Sashe 175
Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Dole tasa Safwan ya aika aka kawo masa Coffee 'din dan ya lura Mu'een taurin kai ne da shi da kafiya, yanayin abinsa kamar Noor, itama haka bata jin magana wani lokacin, wanda duk bai san hakan ba sai yanzu da zama ya ha'da su a asbiti yasa ya 'dan fahimci wasu halayyan ta, sosai take da taurin kai irin na Mu'een, gashi ba ta jin lallami idan ranta ya 6aci.
Cikin sa'a kuma ma ba'a jima ba sai gashi an kawo masa kafin hakan kuwa 'karasar da jerin sallolin dake kasan yayi.
Sai da ya idar kafin Saif ya gabatar masa da Coffee 'din ya kar6a ya sha abin sa cikin kwanciyar hankali, banda 'yar rama da yayi babu abinda zaka gani ajikin sa kace shine marar lafiyan..domin ya 'dan warware.
A hankali yake sipping yana tunanin halin da iyalan sa ke ciki, Saif kam ba 'karamin farin ciki yayi da farkawar 'dan uwan nasa ba sai dai ta wani 6angaren tausayin sa yake ji matu'ka, yasan jin labarin mutuwar Baby shine zai zame masa wani babban illar kuma idan ba ayi sa'a ba...gashi Safwan ya garga'de shi da cewa kar ya sanar da shi tun yanzu su bari tukunna sai ya 'kara samun natsuwa.
Yana cikin sipping Coffee 'din ya dubi Safwan yace" Ya jikin Baby ne..Allah yasa dai ta warware yanzu...".
Shiru Safwan yayi yama rasa ta inda zai fara yi masa bayani.
Saif kam 'kasa yayi da idanun sa kafin Safwan yayi magana kuma sai ga su Ishaq sun shigo da sallamar su.
Cikin natsuwa duk yake duban su, har cikin ransa ya ji da'din zuwan su.
Yayin da suma sukai matu'kar farin ciki da ganin sa a zaune cus jiya bayan isowan su sun zo amma a lokacin bai tashi ba sai gashi kuma yanzu cikin sa'a yana zaune had da cup a hannun sa da alamu jiki yayi sau'ki.
Hannu suka zo suka bashi suna yi masa ya jiki tare da gaisawa da Safwan.
Deen yana murmushi yace" Lalle Maman Daddy 'yar gata ce, kardai duk saboda duba jikin Baby kawai kuka zo all the way from Borno State?..".
Murmushi Ishaq yayi tare da zama gefen sa yana cire hular kansa.
Ganin yana shirin zama ne ya sanya Yah Deen saurin fa'din" A a ku tashi muje Please nima nan da kuke gani ba 'karamin 'kaguwa nayi da ganin su ba...".
Hakan da ya fa'da ne ya sanya Ishaq saurin fahimtar cewa har yanzun bai san halin da ake ciki ba kenan...
Fuskar sa ya kalla sannan yace" Kar ka damu ai zamu...amma gama cin abincin naka tukunna".
Yamutsa fuska Deen yayi yana fa'din" Ai na gama..ya ishe ni fa dama, tun 'dazun su Saif ke 'duramin madara kamar wani 'karamin yaro..."
Yayi maganar yana murmushi tare da ajiye cup in hannun sa a gefen sa.
Maganin sa Safwan ya 6allo ya bashi inda shi kuma yana murmushin yace" Safwan sarkin dubara so dai kake sai na 'kara sha kenan..?".
Da haka ya kar6i maganin ya sa abaki sannan yabi bayan sa da Coffee 'din, dire cup 'din yayi yana sau'ke ajiyan zuciya...yana duban hannun sa inda aka 'daura masa canular ya shafa a hankali cuz 'kai'kayi wurin ke masa.
Yun'kuri yayi yana shirin mi'kewa amma sai Ishaq ya dakatar da shi...da fa'din" Magana fa nazo muyi da kai".
Koma wa yayi ya zauna yana fa'din" Okay ka hanzar ta, na 'kagu inga iyali na..".
Cikin ransa ya ayyana ba mamaki shima yaji labarin abinda ya faru ne, nasan kowa ma tsana ta zai yi yanzu".
Nasiha Ishaq ya fara yi masa cikin natsuwa har ya gangaro kan batun rasuwar Baby...Yah Deen kam tsura masa idanu yayi ganin kamar da gaske yake yi bada wasa ba ya sanya Yah Deen juyawa ya ringa binsu da kallo 'daya bayan 'daya.
Kansa yaji yana juya masa sai ya lumshe idanu" Ishaq kasan bama irin wannan wasan da kai ko?"
" Ana wasa da mutuwa ne Mu'een?"
Imam ya bashi amsar tambayar sa da wata tambayar.
Bai damu ba da wata raunanniyar murya yana dafe da kansa yace" Safwan dagaske Jasmine ta rasu? Dagaske Baby ta tafi ta barni?"
Safwan matsowa yayi daf dashi dan yayi masa bayani cikin natsuwa yace" Jasmine ta rasu Mu'een, tun ranar da su Ammi suka zo bata 'kara kwana da rai ba, idan baka manta ba ranar shine kaima aka kwantar da kai anan 2days kenan yanzu...".
Jajayen idanun sa ya bu'de ya sau'ke su kan fuskar Safwan yayin da ya cigaba da fa'din" ha'kuri zaka yi Mu'een ha'ki'ka rasa Jasmine babban rashi ne mai ta6a zuciya amma babu wani abinda zamu iya aikatawa tunda muma 'din duk shi muke jira..."
A fizge ya furta Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un...kansa ya fara girgizawa a hankali da sanyin murya yace" Ishaq...Nuree fa wani hali take ciki? Ku tashi ku kaini gida please..zan je in duba ta, nasan hankalin ta tashe yake sosai yanzu, kuma ina so in ro'ki Ammi ta yafe min Alhaji ma yayi fushi da ni..yace babu shi babu ni.."
Kuka Saif ya fara a hankali dama yasan dole akwai wani abin tsakanin sa da mahaifin su, Yah Deen duban sa yayi da riannanun idanun sa yace" Saif dagaske ne Jasmine ta rasu..?"
Bai iya ya bashi amsa ba dan kuka da yaci 'karfin sa.
Yayin da Yah Deen ya maida idanun sa ya rufe..ko ina jikin sa ji yayai yana masa gudu, yayin da bugun zuciyar sa ya tsananta ya sosai...amma duk da hakan fa'di yake su kaishi wurin ahalin sa, yana so yaga iyalan sa.
Basu yadda sun tafi ba har sai da liktan sa ya basu dama domin yace ciwon nasa tashi yake yi idan ya riga ya sau'ka kuma shikenan dan haka discharging nasu yayi ya 'kara da fa'din idan akwai wata matsala suyi saurin tuntu6ar sa.
Godiya suka yi tare da kamo hanyar gida dukkan su hadda Safwan dan shima tun lokacin da aka kwantar da Jasmine har zuwa yau 'din bai huta ba.
Cikin motar yake gayawa Ishaq cewa" Nuree tace wai har abada bazata yafe masa ba, ka taimake ni Ishaq wallahi bazan iya rayuwa babu ita ba..itace farin ciki na bana so in rasa ta kamar yadda na rasa Baby Ishaq".
"Kar ka 'daga hankalin ka please Mu'een, Noor mai ha'kuri ce na tabbata zata yafe maka duk abinda kayi mata Insha Allahu".
Abinda kawai Ishaq yace kenan har suka isa gida, yayin da Saif ke share hawaye a 6oye, tausayin 'dan uwan sa yake ji sosai...aganin sa abubuwan sun yi masa yawa ma.
Da isar su 'kofan gidan nasa sai jikin sa yayi sanyi 'kalau bai iya ya sake furta komai ba har suka fiffito daga motan, a hankali ya ringa bin mutanen dake zaune da idanu, hadda abokin Uncle Ja'afar ya gani a wurin zaune wanda ya bashi aiki anan asbitin da ya bari a bauchi, Babban mutun ne mai fa'da aji amma gashi zaune 'kofar gifan sa tare da mahaifin sa wurin kar6an gaisuwar 'yar sa Jasmine, da 'kyar yake 'daga 'kafafun sa amma ya daure suka 'karasa wurin jama'ar, da yawa sun yi farin ciki da ganin ya taho da 'kafafun sa domin duk sun san halin da yake ciki a gadon asbitin...cuz Safwan na kawo musu labarin halin da ake ciki dan su kwantar da hankalin su.
Kowa gaisuwa ya ringa mi'ka masa yayin da shima ya mi'ka gaisuwa ga manyan sa su Alhaji da sauran su, Alhaji Baba a takaice ya amsa masa gaisuwar batare da yako nuna kulawa ba, shi da kansa ya sani shi mai laifi ne a wurin Alhajin dan haka bai damu ba, so yake su ke6e ya samu daman da zai 'kara neman afuwar su.
Bai samu ya shiga cikin gida ba sai da yamma lis wannan ma Safwan ne ya matsa masa akan su shiga ya watsa ruwa ya canza kaya, haka ya shiga ya watsa ya canza wasu kayan sannan ya fito suka yi sallar maghrib da Isha'i...fuksar sa fayau jin kansa yake yi kamar bashi ba, sam baya jin wani nauyi tattare da jikin sa, illah 'kafafun sa dake yi mai nauyi.
Cikin gida suka koma wanda sai a lokacin ya shiga ya gaida su Ammi, itama 'din babu yabo babu fallasa ta amsa shi, haka ma Nuree, abin kuma sai ya fara sashi yana jin wani iri, me yasa bazasu tausaya masa ba ko dan rasa Baby da yayi? Antyn sa Zainab ita ka'dai ce ta amsa masa gaisuwa da tausa sashshiyar murya har ta 'kara da kwanatr masa da hankali... haka ya tashi sum-sum ya fita yana jin babu da'di cikin ransa, itama Anty Zainab in may be da tasan halin da ake ciki yasan da 'kyar ne idan zata kula shi..
Wahshegari akayi sadakan uku da bakwai aranar kuma Alhaji Baba suka koma gida shi da wa'danda suka zo daga Shuwarin gaisuwa..wanda kafin tafiyar sa sai da ya bawa Ammi umarnin ta tafi masa da 'yar sa bai amince Noor ta 'kara ko da kwana guda ba ne tare yake so su koma gida.
Ammi jinjina kai kawai tayi bata sanar da kowa batun Alhajin ba kawai ta ri'ke cikin ranta, dama ko be fa'da ba bata da niyyan sake barin Noor zama tare da Deen yanzu.
Duk mazan sun tafi Illah 'yan biyun Ammi suka rage.
Gidan sai ya zama daga ni, Ammi, Anty Zainab, Ummah ta sai Addah Maryam da suka daga baya.