← Book details Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 144 OF 211

Sashe 144

Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ko bayan gama wayar ta mu da ita ma murmushi  kasa barin fuska ta yayi saboda jin da'din yanda suke bani kulawa, ni kaina yanzu bazan iya ce ga matsala ta ba, cuz ban san ta ba, na kan samu kaina cikin matsananciyar nisha'di idan ina game da waya ta, in 'dauki pics in yi duk yanda nake so da ita, zan yi wanka na in sanya duk irin sittirar da nake so babu mai takura ni, ko shi Yah Deen 'din ba shiga sabgata yake yi ba, ko da kwalliya nayi baya yabamin a zahiri, baya nuna hakan ya birge shi cuz' gudun 6ata min rai yake yi, gani yake kamar idan ya nuna jin da'din sa zan daina sakewa ina abinda raina ke so cikin gidan, banda ma garga'din da Ammi take masa shi da kansa ma baya da burin takura ni ballantana ya hanani sukuni, duk irin dressing 'din da zanyi baya min kallo sau biyu yi yake tamkar hakan baya gaban sa, nima 'din kuwa ba dan shi nake yi ba, ina yin abu na ne kawai saboda nisha'din kaina, babu kowa da ke kawo min ziyara haka nima babu inda nake zuwa, to da wa ma zan zauna balle har inyi hira? ko shi mai gidan ma ba zama yake dani yayi hira ba balle wani daban.

Zama na ni ka'dai da na saba da shi 'din nan shine ya sa sanyi na ya 'karu sosai, har Ammi suke ganin kamar da wani abu da ke damuna.

Duk cikin su kuwa babu wanda bai 'kira yayi masa tambaya a kaina ba, shima 'din ce musu yake yi ba komai, Ammi kam kullum bata gajiya da sake garga'din sa akai na, takance wallahi matu'kar ya zalunce ni Allahn ta nan, yasan me hakan yake nufi dai-dai yake da Allah ya isan ta akansa, har mamakin su yake yi ma wani sa'in, shi a ganin sa ai tun asali haka halayyata take me yasa yanzun kuma ake neman 'dora alhakin akansa dan kawai zama ya ha'da mu? Shifa shiyasa bai ta6a ba'kin ciki da irin zaman namu ba, yanda banaso ya shiga harkata 'dina na hakan yafi masa sosai, aganin sa yawan zama ke kawo sa6ani har asamu matsala ta kunno, in kuwa irin zaman nan ne yasan zamu da'de bamu samu matsala da shi ba, zamu kwana tare mu tashi shikenan ba abinda zai sake ha'da mu har sai ya dawo, idan ya dawo 'din ma baya bu'katar inyi masa komai, zai yi wankan sa ya shiray sannan ya fito yaci abincin da already na ajiye masa, ko da wasa bama ha'da lokacin cin abinci, bai san me zai ha'da ni da shi da har zai zalunce ni ba aganin sa, kuma yaga duk wasu dokoki da ya kafa min tun da aka kawo ni gidan sa acan Shuwarin har yau su nake bi, tsafta ce matsalar sa kuma ba laifi bai ta6a kamani da kuskure kan tsafta ba daga 6angarorin tsaftar jiki da muhalli duk ina kulawa so bashi da matsala dani har abada matu'kar zan kiyaye hakan.

Da abin ya ishi Ammi ne sai tace da shi yayi hanzarin nema min makarantar da zan 'karasa secondary na bata son zama shirun nan.

Bai 'ki ta Ammi ba dan shima 'din kansa abin yana ransa kawai bai 'karasa nutsuwa bane shiyasa bai 'dago zancen ba.

*****
       Sannu-sannu lokaci ya 'dan tafi ka'dan, domin mun doshi makwanni shida da dawowa garin Bauchi, nima yanzu ba laifi na riga na tilastawa zuciya ta da jiki na sabo da komai da ya shafi Yah Deen na daina damun kaina, balle ma da yake ba kullum ne yake neman hakkin sa wuri na ba, yakan yawaita tsallake ranaku hakan kuwa ko nima yafi min har a zuciya ta.

Abu 'daya dake tsaye min rai a yanzu shine ganin da nayi masa da Husnah, bansan me yasa wannan mugun abin ya ke yawan dawo min cikin tunani na ba, na rasa me yasa na kasa mancewa da shi.

Ko abinda ya faru da Ma'u baya damina kamar na Husnah, duk da yake cewa ta dalilin sa Ma'u ta rasa rayuwar ta amma nata bai dame ni sosai ba, a kullum 'kara zirfafawa nake yi cikin tunanin waye miji na? Mecece kuma asalin halayyar sa?"

A yanzu kam na riga na samo wa'dannan amsoshin domin babu makawa dole ne yaci sunan da nasan ko shivkansa ba zai so a 'kira shi da shi ba, babu batun kuskure idan ma nace zan 'kira ala'karsa da Husnah matsayin kuskure yayi amma da'dewan da nayi ina ganin su tarecya zarce a 'kira hakan da kuskure, in haka ne kuwa kenan sun da'de suna aikata son ransu, sannan yazo ya 'kara ribatan Ma'u ya yaudare ta da soyayya 'karshe ya barta ta mutu cikin 'kuncin zuciya...Allah sarki.

Kwata-kwata yanzu na daina tausayin Husnah na daina tausayawa ala'kar ta da shi domin na fahimci harda amincewar ta wannan hawayen da na gani 'kila na wani abin ne daban ba   na irin azabar da naci a wurin sa ba.

Kalmar da ya kamata a 'kira shi da shi koka'dan bana so ko cikin raina in ayyana ta saboda ciwon da hakan ke min, amma ya zanyi...nasani ko da ni ban 'kira shi da sunan ba dole ne da yawan mutane da hakan zasu ganshi, ni kuma aganni matsayin matar sa.

Rintse idanu nayi a hankali hawaye ya gangaro min..a cikin raina na furta 'kaddara kenan...Allah kai ka'dai kasan dalilin ha'da ni da shi, Yah Allah ka shirye shi ya daina duk abinda yake aikatawa marasa kyau, Yah Allah kayi mana gafara gaba 'dayan mu, Ubangiji Allah ka raba mijina da neman mata"....karo na farko kenan da na ambaci Yah Deen da wannan kalmar wato Miji na, ada ko da zanyi masa addu'ah sai dai ince in ro'ka masa gafara da shiriya matsayin Yah Deen, amma yanzu kam nasan babu makawa miji yake agare ni kamar kowa...Ko na 'ki ko naso hakan take ako ina, ciwon da hallayar sa yake min azuciya ni ka'dai nasan abu na.

Gashi bani da abokin hira, ko da ma inada shi ba lalle in iya tattauna batun da kowa ba, shima Yah Deen 'din da farko idan ya ganni wata iri yakan so yaji damuwa ta amma sai in nuna masa ni bani da matsalar komai babu abinda ke damuna.

A kullum baya jin abinda ya banbanta da wannan kalmar duk kuwa 'ko'karin da yake yi wajen ganin ya magance min damuwa ta ko da ban furta ba amma wannan kam ya kasa ganewa balle ya taushe ni...haka na bar abin cikin zuciya ta amma da shi nake ganin sa ko da wani lokaci.

A kullum kuwa zaki ganni babu wargi, ina nan ne haka shiru har abin yabi jiki na, hatta Ummah ta ban iya yi mata dogon surutu yanzu haka ma Ammi...6angaren Ummah ta kuwa ita ka'dai tasan yanda hakan ya dame ta, gani take kamar ina cikin 'kunci ne amma ban gaya mata ba.

Addu'ah kawai take bina da shi a kullum kamar yanda ta min al'kawari kafin na taho.

Cikin hakan akayi min register na makaranta amma wai sai dai in yi full Ss3 har zuwa lokacin da za'a yi SSCE .

Ni kam sai naji hakan yafi min, dan ko ba komai zan huta da zama shirun nan.

Gashi ma Allah ya taimake ni anzo 'karshen semester dole sai next semseter zan cigaba da zuwa so yanzun zan na zuwa ne kawai ina 'dan revising abubuwan da na manta.

_Afuwan please kun jin shiru...._

_Comment_
_Vote_
_Share_

*Salmern ku ce* 😍

💕 *NOORUL* 💕
      (Haske nah)

By
*Salmerh MD*

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

_*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

🅿 *69*

Hakan kuwa akayi domin sai da na sake cin wata guda a gida kafin nan da hutu ya 'kare muka fuskanci karatu.

Fara fita ta makarantar ne nayi sabo da wasu 'dalibai 'kalilan classmate 'dina, sai dai ha'duwa ta da su bai sa komai daga gareni ya canza ba ina nan a yanda nake da halayya ta...sai dai ba laifi sukan ta 6angaren su domin sosai suke 'debe min kewa da surutan su, dan sun iya hira.

Cikin hirarrakin nasu ma nake sake fahimtar wasu abubuwan rayuwa, ni dai ban ta6a fa'di wa ko 'daya daga cikin su komai da ya shafe rayuwa ta ba amma duk da hakan yawan kawo hirarraki yasa har na fahimci ashe akwai wasu dake fama da irin tawa damuwar, a hankali nake 'kara fahimtar cewa irin su Yah Deen na da yawa a fa'din duniya, wa'danda sam ba da tarbiyyar da mahaifan su suka 'dora su akai suke amfani ba.

*****
     Babu yabo babu fallasa nake karatu na, ban kasance daga cikin 'dalibai masu haza'ka da bu'da'd'diyar 'kwa'kwalwa ba, haka kuma bana daga cikin wa'danda za'a 'kira su da marasa 'ko'kari, karatu na dai-dai iyawa ta nake yin ta...a hankali kuma nake 'kara fahimtar salo da hikimar dake cikin rayuwa cikin natsuwa.

Jigon zaman aure, biyayya da kuma kawar da kai duk yanzu na 'kara fahimtar su a 'dan zaman da nake yi da classmate 'dina, duk dama nasan wasun amma ada nakanga kamar Addah Maryam son ranta kawai take gaya min, ko kuma ni 'din sai inga kamar ba iri na ke yin hakan ba, ko kuma tunani na ya tafi akan cewa ni 'din nawa mijin ba nasara zanyi akan sa ba ko da na aikata hakan.

Yanzu me na fahimci ashe yanda nake tunanin Yah Deen 'din ba haka yake ba wanda a yanzu nake ganin kamar ko nima zan iya dawo da hankalin mijina izuwa gareni ni ka'dai, matsalar kawai shine ban san ta inda zan fara ba, inaso inyi hakan amma ban san ta ina zan fara shigan ta ba, hakan yasa na cigaba da bibiyan abin cikin raina.
Chapter 144 · 0% Book details