← Book details Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 211

Sashe 66

Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A haka suka cigaba da lalla6a karatun su har suka ci semester guda, ba zai ce har a lokacin bai san kowa ba dan kuwa makaranta duk rashin son jama'ar ka dole ne sai ka saba da mutane, to ba laifi ya san mutane musamman wa'danda suke 'daukan lectures tare, amma ba sabo mai 'karfi ke tsakanin su ba dan sai dai a ha'du a gaisa ko kuma idan wani issue ya taso ko kuma wani group discussions haka akan ha'du ayi da shi amma bayaga haka babu komai, baya saka kansa cikin su wai shi yana gudun hayaniya, sannan ko mata ma baya shiga sabgar su, saboda ko ka'dan shi har a lokacin bai ga wacce tayi masa da zasu ha'da ala'ka ba koda ta abota ce, balle aje ga zancen soyayya, wannan kam har yanzu bai ma fara tunanin yi ba, bai ta6a jin koda birgewa wata tayi masa ba, a kullun sai yaga duk babu wata 'ya macen da ta kai masa Nanne a komai, har ji yake tamkar bazai ta6a samun irin ta ba, bai ma sa aransa zai sake yin soyayya ba, dan haka karatun sa kawai ya sa agaba.

🤞🏻 *Toh mabiya labarin NOORUL* *...gani na dawo fatan za'a cigaba da bani ha'din kai....masoya na ina son ku, fata* *na ubangiji Allah ya cika muku birikan ku na alkhairi yasa mu dace da hasken Rahmar sa yayi mana kyakkyawan 'karshe....* *{AMEEN}.*

_Comment_
_Vote_
_Share_

*Salmerh ce*😍

💕 *NOORUL* 💕
      (Haske nah)

By
*Salmerh MD*

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

*Jinjinar ban girma ga...Khady, Amatullah, Nanerh⁩, Khul⁩,* ⁨ *Jamilayusuf1980⁩,Mrs Nafi U⁩, Nusy tee, ⁨Maman*Muhammad⁩, ⁨Nana⁩ and my Besty (Dr.Khausar)*
*Godiya nake 'yan Amana.....Allahu ya biya muku bu'katan ku na Alkhairi...sosai nake yabawa da soyayyar ku...Allah ya bar min ku*😍❤
*{AMEEN}*🙏

*Sister SAFIYYAH A.W ubangiji Allah yasa an fara SAI NA ZAMA JARUMA a sa'a, Allah ubangiji ya baki ikon fa'dakar damu Amin...*

😍 *MARYAM ABDUL muna godiya sosai Allahu ya bar zumunci ya 'kare ha'de zu'katan mu...Allah ya nuna mana 'karshen BIYAYYA lafiya*🙏

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

🅿 *34*

Ko da ya koma gida hutu ma bai yi wasa da  Addu'o'in sa ba,  yana 'ko'karin yi babu laifi, kuma ko al'kawarin da ya 'daukar wa Alhaji Baba ma bai yi watsi da shi ba duk kuwa da cewa basu tare cuz gaba 'daya hutun a Azare ya gama shi bai zo wurin su Alhaji Baba ba har hutun ya 'kare suka koma makaranta ya cigaba da karatun sa.

      Duk kuwa ranar da wani course ya caza masa kai ya du'kufa karatu.. tamkar zautacce zaki ga yana ta sumbatu shika'dai yana fa'din...." Duk fa kece kika sani wannan abin Nanne, kuma sai kika tafi kika barni tun ma ban fara karatun ba..."

Ajiyar zuciya yake sau'kewa sannan ya cigaba da karatun nasa cike da alhini.

Ya kan yawaita sallah musamman tsayuwar dare yana ro'kowa Nanne gafaran mahallici, da kuma fatan Allah yasa mu da muke raye mu cika da kyau da imani.
*AMEEN*

******
    Ni kuwa 6angarena duk abubuwan nan da suka faru abaya ban ta6a sanin cewa kukan mutuwar Nannen mu Yah Deen yake yi ba, har ya tafi kuwa bansani ba kuma haka Ammi ma bata gaya min ba.

Bazan manta ba  kwana biyu bayan tafiyar sa a wancan lokacin, muka ha'du da Ma'u 'kawar Nannen mu da suke hirar Yah Deen tare tun kafin rasuwar ta, lokacin muna hanyar mu ta zuwa makaranta ne ni da su Saif...sai ta tsaida ni da fa'din in jira ta mu 'karasa makarantar tare.

Ban yi gardama na tsaya saboda nasan ba 6ata min lokaci zatayi ba tunda duk muna kan hanya ne kuma itama makarantar zata je, Ma'u babu ruwan ta da fitina da yake nasan halin ta  'kawar Nannen mu ce.

Su Saif kam gaba suka yi suka cigaba a tafiyar su, ganin hakan ya sani shagwa6e murya nace " to kujira mu mana".
Na fa'di ina kallon bayan su.

Saif ne yace dani " ku same mu a hanya kuma idan kika tsaya wasa ko kika 6ata time kukayi latti sai na ha'da ki da Ammi".
Nasan ba fa'dan zaiyi ba dan nasan ba halin Saif bane kaiwan magana,  amma duk da haka sai nace " to ku jirani"
Kafin yayi magana sai Ma'u ta iso kusa dani ta na 'dan haki saboda gudu-gudu sauri-saurin da tayi, cikin hakan ta riga shi magana da fa'din " ba ma sai kun jira ta ba ..." Waigowa tayi gare ni ta kama hannu na gami da fa'din " Muje kawai".
  Tafiya muka fara amma tafiyar ta mu ba irin ta su Zaidu ba ce dan sosai suka fi mu sauri...dan haka sai muka cigaba da bin su abaya.

Can sai Ma'u ta kalle ni tace " Kina tayin kyau abin ki Hudah kamar ba ke ba"!
Murmushin jin da'di nayi har cikin raina naji da'din maganar ta, cikin raina nake ayyana yanda Ammi ke ji dani da sauran mutanen gidan, kafin a siyawa su Saif abu sau 'daya wani sain sai an min sau uku, hakan ma idan an tashi sai a ha'da ayi mana dukan mu...sosai nake jin da'din gidan cuz babu mai tsangwama ta illah Zaidu da sam jinin mu bai ha'du da shi ba.
Muryar Ma'u ne ya yanke min tunanin nawa da najiyo tana fa'din
" Wai ke Hudah baza ki koma gidan ku ba?"
Ina gyara zaman jaka ta nace da ita " Ammi ce ta hana ni".
Baki ta ta6e gefe tare da fa'din "...Na fa ji ana cewa wai dan kwa'dayi kawai kike zama a gidan.."
Turus na ja na tsaya ina yatsina fuska ta nace " Kwa'dayin me zanyi?"
" Oho...ni na sani ne?"
Tayi maganar cikin nuna rashin damuwar ta.
" Sai na fa'dawa Ammi da Ummah ta".
Da sauri tace yi ha'kuri dan Allah ni fa kawai na gaya miki ne dan naji wasu na fa'di ba wai dan ki gayawa kowa ba...kuma yanzu idan kika fa'dawa Ummah ta 'dauke ki a gidan waye zai din ga bani labari?"
Baki kawai na tunzura dan ban san manufar ta kan fa'din hakan ba.

" In tambaye ki wani abu?"
Ta fa'di hakan ne tare da dafa kafa'da ta.
Ban ce da ita komai ba dan haka sai ta cigaba da fa'din " Hudah wai dan Allah dagaske ne Yayan su Zaidu ya dawo, ance min wai an gashi shekaran jiya zai shiga mota"

" Ai har ma ya koma ".
Na bata amsa a takaice.
Zaro idanu Ma'u tayi tace " Dan Allah da gaske har ya tafi?"
Sai na 'dage kaina sama alamar " Erh..."
Sau'kar da murya tayi bayan ta sau'ke ajiyan Zuciya sannan tace " Dan Allah Hudah idan ya sake dawowa ki gaya min kinji..kar ki bari sai ya tafi...sa'kon shi ne a wurina nake so zan bashi".

" To" kawai nace mata tare da 'kara saurin tafiya ta.

Ban 'kara cewa komai ba haka ma Ma'u har muka 'karasa makarantar.

  Ko da muka koma gida kuwa kallo daya Ammi tai min ta fahimci akwai abinda ke damuna..." Zo nan Hudah ke da waye ?...Zaidu kai ne ko?"
Da sauri ya girgiza  mata kai har yana 'dage hannu... " Kaina kan cinyar ta nace " Ma'u ce fa ta ce min wai ina kwa'dayi Ammi..."!

'Bata rai Ammi tayi tace " kwa'dayi a ina kuma na me?"

Kamar zanyi kuka nace " wai anan gidan".
" Ma'un 'yar gidan waye da zata fa'di haka? nifa bana son kinbibi da munafurci, yara 'kanana amma sai tsabar tada fitina.."
'Dago ni tayi zaune tace" idan ta 'kara gaya miki irin haka...ba ita ba ko wani daban...make sure that kin sanar dani har gidan uban ta zanje in same ta sai ta gaya min ko gidan nan 'din na ubanta ne da zata ce kina kwa'dayi...".

Ammi kam ta jima tana masifa akan hakan ga dukkan alamu abin yaci mata rai sosai, hatta su Saif ma sai da suka samu rabon su dan cewa tayi wai me yasa basu 'dau mataki ba.

Zaidu shiru yayi yayin da Saif yace " Mu fa Ammi bamu ma san anyi haka ba, kuma itama bata gaya mana ba".

" Ni dai na gaya muku, daga yau ko da wasa wani ya kuma fa'din hakan...ku sanar dani sai naji dalili ".

    *****
        Wasa-wasa lokaci na tafiya rayuwa na 'kara yin gaba, har Yah Deen ya ci kusan rabin semester 'din sa na biyu.

Tun komawar sa makaranta da sati uku aka yiwa Uncle Ja'afar transfer wurin aikin sa daga Azare Bauchi zuwa can Taraba State....ba tare da 6ata lokaci ba suka tattara da Anty Zainab suka tafi bayan sunje har makarantar sukayi masa sallama bayan haka sannan sukaje suka yiwa su Alhaji Baba ma.

     Mu'een bai damu sosai ba da yake baya gida a lokocin dan haka ya cigaba da karatun sa batare da wata damuwa ba har 'karshen semester.

    Sai lokacin da ya dawo hutu ne kafin yaji babu da'di, kewar su ta dame shi sosai....gashi Uncle Ja'afar ma ya 'kira shi yace da shi ya wuce gida kawai kar yace zai zauna shi ka'dai a gida daya ke yasan kadan ga aiki sane yace a gidan zaiyi hutun.

Kwanan sa uku sannan haka badan ya so ba ya tattara ya wuce garin iyayen na sa.

  Sai dai Yah Deen 'kin zama yayi agidan wai mu bama ji zamu dame shi da hayaniya.

Wani gida da Alhaji Baba ya ta6a ginawa acan wajen hanyar  makarantar mu yace zai koma inda Alhaji Baba yaso nuna 'kin amincewar sa amma Ammi ta ro'ki ya 'kyale shi kawai tunda hakan yayi ra'ayi.

Ita kanta tasan ba dai-dai bane hakan amma dan kawai kar su 6ata ran sa ko kuma yaga kamar an 'ki yi masa abinda yake so ya sanya ta amince....amma Alhaji Baba kam sam hankalin sa  bai kwanta da hakan ba, ta ya shi da yake matashin saurayi zai koma zama shi ka'dai acan bacin ga gidan mahaifin sa, ai rayuwar makaranta daban take da na gida...abin ma sam bai masa tsari ba.
Chapter 66 · 0% Book details