Sashe 166
Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Safwan ne yayiwa Mummy jagora har zuwa 'dakin da suke, sosai ta tausayawa baby ganin halin da take ciki tare da fatan Allah ya basu lafiya gaba 'dayan su, koda ta nemi duba Sani driver sai akace mata ai shirin shiga thearter room ake yi da shi sai dai in sun fito, sosai Mummy ta tausayawa lamarin nan ta zauna suna 'dan ta6a hira da Noor.
Koda wasa kuwa bata yi gigin sanar da ita gaskiyan lamarin ba tunda tasan babu maganin da fa'dan zai yi mata.
Mu'een kam kwantar da kujera yayi ya mi'ke ganin kamar hakan zaifi masa, jira kawai yake yi wa'adin sa ya cika, dan gani yake tamkar ba shi da wani amfani yanzu, so ma yake mutuwa ta riske shi kafin ha'duwar sa da mahaifan sa cuz ya san 'kwayar zarra na sassauci ba zai samu daga wurin su ba, kwatankwacin tsanar da yayiwa kansa haka yake tsanar Jiddah ma, domin itama.ta bada babban gudunmawa wurin tunzira zuciyar sa Nureen sa.
'Kirjin sa ya dafe a hankali ya fara tariyo tun farkon ha'duwar sa da Jiddah....
_Comment_
_Share_
_Vote_
*Salmerh ce* 😍
💕 *NOORUL* 💕
(Haske nah)
By
*Salmerh MD*
*Wattpad @*
*Serlmerh-md*
💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*
_*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_
*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*
🅿 *77*
Wata shida kenan yanzu da fara aikin sa a Abuja amma tun ranar zuwan sa na farko 'kaddara ta ha'da shi da Jiddah, motocin su ne suka yi sanadin ala'kar su.
Tafe yake yana 'dan hanzari ya isa inda ke gaban sa yayin da ita kuma ta taho da zafin kanta na 'yan matan ci ta wani 'kwama tabarau a fuskan ta kana ganin ta kallon farko zaka san cewa sosai Naira ta zauna a jikin ta ga kuma wani ji da kai cikin yanayin ta.
Cikin rashin sani ya gogi jikin motar ta a kan Junction da zai shigar da shi cikin unguwa while ita kuma tana fitowa.
Nan take kuwa ta fito cike da masifa tana wani huhhura hanci ta tunkaro shi, saurin dakatar da ita yayi da fa'din" kiyi ha'kuri please kuskure ne".
Yayi hakan ne dan ya gaji a lokacin sam baya san gajiya ga shi ga dukkan alamu kuma ba ha'kuri ne yarinyar ba, ba ya so abin yayi tsayi sam.
Harara ta banka masa sannan ta juya cikin takun ta na isa ga kuma 'daukan hankali tana tafe take mitan" Mutane sai su dinga abu kamar basu da idanu..."
Baiji mai tace ba dan shi daga cikin motar yake bai fito ba amma duk da hakan bai sha wahalar fahimtar 'kananun mitan da take yi ba.
Sai da ya bi bayan ta da kallo sama har 'kasa ya ta6e baki kafin ya juya gami da mi'ka hannun sa ya ciro wasu ku'da'de dai-dai tana shirin bu'de nata motan ta shiga yace" Baki ji ba...".
Waigowa tayi ta dube shi hannun sa 'daya na kan stairy shima ya zuba mata lumsassun idanun sa sannan yace" Idan da matsalar babba ce ga wannan Please ki kai a duba miki motar..."
Yayi maganan tare da mi'ka mata ku'din da ke hannun sa wanda zasu kai kimanin 20k.
Fasa bu'de motan tayi ta zuba mishi idanu harda har'de hannuwa a 'kirji zuciyar ta cike da takaicin wannan rainin hankalin, gani tayi kamar tunda take ba'a ta6a ci mata mutunci irin wannan ba, sai ta rasa me yake ji da shi da har yake tunanin ita Jiddah zata ansa ku'din hannun sa saboda wannan dalilin.
Tana daga tsayen bata ko motsa ba illa 'kan'kance idanu da tayi, kwata-kwata ma bata san ma amsar da ya kamata ta bashi a zahiri ba.
Da kansa ya fahimci ya bata haushi musamman yanda yaga ta tsaya tana yi masa kallon _ka rena min hankali_...gira ya 'dan 'dage sama tare da duban hanya yace" Ga dukkan alamu baki bu'kata...ko? Anyway kiyi maza ki bar kan hanya ni sauri nake yi akwai abubuwa agaba na".
Yayi maganar yana maida ku'din sa inda ya ciro su tare da yiwa motar sa key yaja yayi gaba abin sa batare da ya ko sake duban inda take ba.
Jiddah kam binsa tayi da idanu har yayi nisa sosai ya 6acewa ganin ta, cikin ranta ta ayyana" Ni kuma ga maras abin yi mana dan ka raina min hankali.."
Sosai ya 'kunsa mata ba'kin ciki cikin zuciyar ta, yayin da a wani 6angaren kuma taji ya matu'kar birge ta sosai ya tafi da imanin ta...haka itama taja motar ta tama fasa fitan kawai ta koma gida.
Lokaci zuwa lokaci take sakin tsaki da 'kyar ta samu ta manta da lamarin cikin ranta.
Ha'duwan su na biyu a shopping mall suka ha'du, wanda ya kasance kwanaki takwas bayan ha'duwar su na farko, itace ta fara gane shi ai kuwa sai ta matsa kusa da shi ta tari gaban sa.
Idanu ya waro yana duban ta da mamaki sam ya kasa yuno inda ya santa but her face looks familiar to him.
Murmushi tayi sannan ta tace" Seems like baka gane ni ba".
Kansa ya girgiza mata alamar " Yes".
Sai tace" Last week mun ha'du a junction...".bata 'karasa ba yayi murmushi tare da fa'din" Awwn..waccen mai masifan ko?".
Murmushi ta sake yi masa sannan suka gaisa tamkar sun san juna, tare suka zagaya suka yi shopping 'din su yazo ya biya suka fito, kafin su rabu sai da suka yi exchanging number shikenan tun daga ranar suka 'kulla abota.
Ta kan yawaita 'kiran sa taji lafiyar sa haka shima tun ba ya tuna 'kiran ta har ya fara 'kiran ta da kansa suna gaisawa.
Sau tari ta kanje har asbitin da yake aiki musamman saboda ta ziyar ce shi, amma Mu'een bai ta6a zuwa gidan su ba, bai ta6a binta wani wuri dan kawai gana ba...in kuwa ya taho Bauchi hankalin ta sam baya kwanciya ta ringa damun sa da 'kira kenan tana tambayar yaushe zai dawo.
Wasu lokutan har haushin ta ke kama shi amma baya nuna mata, sau tari idan ta 'kira shi sanda yake gida sharewa yake yi sai ya bari idan ya fita masallaci ya tsaya yayi 'kiran ta...baya ta6a yadda yayi waya da mace cikin gidan sa matu'kar yana Bauchi.
Wasa-wasa abu makamanciyar soyayya ta fara 'kulluwa tsakanin su, sai ya zama na ma Jiddah har gidan sa take zuwa masa ziyara batare da wata damuwa ba.
Takan yawaita zuwa masa musamman a weekend ko kuma idan ya tashi daga aiki har girki tana yi masa watarana sai tace yau ya huta bazai yi take away ba.
Shi kam bai damu ba idan tayi cin abincin sa yake yi ya bishi da ruwa.
Ya kan lura da ita idan yana yin waya da iyalin sa fuskar ta na 'dan canzawa, bai ta6a furta mata kalmar so ba shiyasa shima baya sa fushin nata aka duk kuwa da cewa ya gama fahimtar inda ta dosa amma shi matsayin abota ya ajiye ta har a lokacin bai canza ba.
Sakewan da tayi da shi ya sa bata ko shayin yin wasu abubuwan agaban sa, da yake ma bai ta6a bayyana mata asalin waye shi ba, shiyasa bata san halin sa ba bata san cewa yanda ta saki jiki da shi 'din ya fara canza masa tunani akanta ba.
Musamman ranar duk da tazo har tayi masa girki kafin ta bar gidan sai ta watsa ruwa, sannan ta sake shiryawa ta tafi.
Sosai yayi 'ko'karin kawar da zuciyan sa agare ta amma ya kasa, shai'dan ya riga ya mamayi zuciyar sa tunda da da'dewa, to wanda ma basu saki jiki da shi ba yana iya neman su balle wacce ta kawo.kanta har muhallin sa...ni dai nace Allah ya kyauta.
Jiddah bata ta6a sanin kuksure take aikatawa ba sai watara rana da tazo tayi masa girki, girkin ma mai sau'ki tayi cuous-cous ne da sauce 'din kifi, yayi yayi da ita ma akan ta huta abinta kar tayi amma ta dage tace sai da tayi...a fa'dan ta wai tausayin sa take ji ai tasan bai ci komai ba cuz ranar tasowan sa daga aiki kenan shine tazo.
Ai kuwa ta shiga wanka ta fito tana 'daure da towel a jikin ta ta zauna gyara make-up 'din ta bata ankara ba kawai sai ganin shi tayi ya shigo yana binta da mayatattun idanun sa idanun sa masa rikita zuciyar mai rauni.
Wani shu'umin kallo yake binta da shi wanda yasa ita da kanta ta fahimci cewa ba lafiya yake ba, take ta rikice jikin ta ya fara rawa bayan fahimtar dalilin kallon nasa tasan bai wuci dan ya ganta cikin wannan yanayin bane tunda tasan bai taba shigo mata a irin wannan yanayin ba, bama ya ta6a kallon ta a hakan ba sai yau, domin kullun idan zatayi shirin ta a palour yake zama kuma baya shigowa har ta kammala ta fita, yau 'din ma bata san mai ya shigo da shi ba.
Barin kwalliyar tayi ta taho da sauri da niyyar 'diban kayan ta ta sitirce jikin ta amma ga mamakin ta sai taji shi a bayan ta har tana iya jiyo hucin numfashin sa kusa da ita.
Kafin tayi wani yun'kuri har ya kamo waist 'din ta ya matsa kusa da ita tare da juyo da ita ta fuskance shi.
Jikin Jiddah rawa ya fara take ta fara 'ko'karin jan jikin ta daga nashi dan sosai ta rikice da yanayin nasa a lokacin amma sai ya 'ki sakin ta.
Tana shirin yi masa magana yayi saurin dakatar da ita ta hanyar sau'ke bakin sa saman nata ya fara kissing 'din ta kamar ta sa shi...dole hakan ya tilasta mata yin shiru illah mutsu-mutsu da take yi amma ta kasa 'kwatan kanta dan ya riga ya kewaye ta da hannayen sa biyu.
Tunda take a rayuwar ta babu wanda ya ta6a ko kwatanta yi mata irin hakan ko da wasa..shiyasa lokaci guda tsoro ya mamayi zuciyar ta ta fara hawaye tana tsoron mai kuma yau Allah ya ha'da ta da shi.