← Book details Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 211

Sashe 22

Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zaunar da ita yayi cikin d'akin nasa yace ta goge jikin ta ta gama kintsawa kafin ya dawo bari yaje ya 'dauko mata kayan da zata saka.

Koda yaje 'dakin nata bai bi ta kan kayan da suke cikin closet 'din nata ba sai ya bu'de akwatin data shirya ya zazzage shi kaf kan gado.

A ciki ya za6a mata dogon riga da mayafi ha'di da inner set sannan ya koma 'dakin nasa ya kai mata.

Yanda ya bar ta a haka ya dawo ya same ta ta 'kurawa waje guda idanu, Deen sai ya zuba kayan a kan gado sannan ya kama hannun ta zuwa gaban dressing mirror yace " maza ki shirya da wuri mu tafi kinji, ga kayan ki can idan kin gama sai ki shirya ina zuwa yanzu kinji ?".

Yana gama fa'din hakan ya juya ya sake fita.

Hauwa kam tuni ta fice abinta ta 'kofar kitchen, dama yau 'din ba wani aiki bane a gidan ko da safe da tazo ma Noor bata barta tayi aikin komai ba dan bata son damuwa alokacin shiyasa kawai tace mata taje gida anjima da yamma ta dawo, toh ita Hauwa sam sai taji hankalin ta bai kwanta ba shiyasa ta dawo da rana sai kuma ta tarar gidan ba kowa.

Kafin ma ta gama kuwa taji shigowar Noor 'din bayan Deen ya bar kitchen 'din, lokacin data fito ta ga Noor na kuka a jikin sa sai tayi baya a hankali yanda babu wanda zai ji motsin ta ta koma ta fita ta kofan baya ta zauna a wurin.

*****
'Bangaren Deen kuwa 'dakin Noor ya koma kaf kayayyakin sai da ya maidasu mazaunin su har da na Jasmine gaba 'daya ya kai 'dakin ta itama.

Kafin ya fito sai ya 'dan za6o kayan Jas 'din kala biyu marasa nauyi ya zuba cikin jaka sai ya bar su a palour da nufin zasu tafi dashi saboda garin a 'dan kwai sanyi-sanyi.

Kitchen ya koma ya duba Hauwa da niyyan sanar da ita taje ta kintsa 'dakin Noor 'din amma sai ya tarar bata nan, dan haka kawai sai ya sha ruwa saboda rabon da yasha ruwa tun safe, ko a jirgi bai sha ba saboda rashin natsuwa.

Yana komawa 'dakin shima ya shirya sharp-sharp ganin tana sallah sai ya duba agogo, kafin ya gama shiryawan ma har ta idar.

Alwalar ya 'dauro shima sannan suka fita a tare da ita.

Shaf kuma sai ya manta da kayan Jasmine 'din da ya bari a parlour bai tuna dashi ba.

Har sun fita harabar gidan sai kuma Deen ya tuna babu driver yanzu a gidan, duban sa ya kai kan 'dayan motar dake ajiye a garag.

Kamar wasa yace da Noor ta 'dauko mishi key 'din wancan motar inda yayi maganar yana nufan inda motar take.

Da 'dan hanzari ta koma ta 'dauko masa ta bashi yana gwadawa kuwa sai mota ta tashi inda suka shiga suka tafi aciki.

Kafin su isa asbitin sai da ya tsaya a wani masallaci yayi sallah sannan ya dawo suka cigaba da tafiyar.

Tambayar.... shi waye ya sanar dashi inda Baby take... ta jefa masa, kafin ya bata amsa kuma sai ta 'kara fa'din me yasa to basu koma gida ba da ita ba kuma an ta 'kiran wayar Sani bata shiga.

Deen cewa yayi " ki bari idan muka je zaki gani ai da idanun ki".

Jan bakin ta tayi tayi shiru sai dai still wasu tarin tambayoyin ne cike fal a zuciyan ta, amma kawai ta ri'ke a ranta ta cigaba da binsa da idanu, 'kaguwan taga Baby Jas ka'dai ne yafi cika ta a lokacin.

Deen kuwa a wani plaza ya tsaya ya shiga shi ka'dai, 'dan tsaki taja bayan ya bar cikin motar, ko wani tsayuwan sa 'daya ita ka'dai tasan irin haushin da hakan ke bata.

Bata damu da me yaje siya ba balle ta damu da sanin ko menene da kuma manufar su ita dai kawai akaita wurin yarinyar ta.

Sa'an ma datayi shine daga wannan plaza 'din bai k'ara tsayuwa ba sai asbitin da da yake aiki.

Nan kam 6ata rai tayi ganin ya shigo harabar asbitin yaja ya parker sai ta kasa ha'kuri tace " haba Yah kaifa kace zaka kaini......"
" mun zo ai " ya tare ta da fa'din hakan tun kafin ta a takaice.

Da kallon mamaki ta bishi sai kuma ta 'kara bin asbitin da kallo goshin ta ta tattare tana duban sa.

Fargaba ne ya ziyarce ta harma bata san lokacin da ta fito daga cikin motar ba tana fa'din " dan Allah Yah Deen ka gaya min me ya samu yarinya ta? Me take yi a asbiti?"
A ru'de take maganar kamar zatayi kuka.

Bai tanka ta ba sai kawai ya kamo hannun ta suka fara tafiya, bai 'dauko komai daya zo dashi ba duk ya bari cikin mota a hakan suka nufi ciki yana kwantar mata da hankali tare da fa'din " k'addara tana kan kowa Nuree, kuma Jas ma bata fi 'karfin Allah ya 'dora mata komai daga cikin buwayar sa ba, abin luran kawai shine tata 'kaddarar ba jarabawan ta bane a 'kananun shekarun tan nan, 'kaddarar ta iyayen ta ne, jarabawar iyayen ta ne...ina fata zaki kar6e ta hannu bibbiyu ki kuma gode Allah......cikin sa'a ma Baby bata yi wani raunin kirki ba sa6anin Sani da hannun sa 'daya ma kacokam cire shi za'a yi saboda ya lalace gaba 'daya".

Tuni ta fara hawaye wanda cikin kukan ta tace dashi " Yah Deen me yasa me su?"

" They had an accident Nuree, ni kaina bansan ainahin me ya faru ba amma in munje yanzu zamu iya jin bayanin gaba 'daya amma fa sai kin nutsu kinji?

Sai ta 'dage kanta sama.

Cigaba yayi da fa'din " Baby zata warware in sha Allahu domin nata bai yi tsanani ba, kar kuma ki ganta ki fara wannan kukan kin san banaso ko?"

" Uhm bazan yi ba insha Allahu".
Ta fa'di tare da goge hawayen da 'dayan hannun ta.

Direct 'dakin da aka kai Jasmine ya wuce dasu inda suka tarar da wata Nurse da kuma Dr. Safwan a kanta yana 'ko'karin gyara mata mazaunin hannun ta.

Hawaye kawai Noor ke sau'kewa da taga jikin 'yar ta duk farin bandages tana kwance kamar ba ita ba, kamar ba ita ce suka rabu da safe cikin raha ba.

Da gudu ta 'karasa bakin gadon taje ta kama hannun Jas 'din tana kuka tana fa'din " Baby please ki bu'de idan ki ki ganni kinji.....gani nan Baby nazo wurin ki, nice Mummyn ki baby please ki bu'de idanun ki ki kalle ni....."

Safwan ne ya mi'kawa Deen hannu suka gaisa sai yace " kaga ai ka nutsu ba kamar 'dazun ba".

Bayyananniyar murmushi kawai Deen yayi masa na 'karfin hali sai yace " ya jikin nata....naga har yanzu bata farka ba?"

Safwan sai yace
"Ah ah ai kana fita ta farka inaga ma ko gida baka isa ba, da sunan ka kuwa tafara magana " wai Daddy kaga Sani ba, ni kam kace masa bana so".......Ta'ki barin kukan ne shine kawai na sata bacci".

Deen cewa yayi " hmm ai Jas ban san irin dramar dake tsakanin ta Sani ba".

Safwan cikin ransa yace " wannan kam babban drama ne abin Allah wa dai Mu'een....sai fatan Allah ya gyara lamarin kawai"

A fili kuwa shiru yayi ya 'kyale sa dan tun farkawar Jas da yaji sunan Sani a bakin ta sosai ya shiga ru'du duba da yanayin da ya ganta ciki.

Cikin hikima ya rin'ka tambayar ta har ta sanar da shi komai iya wanda ta sani.

Safwan ji yayi tamkar ya zubda hawaye dan tsananin 6acin rai, rashin imanin yayi yawa sosai........babu mamaki abinda ke nan ya sumar da ita tun kafin afkuwar hatsarin.

Da kansa ya sake duba ta bayan ya sata bacci, nan kuwa ya tabbatar da zargin sa.....sosai ransa ya 6aci ya kuma ji haushi sam baiji da'din faruwan hakan ba, wasu mutanen ma sai yake ganin basu da tunani, in ba haka ba mai mutun zai samu ajikin 'yar yarinya kamar Jasmine in banda hauka da rashin tunani.

Da kansa yayi mata duk wani abinda ya kamata, da yake ba sai anyi mata 'dinki ba dan ba'a wani shige ta sosai ba kuma yarinya ce a hankali wurin zai ciko da kansa idan tana 'kara girma.

Yana so ya sanar da Deen amma abin gatsau yake jin sa yafi son Jas da kanta ta sanar dasu tunda tasan duk abinda ya faru.

Juyawa suka yi da niyyar barin 'dakin, suna tafiya a hankali inda Safwan ke yiwa Deen bayanin cewa " Sani shi har yanzu bai farfa'do ba balle asan wasu abubuwan dake damun sa".

Sai Deen yace muje ma in duba shi, yaushe za'a yi masa aikin?"

Safwan yace " sai gobe idan Allah ya kaimu".

" Okay...Allah ya nuna mana goben yasa kuma ayi a sa'a".
Safwan sai yace "Ameen tare kuma da 'kara bawa Deen 'karfin gwiwa akan faruwar lamarin gaba 'daya.

Zuwa yanzun kuwa Noor kwantar da kanta tayi gefen na Jas 'din yanzun bata kukan da sauti, bakin ta kusa da kunnan Jas a hankali take karanto mata addu'ar neman sau'ki gurin mahallici.

Tuni Noor ta 'dago kanta ji da tai Jas ta kama mata hannu tana 'dago kanta kuwa sai suka ha'da idanu da ita.
" Mummy"!
Jasmine tace a hankali.

Sai Noor tayi saurin tashi ta zauna cikin tsananin farin tare fa'din " Alhamdulillah Jasmine.....Yah Deen zo kaga baby ta tashi!".

Suna daf da 'karasa barin 'dakin sai suka jiyo abinda Noor 'din ta fa'di, a tare dukkan su suka dawo cikin hanzari zuwa gaban gadon.

Comment
Vote
Share

*Salmerhn ku ce*
[11/27/2019, 7:09 AM] 🌸Salmerh🌸: 💕 *NOORUL* 💕
(Haske nah)

By
*Salmerh MD*

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

🅿 *12*

Farin ciki ne mai tsanani ya ziyarci zu'katan su, Deen kam ji yake tamkar ya taka rawa, _Alhamdulillah....Alhamdulillah_ kawai yake furtawa a fili ba tare da damuwa ba.
Chapter 22 · 0% Book details