← Book details Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 159 OF 211

Sashe 159

Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kwatsam rana tsaka sai na fara cin karo da sa'k'konin wata mai suna Jiddah cikin sha'anin sa musamman wayar sa...wani abu guda da ni ni kuma arayuwa ta bana iya danne zuciya ta a lokacin, idan naga 'kira ko kuma sa'ko ya shigo masa daga wata daban na kan ji ni cikin tsananin tashin hankali musamman idan abin ya shafi 6angaren soyayya ne, tsoro nake kar rayuwar farin cikin mu ya sake samun gi6i...ina tsoron.kar wata ta 'kwace min shi, ban manta ba lokacin da yake neman Yusrah sosai rayuwar da shi ta canza, ina tsoron kar wata ta sake shiga tsakanin mu dan a yanzun bazan iya jurewa ba.

Tsoro nake ji sosai kar ya kasance wancan rayuwar da yayi abaya da Husnah ita yake sake maimaitwa da Jiddah, tsoro da fargaba sosai suke ri'ke zuciya ta har yana barazanar hana ni sukuni.
       Ina son miji na irin soyayyar da duk wata mace da ta cika mace take yiwa mijin ta, Hafsat koka'dan na tsani inga wata mace ta ra6e shi duk da nasan yaudarar kaina kawai nake yi domin yana da daman auro uku baya na amma na kasa jure hakan.

Ko abaya ma dalilin  kenan da ya sanya nake sake mai jiki na a duk lokacin da ya bu'kaci hakkin sa aguna koda ni bana ra'ayi na kan sawa raina dole, ba dan komai ba sai dan kawai inga na faranta masa, inga cewa ban barshi cikin 'kuncin da har zai iya sha'awan wata macen daban bayan ni ba... ban sani ba ashe hauka ta kawai nake yi.

Comment
Vote
Share

*Salmerh ce*😍

💕 *NOORUL* 💕
      (Haske nah)

By
*Salmerh MD*

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

_*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

🅿 *74*

Da kaina kuma na fahimci jin da'din da yayi da wannan canjin nawa ya kuma bani wani babban muhimman cin da har yau 'din nan nasan ina da shi a wurin sa.

Domin ko yanzu Yah Deen kusance ni sai yayi min sumbatu, ya yaba min, ya samin albarka, ya kuma nuna min cewa ni ta dabance, Hafsat yanzu har na saba, inajin kaina ne tamkar Zahra cikin taurari saboda irin riritawar da yake yimin, saboda shi nake duk wasu abubuwan da mata ke yi dan kula da jikin su dan jin da'din mazajen su, babu abinda bansa kaina na koya ba sabo shi da soyayyar sa, duk wani abu da zai kawo mana farin ciki indai bai sa6awa addini ba Hafsat a hankali na sawa raina shi na koya duk dan saboda Yah Deen.

Da kaina na ringa neman ilimi kan zamantakewa, ha'kuri juriya da biyayya hatta kwanciyar aure duk sai da na nemi 'karin ilimi akan su, duk wani styles na kwanciyar aure na koya dan kawai in faranta masa.

Na kan ji kaina kamar zai fashe idan Yah Deen ya yaba min bisa wani abin da na yimasa musamman a shimfi'dar mu, zuciya ta duka na bashi yake sarrafawa, na bashi rayuwa ta na bashi duk wani abu da ya shafe ni, yayin da shi kuma ya dinga cika ni da 'karyar yana so na yana 'kauna ta, ashe duk 'karya ne, Yah Deen ba zai ta6a so na ni ka'dai ba, ban san ya zanyi da shi ba, wallahi na 'kwammaci da auren sa yayi ya cika gidan sa da mata da zai fi min akan a ringa yiwa yara na kallon 'ya'yan Mazina ci mai neman mata.

     Allah be yoni mai tsananin san a kusance ni ba amma dole nasawa raina tun ban saba ba har nazo na saba kawai saboda shi da farin cikin sa...duk da hakan fa Yah Deen ya raina 'ko'kari na Hafsat ya zanyi masa...ya zanyi masa ya fahimci ciwon da yake 'ko'karin yi min cikin zuciya ta?

Sosai abin nan yake damuna a zuci wanda ni ka'dai na na ri'ke ban sanar da kowa ba ciki kuwa har Ammi na da kullum take cikin tuna min cewar matu'kar naga abinda bai game ni ba tare da shi in sanar da ita, amma bazan iya ba Hafsat ina matu'kar son shi, ina 'kaunar sa, sosai nake tausayin ranar da 6acin ran iyayen sa zai sau'ka kansa, shiyasa ma na kasa sanar da kowa hatta ke da kike matar abokin sa ban ta6a sanar miki ba kin sani, Ummah ta, Anty Zainab da Addah na Maryam duk babu wanda ya sani.

Duk yanda na so zama na da shi yayi kyau amma da zarar mun fara 'daukan hanya sai kiga ya sako wani al'amarin sa daban ya gusar mana farin cikin mu, domin harga Allah ni 'kwa'kwalta 'karama ce, ban iya ha'da abu biyu lokaci guda ba, bazan iya danne kishi na akan sa ba balle in rayu cikin walwala kamar yadda na saba while nasan zahiri ga halin da ya cusa kansa.

Nakan zurfafa tunani wani lokacin sai kuma inga ai kyautata zato ya kamata inyi masa ba munanawa ba, domin ban tabbatar da wacce irin ala'ka bace tsakanin sa da Jiddah...dole na kawar da kaina da sunan basarwa ko ince gudun zato haka na cigaba da rayuwa ta ni da yarinya ta...amma bazan miki 'karya ba Hafsat na dai danne ne kawai amma sanin asalin halin sa yasa na kasa cire batun cikin raina, haka muka koma rayuwar mu kamar baya bana iya wani sakin jiki da shi, duk yadda yaso yaji abinda ke damuna kuma ban iya sanar masa.

*****
    Tun bayan tafiyar sa sai muka raba hanya da su Baby domin nima na fara tafiya makaranta da kaina yanzu nake driving, yayin da Sani kuma yake sau'ke baby ita ka'dai yake yake kuma 'dakkota.

Tun a lokacin abubuwa suka fara ta6ar6arewa ta 6angaren Jamsine, domin ganin ya samu ishshen damar da zai ke6e da Jas ne shai'dan ya fara yi wa Sani muguwar sa'ka azuci, cikin lumana ya fara lalata min tarbiyar yarinya batare da na farga da hakan ba, sau da dama Baby na so ta gaya min wani abu amma sam bana bata hankali na domin asali ni ba gwanar zama in saurari surutan Baby ba ce, baya ga haka ma kuma nima 'din a kullum ina tafe ne da tawa damuwar.

Kwata-kwata sai Allah ya toshe min kwakwalwa ta ya kawar min da tunanin wani abu a raina...sam ban ta6a sa hankali na ga canjin da rayuwar Baby ya shiga ba, dan duk yanda naga ta canza sai in ga kamar damuwar rashin mahaifin ta ne kawai ba komai ba.

Daga baya ma sai bata ko gwada kawo min wata magana, sau tari kuma sai dai in ga ta dawo fuskar ta wata iri ba fara'a sam..cikin raina sai ince" Gado".
Nufi na ta gaji halin ubanta ne wurin rashin fara'a, ban sani ba ashe Jasmine cikin tsananin damuwa take, a hakan ma sosai Sani yake garga'din ta akan kar ta fa'dawa kowa, duk ranar da ya san yayi kissing 'din ta ko wani abu ya kan yi mata garga'di sosai akan kar ta sanar da kowa...hakan kuwa yake faruwa domin bata gaya min, amma duk da haka nasan da ace tana samun damar yin hira da ni da wani lokacin dole zan 'dan ji hint daga bakin ta, amma da kaina na toshe wannan damar.

Kuma Allah da ikon sa sai kiga duk ranar da ta yi su6ul da baka ma tayi niyyan sanar da ni sai kiga wani abin yazo ya shiga tsakanin maganar  dole maganar ta yanke ko kuma kiga ni 'din na kasa sauraran ta har batun ya wuce...kinsan idan Allah yaso jarabtan bawa gaba 'daya 'dauke hankalin sa yake yi akan abin shiyasa koda wasa ban ta6a tunanin wani abu makamancin hakan ba game da Baby.

Da kaina kuma sai na fara experiencing wani abu, bakin Baby jan sa ya 'karu gashi sai ya zama wani iri ba kamar baya ba da yake 'dan cukul amma yanzu ya fito sosai kullum sai kiga kamar a kumbure, duk da nasan bakin dama asali ja ne saboda hasken ta amma sosai ya 'karu a lokacin.

Ranar ma ina mata wanka ne nake tambayar ta ina shafa bakin nace" Wai meke damun ki ne baby abakin ki?"

Rau-rau naga tayi da idanu tamkar zata yi min kuka tana kallon cikin idanu na.
Sai nace" Yana ciwo ne yanzu?"
Kai ta girgiza min alamar a a still tana kallon cikin idanu na.
Sai nace" Shikenan to..na 'karasa da fa'din" Kallon fa? Bana hanaki yi min irin kallon nan ba Baby...yana sa rashin kunya ki daina kinji Ammi na?"
Kai ta 'dage min kawai alamar to.

Allah sarki baiwar Allah ashe zuciyar ta magana ce a 'kunshe amma tana tsoron fa'di saboda garga'din Sani da kuma tsoron hantarar da zan mata akai...wallahi yau ka'dai nayi dana sanin tsangwamar da nake yi mata yafi sau hamsin cikin zuciya ta...wanda na tabbatar da na yi ta ne a kurarran lokaci.

Ranar Baby bata iya tace da ni komai ba nima kuma ban sa komai aka ba har na kammala yi mata wankan...
Damuwar halin da ubanta ke neman shigar da mu ne duk ya dame ni.

Shima 'din da kansa yazo ya fara fahimtar rashin walwala daga Jasmine, dan idan ya dawo yanzu ba kamar da take walwala ba, amma sai yace ai dama yasan rashin kulawar da nake yi matan nan dole zai yi mata illah watarana, a fa'dar sa wai ai dan bana jan ta ajiki ne shiyasa take 'dan shiga damuwa kuma gashi shi baya nan, a lokacin har zama yayi yai min nasiha akan hakkin yaro da Allah ya 'dora akan iyaye...yace min kin hana kanki farin ciki kuma kin.kasa sanar dani abinda ke damun ki Nuree gashi kuma abin naki har ya shafi Baby, idan haka kika ce zaki cigaba da rayuwa Nuree dukkan mu hakan zai cutar mu ne".
Cikin raina nace" Ai kaine ka ja mana".
Kwantar da kansa yayi yai min nasiha wanda daga 'karshe ya 'kara da fa'din idan ban saki raina ba da Ammi zai ha'da ni ta min bulala.
Chapter 159 · 0% Book details