina kamar na'ura wurin tunani, duk wani abu da ya faru tsakanin mu sai dai in bishi da idanu, amma cikin zuciya ta kuwa tamkar zata fashe saboda yawan tunane-tunane.

Batun kishi ma da kansa yace min shi tun asali ma yakanji matsanancin kishi na tun ma kafin batun aure tsakani na da shi ya gifta, yace ko da dasu Saif yaga muna mu'amala har cikin jinin sa yake jin haushin hakan amma a lokacin sai ya rasa dalilin sa na jin haushin mu gaba 'daya matu'kar ya gammu tare muna walwalar mu, sai daga baya a hankali ya fahimci halin da yake ciki.

Duk kuwa 'yar sha'kuwar da ta gifta tsakanin mu da shi still ba koda yaushe ne zaki gan mu tare cikin farin ciki ba, da yake ma sha'kuwar bata zahiri bace hakan yasa duk kowa ke kama kansa wani sa'in, surutun Yah Deen na zuwa ne lokacin da ya ga dama har ma kiji yana bayyana abinda ke ransa, wanda nima cikin hakan nake 'dan tsintan wasu abubuwa da suka shafe ni, amma da yake wani lokacin yana 'dan canzawa ya koma asalin Mu'een 'din sa sai hakan ya 'kara sawa nake jan jiki na daga gare shi har sai in shi ya nemi zama tare da ni.
Chapter 148 · 0% Book details