← Book details Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 211

Sashe 12

Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana jin ya tambayi dalilin kallon tamkar dama jira take yi sai ta juyo da kyau ta fuskance shi sannan tace " wai jiyan nan me ya sami wayar ka ne Yah Deen muna cikin magana naji ta yanke ko dana sake 'kira kuma bai shiga ba.....miye dalili".

Shi kam ma sai a lokacin ya tuna da batun wayar tasa dake jefe cikin motar, bai ce da ita komai ba sai da ya 'dauko wayar kafin yace " kin ganta ma ni ai sam na manta da ita, tun jiyan tana mota ina jin ba caji ne shiyasa".

Shiru tayi bata sake yin wata magana ba, tasan dai ba rashin caji bane ya sanya hakan, in ma rashin cajin ne ai kuma ba zai kasance ya bar wayar jefe a mota ba.
Sai dai bata tsawaita tunanin a ranta ba, duk kuwa da cewa tana da ya'kinin akwai wani dalili 6oye bayan wannan amma tunda kam shima 'din be nuna mata 6acin ransa ba ai shikenan.

Batayi mamaki ba lokacin da ya jona wayar a caji sai taga yana da kimanin 50% na caji a ciki, kauda kanta tayi tamkar bata gani ba ta koma kallon gefen hanya.

Kafin su isa kuwa aka ringa 'kiran Deen kan wani emergency aikin da ya taso dole tasa suna sau'ka ko hutawa bai yi ba sallahr azahar ka'dai yayi sai ya fito da shirin tafiya da jakar sa ka'dai a kafa'dan sa da yake motar kasuwa zai bi bai taho da mota ba san da zai zo.
_sai fatan Allah ya sau'ki Mu'een lafiya......Ameeen_

*****
Jikin mahaifin Sani yayi tsanani sosai, cuz a lokacin da aka kai shi asbitin ma ko gane ahalin sa bai yi illah sunan Sani da yake iya furtawa a hankali.

Gashi dama yana da hawan jini tun a baya sai kuma wannan ciwon da ya 'kara sako shi a gaba.
Da farko duk sun raina ciwon domin ganin kamar abin bana kirki bane sai babu wanda ya damu, amma tashin farko da ya gigita shi da azaba 'kafar sai take 'kara 'kumburi ga shi baya iya bacci koda dare ne.
Dole tasa suka kaishi wani asbiti dake cikin garin Jos.
Ko a asbitin ma ansha fama dashi kusan wata guda amma abin ba sau'ki sai an 'daga shi an kuma kwantar, daga 'karshe sai suka tattara shi zuwa gida domin a gwada yi masa na gargajiya.

Alhamdulillah kuwa ba laifi,sai aka dace domin kumburin 'kafar tasa ya ragu sosai ba kamar da da yake girma kullum ba.
Sai dai bakin da ciwon ya sanya ne yake sake bu'duwa amma shima suna 'ko'karin sanya masa maganin da aka basu a kullum.

Ganin kamar an 'dauko hanyar warkewa ne ya sanya Sani fara haramar komawa Bauchi bakin aikin sa, amma sai mahaifiyar sa ta taka masa birki.
Domin kuwa shi ka'dai ne 'dansu namiji da Allah ya basu a gidan gaba 'daya, 'yan uwan sa kaf mata ne, kuma duk suna gidan mazajen su, mahaifin nasa kuwa komai sai an taimaka masa kama daga wanka, bawali, alwala sallar ma kanta da sauran su.
Abinci ne ka'dai yake iya kaiwa baki da kansa yaci ya sha ruwa baya ga haka kuwa ba iya yin komai.

Sani dole ba dan ya soba ya sake wani zaman dan kulawa da mahaifin nasa.

*****
'Bangaren makarantar Jasmine kuwa Noor ce taci gaba da kaita makaranta tana kuma 'dauko ta har sukayi exams suka kar6i hutu, daga nan ne sai take barin ta a gida suna zama da Hauwa ita ta tafi nata makarantar ta dawo, dan su ma 'din jarabawar suke yi a halin yanzun so bata wani jimawa take dawowa gida.

Rayuwar su a kullum dai-dai take tafiya musu basu da matsalar komai, sai 'dan abinda ba'a rasa ba saboda halin rayuwa.

Lokacin da hutun Jasmine ya 'kare a lokacin kuma Noor ta fara nata hutun dan haka sai taci gaba da kaita makarantar da kanta kamar baya.

Bata ta6a gajiya ko 'kosawa da hakan ba, bata san me yasa ba amma haka kawai sai tafi jin da'din hakan, tafi jin natsuwa da kai Jasmine tana kuma 'dauko abinta.

Deen ma na 'ko'karin zuwa yana duba su duk bayan 2-3weeks baya ta6a wuce hakan batare da yazo Bauchi ba.
Idan yazo yayi weekend 'din sa sai ya koma Abuja.

Sha'kuwar sa da 'yar sa kuwa babu abinda ya ragu sai ma gaba domin kuwa koda baya gida ma toh kullum sai sunyi waya dashi kusan sau hu'du ko uku a rana.

Zaku yi mamakin irin masifaffen son da yake yiwa Jasmine 'din tamkar wanda akace masa ita ce 'daya k'wal 'kwansa a duniya gaba 'daya, yanzun ko bacci Jas bata yi sai taji muryar Deen, shima d'in da yake yasan abinsa to baya ta6a tsallake lokaci in dai bada wani 'kwa'k'kwaran dalili ba.
8:o clock bata gotawa batare da 'kiran sa ya shigo wayar Noor ba, haka zasu yi ta hira abinsu har sai bacci ya 'dauke ta kafin nan, wani sa'in ma shine yake karanto mata addu'o'in bacci awayar idan ya fa'da itama ta maimaita har su kammala gaba 'daya, a kullum 'karshen maganar sa da Jas shine " I love you Diamond 'din Daddy"

Itama sai tace " i love you Daddy".

Noor kuwa sai dai ta zama 'yar kallo da sauraren su, sau tari tagumi take yi ta zubawa Jas idanu tana kallon ta idan suna wayar, gani take yi da ace Deen ne yayi jigilar rainon cikin Jasmine tare da haihuwar ta da bata san abinda kuma zai aikata ba a rayuwar Jas tsabar so.
Zuwa yanzun baya bata mamaki sai dai kawai tana matu'kar jinjina masa afili da zuciyar ta.

A kullum sai bayan ya gama da Jasmine kafin nata turn 'din yake yi, wanda itan ma ba laifi Deen yana matu'kar 'ko'kari wajen ganin ya bata isassan lokacin sa a wayar, sosai yake nuna mata zallan son da yake mata tare da kewar ta a kusa da shi.

Haka rayuwar su taci gaba da tafiya da da'di ba da'di har aka kafe result 'din su Noor inda cikin rashin sa'a tafita da carryover har guda uku.

Ita da kanta batayi mamaki ba, dan tasan dama da yaya ma take iya karatun, bata kasance cikin 'dalibai masu haza'ka sosai ba.... ba kuma za'a ce da ita doluwa ba, tana nan ne a tsakiya tana lalla6awa and ta 'kara ha'dawa da rashin attending wasu lectures 'din, hatta test tayi missing har guda biyu ta dalilin 'dauko Jasmine daga makaranta, cuz bata tsayawa ta saurari komai matu'kar lokacin tashin Jas yayi to kuwa barin komai take yi tayi tafiyar ta.

Hakan bai ta6a damun ta ba, dan kuwa sama taka kawai ta tsinci kanta da son kaiwa da 'dauko y'ar ta ta da kanta batare da tunanin makomar nata karatun ba.

Hatta da Carryover 'din ma bai wani 'daga mata hankali sosai ba duk kuwa da cewa tana masifar son karatun amma farin cikin 'yar ta da walwalar ta yafiye mata komai.

Deen ne ma ya 'dan yi mamaki da yaji labarin dan kuwa last semester result 'din ta ba haka yake ba, batayi carrying ko wani course ba, tashi 'daya kuma wannan karan sai gata da 'yan rakiya har guda uku...... yaso yaji dalilin hakan amma sai ta nuna masa cewa ita kawai bata gane karatun ne yanzu sosai shiyasa.
Da kansa ya zurfafa tunani ya gano inda matsalar take, sai ya bari akan da hutun ta ya 'kare zai nemo wani driver 'din ya fara tafiya da Jas kafin Sani ya dawo, idan kuma ma ya dawo shikenan Alhamdulillah.

*****
Wasa-wasa har sai da Sani yayi wata uku cif bai dawo ba, sau 'daya Deen yaje duba mahaifin nasa daganan kuwa bai sake zuwa ba dan garin yayi lungu sosai gashi hanyar ba kyau ba gyara, akwai 'kura sosai hakan ya sanya bai 'kara sha'awar komawa ba.
Ya kan yawai ta 'kiran sa a waya su gaisa tare da jin ya jikin mahaifin nasa musamman ma saboda zaman tare, wani sa'in har ku'di yake aika masa tare da 'kara kwantar masa da hankali akan ya nutsu ya kula da mahaifin sa da kyau.
Ya kance da shi kar ya damu kansa a duk lokacin da ya samu daman dawowa Bauchi aikin sa na nan yana jiran sa.

Comment
Vote
Share

*Salmerh ce*😍
[11/17/2019, 9:35 PM] 🌸Salmerh🌸: 💕 *NOORUL* 💕
(Haske nah)

By
*Salmerh MD*

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

🅿 *7*

Watan Sani uku da 3weeks sannan ya samu daman dawowa Bauchi.. ganin mahaifin sa ya samu sau'ki sosai ya warware.

Shi kansa Sani a rame ya dawo duk ya fita hayyacin sa, gashi dama asali ba jikin kirki ne da shi ba, yaro ne matashi 'dan shekara ashirin da uku (23yrs) amma yanda mahaifiyar sa ta sako shi gaba da batun aure ma ka'dai yafi 'daga hankalin sa.

Sam baya son maganar aure a yanzu, yanda yake jima in zaiyi auren nema to Hauwa ce yake ganin zai iya aura dan sosai yarinyar tayi masa, itan ma da ace zai samu daman ke6ewa da ita yana jin da shikenan an wuce wurin.

Sam bai shiryawa yin aure a yanzun ba, hakan ma da 'kyar ya samu ya lo6a mahaifiyar tasa da sunan zai dawo nan da wata 'daya sai ayi maganar auren, jin hakan da ya fa'da ne yasa ta amincewa har ta barshi ya taho, Sani kuwa har cikin ransa koka'dan baida niyyan komawa Jos a kwana kusa.

Ranar da Sani ya dawo Bauchi Deen na gida dan a lokacin shima yazo Bauchi, a yanda Deen ya gansa kuwa sosai ya tausaya wa yanayin sa, dan haka sai ya bashi hutun 1week acewar Deen idan ya huta ya nutsu sai ya fara fita aikin sa.
Chapter 12 · 0% Book details