← Book details Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 211

Sashe 59

Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

   Wannan karan da yaran turanci ya tambaye ta wai ni 'din daga ina haka?"
Murmushi Ammi tayi masa sannan tace da ni" Je kawowa Yayan ki ruwa mai sanyi ya sha kinji".

Tun ma ban amsa mata ba balle akaiga na matsa a gurin yayi saurin furta " ah no barshi...ban bu'kata Ammi".
Yayi maganar yana kallon Ammi...yana gama maganar kuwa sai ya 'dauke kansa ya koma duban agogon dake 'daure a hannun sa.

" Wai kana nufin baka gane ta bane ko me?" Ammi ta tambaye shi.
Sai ya 'dago ya kalle ta, bata damu ba ta cigaba da fa'din "...Hudah ce fa Hudah ta ko yau 'din ma sai ka mare ta sannan zaka gane ta?"

Murmushi yayi yana murmushin yace da ita" to dan Allah Ammi ni me nace ne?"
" kai de ka sani"
Ammi tace a hankali.
Sai ya girgiza kansa a sace ya sake kallo na cuz maganar Ammin sosai ta bashi dariya, kuma ita tasa ya tuna da ko ni wacece, kawar da kansa yayi gefe dan yanzu kam har cikin zuciyar sa ya gane ni...ala'ka ta da Ammin sa ne har yau baisani ba kuma ya kasa ganewa.

Mi'ka yayi a hankali gami da mi'kewa tsaye..." bari in 'dan watsa ruwa Ammi zan 'dan huta  ma ka'dan amma saboda ina da wurin zuwa anjima".
Bai saurari jin amsar ta ba ma kawai ya juya ya fara tafiya abinsa...Ammi sai ta bishi da idanu sannan tace
" idan ka gama sai kayi magana akawo ma ko 'dan abin sha ne ma"

" okay " kawai yace gami da shigewa ciki.

Ni kam shiru nayi duk jiki na yayi sanyi da ganin sa, dan shi ka'dai ne na kasa sabawa da shi har yau a cikin gidan.

  Wanka yayi ya fito ya mi'ke kan gado cuz already yayi sallar la'asar tun kafin ya taso.

Da hannayen sa yayi pillow yana kallon fan 'din da ke juyawa saman 'dakin, farin ciki sosai yake ji yau zai ga sahibar sa, kamar an mintsine shi kuma sai ya mi'ke ya janyo jakar da ya zo da ita, kayan sawan sa ne ka'dai da sauran kayan amfanin sa, sai wata jaka da ya ciro daga ciki.

Kan gadon ya zazzage kayan sai ga Less na mata mai masifar kyau kala 'daya da turmin exclusive atampa 'daya sai takalmi 'daya da kuma mayafi shima guda 'daya.

Takalmin ya 'daga yana juya shi a hannun sa yana murmushi, a fili ya furta " Allah yasa banyi kuskuren number ba".

   Jin motsin kamar za'a shigo ne ya sanya shi saurin tura kayan 'kar'kashin pillow ya yi tsuru-tsuru kamar mara gaskiya yana kallon 'kofa, he thought Ammi ce zata shigo, sai kuma yaga ashe Zaid ne ma.

Ajiyan zuciya ya sau'ke a fili sannan ya ce da shi " ya akayi?"
" Ammi ke 'kiran ka" cewar Zaidu.
Sai yace
" okay.. gani nan zuwa...let me dress up".
Yayi maganar yana mi'kewa tsaye.

       Bayan juyawan Zaid ne ya saki murmushi, a hankali ya 'dan bigi 'kirjin sa sannan a fili ya furta " silly me!...me yasa zan ji kunyar Ammi idan taga kayan? Ya tambayi kansa.
Wani side na zuciyar shi ne ya bashi amsa da fa'din"...may be ina jin kunyan kar tagani ta gane cewa 'dan ta ya fara soyayya ne?"
" to Alhaji Baba fa, ya akayi da kaina na iya sanar da shi har ma na bashi amanar kulawa da ita?"
Ya sake tambayar kansa.

Baya ya koma ya fa'da kan bed 'din da bayan sa" ....wayyo ni!...ashe abin kunya na tafka babba har haka? shaf hakan bai ta6a zuwa kaina ba...Alhaji Baba zai ce banda kunya!...ohh Yah Allah ya zanyi yanzu?"
Ya ware idanuwa tamkar da wani yake maganar.

Sai kuma ya saki murmushi ya girgiza kansa lumshe idanu yayi sannan yace " Duk laifin kine fa Nanne, da baki shiga zuciyar wannan Deenin ba nasan da bazai iya aika ta irin hakan ba".
Da murmushi ya rufe tunanin kana ya shirya ya fito parlour wurin Ammi.

Zama yayi gefen ta yana fa'din " Ammi ni da nace zan huta kuma sai kika sa a 'kirani?"
Abinci ta nuna masa da hannun ta tare da fa'din " ai nasan idan na barka bacin komai zakayi ba shiyasa"....
" Ai ko yanzun ma ba ci zanyin ba Ammi, banjin cin komai Allah, farin cikin da nake ciki ma ya ishe ni....bari sai zuwa anjima can babu mamaki zan nema".
Da mamaki Ammi ke kallon sa har ya dasa aya a maganar tasa sannan tace..." Farin ciki ne zai hana ka cin komai Mu'een? yau ne ka fara ganin mu? ko kuma yau ne ka fara zuwa garin nan?"
" Ai yau 'din na musamman ne Ammi".
Yayi maganar yana murmushi.

" Kai de kasani"
ta fa'da tana murmushin itama,  while a cikin zuciyar ta ita ka'dai ta san tausayin sa da take ji, tasan cikar farin cikin nasa ba na ganin su ka'dai ba ne, sam bata son wannan fara'ar tasa ta 6ace daga kan fuskar sa, sai dai tasan wannan dole ne, ko ba yanzu ba, ko anjima ko gobe, sati, watanni ko shekara matu'kar mummunan labarin ya isa kunnuwan sa dole farin cikin sa zai yi masa 'kaura.

Har ya sumbaci goshin ta ya wuce ciki bata lura ba sai bu'de idanun ta tayi taga baya nan.

Tagumi ta zabga nan kan dinning 'din kawai tausayin sa na 'kara shiga dukkanin ga6o6in jikin ta.

Alhaji Baba ma yau har sai da aka idar da sallar maghrib kafin suka dawo cikin gidan tare shi da yaran nasa da duk suka ha'du a can masallaci.

Suna ha'duwa Alhaji Baba ya saki fara'a ya bashi hannu tare da fa'din...
    " ....sau'kan yaushe?"
" Tun jiya da safe Alhaji"!
Mu'een ya bashi amsa da fa'din hakan.
Alhaji Baba sai yace
"Ashe har ka tsufa gidan ma ni ban sani ba?"

" Ni ai har na yi fishi Alhaji, awanni na kusan biyu a garin nan amma ka 'ki dawowa ai da niyyya ta ma yanzu in bika can gidan gonar inga ko lafiya".
" Shi kenan ai yanzu kam tunda gani nazo, ayyukane yau 'din suka 'dan taru mana sai a hankali".

" babu laifi Allah ya taimaka"
Cewar Yah Deen kenan.

Koda suka shiga cikin gidan ma a parlour suka zauna shi da Alhaji Baba suna sake gaisawa, su Saif kuwa 'dakin su suka wuce dan dama basu zama da shi suyi hira, dama Alhaji ka'dai ne amma da Deen kam a a.

Ni kuwa da Ammi muna 'dakin ta tana duba Hisnul muslim yayin da nayi kwanciya ta daga gefen ta har bacci-bacci nake ji yana shirin dauka ta.

Mu'een bai yadda ya zauna nesa da Alhaji ba saboda tambayar da yake son yi masa dan haka gefen sa ya dawo ya zauna a hankali cikin ra'da yace " Alhaji Baba amana ta"!
Ido Alhaji ya 'dan bu'de yana kallon sa a 'ko'karin sa na ganin ya 6oye damuwar dake cikin ransa....cikin 'karfin hali yace da shi " amana wace iri?"

" Haba Alhaji, ai amana guda 'daya tak na bari a hannun ka kuma ita nake tambaya fa?"
ya 'karashe da shagwa6a wa Alhaji Baban.

Kasa juran kallon sa cikin yanayin Alhaji Baba yayi sai kawai ya kauda kansa gefe, sannan a hankali cikin basarwa yace " ai ni har na manta da batun ma gaba d'aya".
Mu'een zai sake yin wata magana sai Alhaji Baba yayi saurin mi'kewa tsaye bai jira jin komai ba kawai ya nufi hanyar 6angaren sa yana fa'din " idan ka gama ka sameni ciki mu 'karasa maganar".

Ido Yah Deen ya lumshe gami da mi'kewa tsaye shima ya wuce 'dakin sa, wata arniyar shadda ya ciro mai kalar sararin samaniya sabuwa dal ya sanya ajikin sa, agogo, hula da takalmi ma duk ba'a barsu abaya ba...ya dauki a'kalla kusan rabin sa'a kafin ya kammala shiryawan cuz cikin sanyi yake yin komai, can 'kasan zuciyar sa yake jin babu da'di sai dai bai san dalili ba sam.

  Sai da ya gama 'daura links 'din hannun rigar sa kafin ya sake taje gashin kansa, turare ya sake fesawa ajikin sa mai sanyin 'kamshi...sannan yaje ya maida kayan da ya siyo matan cikin leda cuz tun 'dazun bai sake bi takan su ba...da gama sasu cikin ledan sai ya ajiye gefen gado da niyyar da ya dawo daga wurin Alhaji kawai sai ya 'dauka ya wuce.

   Agogo ya kalla sannan ya fito a hankali yana gyara hular kansa ya nufi 6angaren Alhaji Baba, sallama yayi aka bashi iznin shigowa inda yaje ya samu Alhaji zaune har ya fito daga wanka ya shirya cikin farar jallabiya yana 'ko'karin shafa man zafi kan gwiwan sa.

A hankali ya 'karasa ya kar6i man zafin yana fa'din " Alhaji har ka fara abin tsoffi tun kafin ma kayi jika ko 'daya ko?"
Murmushin ya'ke Alhaji Baba yayi sannan yace " in bazaka yi ba bani abina ni".
" a a gashi inayi ai Alhaji".
Mu'een ya fa'di yana shafa man gami da 'dan massaging gwiwar a hankali.

'Dan satan kallon sa Alhaji Baba yayi sai ya cigaba da kallon gwiwar tasa " sai ina haka na ganka cikin shiri kamar me shirn barin gari?"
" Unguwa zani"
Ya bashi amsa a takaice.
" To bani abu na na 'karasa kar na 6ata ma lokaci...maza yi tafiyar ka".
Mu'een 'kara yin 'kasa yayi da idanun sannan yace
" A ah ai sai naji dahir daga bakin ka kafin zanje, kar inje a koro ni dan bafa sani na akayi ba Alhaji".
" Har ina ne haka?"
Alhaji Baba ya sake tambaya as if bai gane inda zancen Mu'een 'din ya dosa ba.
Sai da ya saki murmushi kafin ya biyo bayan ta da fa'din " zance fa zani...shiyasa ma na shirya da wuri dan ban son dare yayi sosai".

Ido Alhaji Baba ya lumshe cikin zuciya ya furta" Innalillahi wa inna ilaihi raji'un..."
A hankali ya sake furta sunan _Muhammad_ .

'Dagowa yayi ya kalle shi batare da ya amsa ba jin cikin lokaci 'kalilan muryar Alhaji Baba ta canza...'dan matsakaicin hasken 'dakin bai hana shi hango kwantacciyar damuwar da ta bayyana kan fuskar Alhajin ba.
Chapter 59 · 0% Book details