← Book details Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 211

Sashe 40

Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Lumshe ido yayi sannan sannan kamar an ingiza shi yayi taku 'daya, na biyu sai gashi tsaye a gaban su, yana bu'de idanun sa nan take sai ya sau'ke su kan fuskar Hayatuddeen yana dariya har a lokacin, dun'kula hannun sa yayi cikin zafin rai ya bashi naushi a bakin nasa da yasa nan take sai ga jini....batare da 6ata lokaci ba sai ya ware hannun ya sau'ke mishi mari 6arin makauniya a duka gefe da gefen fuskar tasa wanda hakan ya faru ne tun kafin Hayat ya warware daga jin sau'kar naushin.

Sauran abokan tafiyar tasa duk sai suka yi turus gami da matsawa baya ka'dan, yayin da wasu suka kama baki, wani kuwa bakin ya bu'de cike da mamaki.

Yana gama yi mai marin kawai ya watsa hannun sa gami da goge guntun hawayen da suka zubo masa, tafiya yaso yayi batare da ya furta komai ba amma taku uku masu kyau bai yi ba kawai ya fa'di 'kasa warwas a wurin dafe da 'kirjin sa.

Mu'een ya kasance ba mai tara abokai bane haka kuma ba mafa'daci bane, rayuwar sa kawai yake yi cikin school 'din with respect tsakanin sa da kowa, bashi da shiga shirgin da ba nasa ba, abokin sa 'daya ne tun shigar sa makarantar wanda shima shigan su SS3 akayi mai transfer zuwa wata makarantar a can Maiduguri dan ya kammala acan....shiyasa yanzu bashi da aboki ko 'daya.

Amma da yake tun naushin da ya yiwa Hayat na farko hankalin sauran 'daliban da ke gurin ya dawo kansu shiyasa yana fa'duwan akayo kansa ana salati yayin da wasu ke furta" ikon Allah...ganin cewa shine da bugu kuma shine da kaiwa 'kasa.

'Bangaren Hayat kam haushi kamar ya kake shi, haka ya 'daga 'kafafu fuu yayi hanyar waje da fasheshen baki ya nufi offishin mahaifin sa.

Ba'a 'dauki dogon lokaci ba wurin isar da sa'kon abinda ya faru ga headboy 'din makarantar wato Mu'een.

Nan take aka zo daga school administration aka 'dauke shi zuwa asbiti da ambulance cikin hanzari.....suna zuwa aka fara bashi taimakon gaggawa musamnan da yake jikinsa da uniform na makaranta.

Principal da kansa ya nemi Uncle Ja'afar ya sanar dashi halin da ake ciki wanda nan take shima ya garzaya asbitin wurin Mu'een a rikice.

Lokacin da yaji abinda ke damun sa ba 'karamin tashin hankali ya shiga ba, wani 'dalibin ne da suke class 'daya dashi akazo asbitin dan shi sosai Mu'een ke birgesa duk da ba sa wata abota amma duk halin da yake ciki yanada labari.
Shine yake basu labarin duk abinda ke faruwa da Mu'een 'din, tun daga kan team 'din su na ball, da batun debate har abinda ya faru tsakanin sa da Hayat last kafin faruwar hakan.

Uncle Ja'afar ya damu sosai fiye da zaton mai karatu dan masifa ya fara yiwa malamai biyu dake tare da su a wurin su kuma suna bashi ha'kurin cewa basu san da wannan batun ba sam dan ba 6angaren su bane.
" munafukan banza munafukan wofi....an gaya muku shi 'din bashi da galihu ne ko ance muku ba'a son shi, wallahi da Mu'een na fa'da min halin da yake ciki da sai inda 'karfina ya 'kare wajen faranta masa.... da bazan ta6a bari a wula'kan ta min yaro ba, wato dan kunga 'dan mai arzi'ki shiyasa kuka fifita shi akan yaro na ko, to gani gaku wani abu ya same shi kuga mai zai faru tsakani na da ku...aikin banza aikin wofi".

Su kam ha'kuri sukayi ta bashi daga nan suka dan'ka shi hannun Uncle Ja'afar 'din sukayi gaba abin su.

Sam bai tuna ya 'kira Alhaji Baba bama har sai da dare yayi kusan 'karfe sha 'daya jin cewa numafshin Mu'een ya daidaita kafin ya sami hankalin tunawa da Alhaji Baba take kuwa ya 'kira yayi masa bayani.

Ammi taso binsa lokacin da zai taho dan sosai hankalin ta ya tashi da jin abinda ya farun amma Alhaji Baba ya hanata....koda yaje ma bai wani nuna damuwar sa a zahiri ba duk kuwa da cewa ya damun amma daga Allahn sa sai zuciyar sa ne suka san hakan.... ganin yanda Uncle Ja'far gaba 'daya ya fita hayyacin sa ne ya sanya Alhaji Baba 6oye tasa damuwar sa kawai ya dinga kwantar masa da hankali.

Allah cikin ikon sa kuwa kafin Azahar tayi Mu'een ya tashi wasai dashi kamar bashi ba sai 'dan abinda ba'a rasa ba.

Amma harda 'dan rama yayi a kwana 'dayan da yake kwancen, Alhaji Baba fa'da yayi masa sosai akan rashin ha'kuri da kuma biyewa zuciya da har zai je ya bugi 'dan mutane akan kishin ya maye gurbin sa.

Mu'een bai ce dashi komai ba, dan yasan ba Alhaji Baba ka'dai ba kowa ma babu mamaki a haka aka 'dauki abin.....idan ya fahimtar da Alhaji Baba to sauran mutane fa dole akan hakan zasu 'dauke shi......amma shi sam ba nufin sa kenan ba, me yasa zan dake shi dan kawai ya sha gabana akan wani abu?
Wannan ai ba komai bane face halin rayuwa, amma ya bar ni da haushi na da nake ji mana dan me yasa zai 'debo wasu banzayen abokan sa da ko kallo ma basu ishe ni ba suzo su tsaya agaba na suna gaya min magana son ransu.....zan iya 'daukan komai amma banda rainin hankali".
Cikin zuciyar sa yake wannan maganar yayin da a fili kuwa Uncle Ja'afar ya 'dago ya kalla gami da fa'din " ni gida zani Uncle..."

" Baka jin komai ne?"
Uncle 'din ya tambaye shi cike da kulawa.

Sai ya 'dauke kansa gami da kallon gefen gadon yace " ina jin nawi a 'kirjina da kuma zafi sannan numfashi na na sar'kewa".

Da sauri Uncle Ja'afar yace
" Bari toh sai Doctor ya sake dubaka tukunna".

Alhaji Baba shiru yayi yana kallon su har Uncle Ja'afar ya fita 'kiran Doctor....'dakin sai ya zama shiru gaba 'daya.

Mu'een ne ya yanke shirun da fa'din " Ya su Ammi?"
Inda yayi maganar a hankali batare da ya kalli fuskar Alhaji Baba ba kamar ba'a son ranshi ba.

Ajiyan zuciya Alhaji Baba ya sau'ke sannan batare da ya bashi amsar tambayar tasa ba ya 'kira sunan shi da fa'din " Muhammad!"
Cikin natsuwa.

'Dagowa yayi ya kalle shi gami da bashi hankalin sa gaba 'daya.

" Dan Allah ba dan ni ba Mu'een ka daina saka kanka cikin irin wannan rigimar kaji, mutane kala-kala ne Mu'een ni nan na ha'du da ire-iren mutane wasu zuciyar su babu Allah ciki dan Allah ka daina cusa kanka cikin ire-iren su, ba nason wani abu ya same ka ko ka'dan...."

Cikin 'karfin hali yace " Alhaji ka daina ha'da ni da Allah nifa ban shiga rayuwar kowa ba shine ya ke gaya min magana bayan sun 6ata raina shiyasa na maresa".

Alhaji Baba cewa yayi
" amma me yasa bakayi ha'kuri ba to a lokacin?"

" nima ban sani ba Alhaji".
Yace A hankali.

" shai'dan ne ya ingiza ka Muhammad shiyasa ka kasa ha'kuri har ka biye masa...."

Sallamar Zainab ne ya katse maganar Alhajin inda ya amsa mata sallamar tata gami da mi'kewa tsaye....barka da hanya tayi masa gami da gaishe sa wanda suna gama gaisuwar sai yayi waje.

Kallon ta ta dawo dashi kan Mu'een tace " ya jikin naka Mu'een?"

" Da sau'ki Anty sai godiya, please kice da Uncle mu koma gida ni banson asbitin nan".

Murmushi Zainab tayi gami da fa'din " ai kai da gida sai ka warke".

Dai-dai nan su Ja'afar da likita suka shigo bayan su kuma Alhaji Baba ne.

Bayan likita ya sake duba shi sai ya tabbatar musu da cewa ciwon sa bai kammala kwanciya ba tukunna sai an 'kara bashi kulawa.

Da jin haka sai ya lumshe ido gami da furta " ya salam" cikin zuciyar sa.

Haka aka cigaba da bashi kulawa har kwana uku daga nan Alhaji Baba ya koma gida.

Dan likita ya tabbatar musu da cewa zuwa jibi insha Allahu za'a sallame shi.

Washe garin tafiyar Alhaji Baba ne dismissal letter ya same shi har asbiti, abin takaicin ma wai shine Hayatuddeen ne ya kawo masa cike da izza da gadara,
wannan abin ba 'karamin 'kona ransa yayi ba har ciwon sa yaso dawowa sabo.

Uncle Ja'afar ne ya dinga kwantar masa da hankali dan ko shi Uncle Ja'afar 'din ma abin ya bashi haushi amma magangunun Alhaji Baba kafin ya wuce jiya su suka hana shi yin wani yun'kuri.

'Bangaren Mu'een kuwa sai ingizashi zuciyar sa take sake yi akan ya koyawa Hayatuddeen hankali....sam baiji zai iya barin sa haka kawai ba tunda har yayi sanadin da aka kore shi daga makaranta.....in ma akan yayi fa'da ne ai Hayat 'din shi ya tunzura shi, kuma in dole ne sai anyi hakan mai yasa sai Hayat....me yasa ba za'a 'kirashi ya kar6a da kansa ba.

The following day aka discharging nasu suka koma gida, Mu'een bai sake taka 'kafar sa a makarantar ba dan haushi, Uncle Ja'afar ne yaje da kansa ya kar6o mai transfer dan ya canza masa wata makarantar inda anan ya samu labarin cewa babu wanda ya kori Mu'een daga makaranta, Uncle Ja'afar ne ya ciro DL ya nuna musu sunyi mamaki sosai cuz stamp da komai na makarantar ne amma kuma ba su sukayi ba...su shirin bashi horo ma sukeyi na sati biyu kuma gashi nan suka nunawa Uncle Ja'afar.

Uncle Ja'afar ma sai ya sanar dasu wanda ya kai wa Mu'een lettern sai yaga basu nuna wata damuwar komai ba sai ma ha'kuri kawai da suke bashi.

Abin mamaki, da wata makarantar ce a yanda ya sani ya san yin hakan babban laifi ne ace 'dalibi ya aikata irin hakan sa6anin wannan da yake ganin kamar babu adalci cikin lamuran su.

Wannan dalilin ne ya sanya shi 'kin fasa kar6ar transfern acikin satin ya canzawa Mu'een makaranta dan baya son ya 6ata lokaci a gida dan zuwa nan da watanni biyar zasu fara zana waec.

Ba yabo ba fallasa ya fara zuwa makarantar babu laifi tayi masa sai dai bata shiga ransa sosai kamar waccen ba amma a hankali makarantar take shiga ransa musamman da ya fara karantar yana yin makarantar.
Chapter 40 · 0% Book details