Sashe 180
Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sosai yayi mamaki don kuwa kafin ya shigo sai da ya tambayi Bala mai gadi ya tabbatar masa da cewa yana ciki kafin ya iso.
Jim ya tsaya da tunanin ko yana bayi ne shiyasa yaji shiru, parlourn babu wadataccen haske sosai duk da haka sai ya fara bin ko'ina da kallo yana daga tsayen bai motsa ba.
Can gefen doguwar kujera ya hango abu a zube sai ya 'dan tsuke fuska da tunanin me kuma ya zubar a wajen.
'Karasawa wurin yayi a hankali ya tsaya yana duban abin da ya gani, komawa yayi ya lalu6i switch ya kunna haske ya grawaye parlourn gaba 'daya nan idanun sa suka tabbatar masa da abinda ke 'kasan tiles in.
A firgice ya furta _subhanallahi_ , take ya fara duba shi cuz yasan koma ina yake yanzu cikin mawuyacin hali yake, 'dakin sa ya fara le'kawa sai dai nan ma da ya tura sai yaga duhu ba'kiri'kirin nan yayi tunanin ko baya nan 'dakin, har ya juya da nufin duba sauran 'dakunan sai ya jiyo nishin sa dake fita da 'kyar.
Komawa yayi da sauri, bai ma tsaya ya kunna wutan 'dakin ba ganin kamar zai 6ata mai lokaci kawai ya ciro wayar sa ya kunna hasken ta wanda a lokacin tsaye yake a bakin bed 'din yana kunna hasken ya ganshi lullu6e cikin bargo.
Yanda yake jiyo yanayin fitar numfashin sa ka'dai ma already ya rikitar da shi.
Da 'dayan hannun sa ya yaye mayafin nan yayi arba da fuskar sa idanuwan sa a lumshe yana fitar da numfashi da 'kyar....ba bu'katar sai ya sake ta6a jikin sa cuz jikin mayafin ka'dai ma ya tabbatar masa da yanayin da jikin sa ke ciki.
Sunan sa Safwan ya 'kira yana ji amma bai iya ya amsa ba, sake 'kira yayi amma still ya kasa bu'dan baki ya masa shi cuz sosai ya galabaita gwanin tausayi...hankalin Safwan gaba 'daya ya tafu ne ga zafin da yaji jikin sa yayi sosai ya rikitar da shi.
Hannun sa na dama na dafe da kan 'kirjin sa saitin zuciyar sa yana numfashi da 'kyar...idanun sa a lumshe.
Ko ba'a fa'da wa Safwan ba yasan sosai Mu'een ke jin jiki domin shi mutun ne mai matu'kar jarumta, ya kan iya daure ciwo yayi ta tafiya da shi indai ba fin 'karfin sa yayi ba.
Ko ciwon zuciyar sa ma ba ko wani lokaci bane yake bari a kwantar da shi, ahakan zai ta tafiya da shi har ya sau'ka da kansa sa6anin 'yan kwanakin da dauriyar sa ta kasa yin amfani, duk ya fita hayyacin sa gaba 'daya.
Fita yayi da sauri ji yake tamkar ya zubda hawaye, ya rasa da me ya kamata ya kwatanta wannan abin,.kansa ya fara kullewa.
Mai gadi ya yiwa magana yazo suka kama shi, sai da suka sanya masa kaya jeans da tshirt sannan suka fitar da shi.
A motar sa suka sanya sa sannan ya sanar da Mai gadin cewa asviti zai kaisa dan Allah ya kula da gidan 'kilan ba yau zasu dawo ba.
Jinjina kai Bala yayi zuciyar sa cike da tausayin ogan nasa, domin yasan abubuwa ne kawai suka yi masa yawa ba komai ba.
Da fitan su sai Bala ya koma ya tsaftace parlourn yana yi yana girgiza kansa...lokaci 'kalilan gida ya zama wani iri kamar ba gidan da suka saba walwala ba.
Hauwa kam tunda Jasmine ta rasu ya lura itama bata saki jikin ta ba, da farko da mahaifyar ta suka zo ta'aziyan Hauwa na kuka sosai dan Jasmine mutumiyar ce, ko daga baya ma kusan kullum sai tazo ta gaida Noor jiya da yau ne ka'dai bai ganta ba...bai sani ba ashe Noor ce tayi mata bayani a 6oye cewa zasu bar garin ne.
Da yake asbitin nasu ne so suna zuwa aka hau bashi taimakon gaggawa, Safwan sai da aka tabbatar masa da cewa yayi bacci kafin hankalin sa ya 'dan kwanta.
Sai lokacin kuma ya iya ciro wayar sa ya 'kira Hafsat dan tun 'dazun take ta 'kiran sa amma bai iya ya 'daga ba.
Nan yayi mata bayanin abinda ke faruwa tare da tabbatar mata da cewa anjima ka'dan zai dawo gida tunda ya samu bacci... itama Hafsat cike da tausayawa ta nuna alhinin ta a bayyane, duk abubuwan da suka faru abaya amma sosai take tausayawa Dr. Mu'een domin kuwa ga dukkan alamu yayi nadamar komai.
Da gama wayar ta da Safwan ta 'kira Noor, nan ta fara yi mata nasiha tana nuna mata rashin kyautawar ta, ita ce ta bayyana mata halin da yake ciki a lokacin...Noor kam bata ce da ita komai illah kuwa da take yi hadda sheshshe'ka, da hannun ta 'daya ta toshe bakin ta tana kukan tausayin su gaba 'daya.
Hafsat kam jin Noor bata tanka ta illah kuka ya sata fa'din" Ki dai nutsu ki sake tunani Noor kar ki biyewa zuciyar ki please.."
Daga haka ta yanke 'kiran ta bar Noor da aikin kuka.
Ita sam ta rasa inda zata sa ranta.
Cikin wannan halin Ammi tazo ta same ta ai kuwa masifa ta hau ta da shi wanda dole daga 'karshe lallashi ta koma dan Noor ta kasa yin shiru.
Tun lokacin da Safwan ya sanar da ita cewa Noor sun wuce da su Ammi hankalin ta ya kasa kwanciya, balle da ta 'kira ta ji kukan da take yi sai hankalin ta ya 'kara tashi.
Bayan isha'i ta sake 'kiran ta amma sai taji baya tafiya akashe, sosai taso ta sake yi mata nasiha taja hankalin ta cikin natsuwa akan tafiyar da tayin cuz aganin ta ba mafita bace kwata-kwata, da ha'kura tayi kawai suka rungumi juna suka gyara dukkan kurakura su da zai fi...ga shi da alama itan ma ranta bai sake da tafiyar ba tunda kuka take yi.
Sai dai rashin samun nata bai bari ta fitar da abin ranta ba.
*****
'Bangaren Safwan kuwa kafin ya tafi sai da ya bi ya duba Sani, a koda yaushe idan kaje zaka same shi ne cikin wani mawuyacin hali, har yau 'din cikin dangin sa babu wanda ya san halin da yake ciki, shi da ya fito da niyyan neman abin yi sai gashi zai koma musu gida da hannu guda sanadiyyan son zuciyar sa.
Kuka sosai yake yi yana tausayin kansa, dan yasan dole Allah sai ya hukunta shi, gani yake wannan bakomai bane akan tanadin da Allah yayi masa, kullum cikin zuciyar sa istighfari yake jerowa yana kuka, yana kunyar ranar da zai ha'du da mahaifiyar sa yaba ta labarin abubuwan da ya ai kata cuz tabbas dole ya bata labarin da bakin sa, ayanzu ba shi da za6i illah ya maida hankalin sa ga neman gafara wurin ubangijin sa.
Tunda yaji labarin mutuwar Jasmine daga bakin Safwan shikenan ya rasa natsuwa.
Kuka yake yi yana fa'din" Ban nemi yafiyar ta ba, gashi ta rasu...ya Allah ka yafe min kasa Baby ma ta yafe min, Kaico na, dana kasance mai son zuciya ta, kaico na da na sake har Shai'dan yayi min illah a zuciya ta ya sani aikata abinda zai jani ga dana sani na har abada.
Allah sarki Jasmine, yarinya mai tsananin tausayi da sanyin hali, bazai manta ba ko ranar da abin ya faru da ta ganshi wani iri sosai ta nuna tausayawa agare shi koda ta tambaye shi abinda ya same shi kuwa sai yace mata zazza6i ke damun sa.
Jasmine cikin tausayawa tace" _Sorry kar kayi kuka kaji, idan Daddy na yazo zai baka magani amma kace kar ya maka allura akwai zafi_ ..."
Hawayen sa ya share da 'dayan hannun san mai lafiyan, kana yace" Allah ya ji'kan ki Aishatu, Allah yasa kiyi ceto Allah ya bawa iyayen ki madadin ki...wallahi nayi hasarar rayuwa ta, Yah Allah ka yafe min, ka yafe min Yah Allah...da wani idanu zan dubi Oga Deeni ince masa yayafe min, ga shi nayi sanadin da yarinya ta rasa rayuwar ta...
Kuka yake sosai ahakan Safwan ya shigo ya same shi.
Sosai yayi mamaki da ganin halin da Sani ke ciki..." Innalillahi haba Sani me ke damun ka kuma? Dan Allah ka daina 'daga hankalin ka ciwo ai ba mutuwa bace, kuma tana iya samun kowa, kar kaga kamar Allah bai son ka ne da ya jarrabe ka da hakan, kuma ai dama ba'a gama wa bawa halitta har sai ranar da ransa ya bar jikin sa, duk cikin 'kaddarorin Ubangiji ne kar kace zaka tambaye sa dalili kuma domin shine masanin komai shine yasan mai yasa ya jarrabe ka da hakan...."
Sani bai jira yaji 'karshen maganar Safwan in ba yace"...Dr...ya zanyi? Ya zanyi da rayuwa ta? Ta ya zan iya sakin raina bacin nasan Jasmine bata yafe min abinda nayi mata ba gashi tabar min duniyan, ina zan shiga inji da'di, wallahi ciwon nan baya damu na kamar yadda nake jin ciwon rasa Baby, nasan yanzu haka iyayen ta na cikin wani hali ta ya zan iya zuwa gaban su in ce su yafe min, kunya nake ji soaai Dr...wallahi tir nake yi da halayya ta, har abada nasan da wannan abin za'a yi ta kallo na...ina ma da nine na mutu..ina ma da nine na bar duniyan ba Baby ba....".
" Kar kace haka, yanzu fa na gama gaya ma ba'a yiwa Allah tambaya, ko ka manta kai muslumi ne, duk abinda ya dame ka kawai ka juya ga Allah, in batun Baby ne kuma kawai kayi ta istighfari ka tabbatar kayi tuba na gaskiya, ko da wasa kar ka sake kwatanta irin wancan abin har abada ina da ya'kinin Allah zai yafe maka idan kayi hakan...."
" Nagode, nagode sosai Dr. Insha Allahu zan nemi garafa wajen mahalllici na, zan ro'ke shi ya yafe min..."
Daga haka bai sake furta komai ba kawai ya cigaba da kukan sa.
Safwan tashi yayi ya bar 'dakin yana jin tausayin su a zuciyar sa.
Kafin ya fita sai da yabi ya sake duba Mu'een yaga baccin sa yake yi, cikin zuciyar sa yayi masa fatan Allah ya bashi lafiya kafin ya nufi inda motar sa take ya kama hanyar gidan sa.