← Book details Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 129 OF 211

Sashe 129

Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya so ya ban ha'kuri kan maganar can amma sam baya so ya sake tunowa da shi, shi kansa yanzu haushin kansa yake ji da ya sa Husnah tazo har gidan sa a 'dakin matar sa yayi fasi'kanci da ita...da kansa ya zauna yayi tunani tare da kwatanta abin cikin ransa, ya 'kiyasta yanda yaji ranar da su Imrana suka zo da niyyar ya basu kyautan matar sa kamar yanda yayi musu al'kawari, duk da bai ji cewa hqr cikin zuciayr sa yana son Noor ba amma yanda yaji lokacin ya san da hakan zai faru dagaske da mutuwa ce ka'dai bazai yi ba, 'kilan ma mutuwar ta iya riskar sa saboda ba'kin ciki bai sani ba kuma ko dan saboda Noor ne yaji hakan ba, bai sani ba ko har akan Husnah zai ji hakan....idan hakane kuwa dole Noor ma zata ji ciwon ganin sa gani mafi muni yana aikata zina a gidan da yake na auren ta ne, cikin 'dakin ta da wata macen daban,  duk da 'karancin shekarun ta amma yasan dole zata ji ciwo cuz shi kishi bai san 'kan'kanta ba...dan yanayin tan alamun kishi 'karara ne ya bayyana tattare da ita.

Cikin zuciyar sa yayi al'kawari insha Allahu bazai sake neman Husnah ba, bazai sake cin mutnucin auren ta ba, wanda yayi abaya ma yana fatan ubangiji Allah ya yafe masa, daya je kuma zai nemi gafarar ta cuz shivya tilastata zuwa da barazanar zai tona ta wurin mahaifiyar ta, yana jin Husnah navkuka tana ro'kan sa akan yayi ha'kuri ya bar ta ta fuskanci ubangijin ta amma yayi biris ya kashe wayar sa, dole hakan ya tilasta ta sake 'kiran shi ta tambaye shi cewa matar sa fa dacyake tana da labarin an 'daura masa aure shima...sai yace kar ta damu babu komai yarinya ce matar gidan.
Cewa ta sake yi kar a ganta kuma a sake zuwa a sanar da iyayen sa..amsar da ya bata shine wanda Hudah taji ranar da ta farka a bacci...idan ya tuna wannan abin ya kan sake jin haushin kansa da kansa akoda yaushe.

Ba zai gaya wa Noor a zahiri ba amma insha Allahu saboda ita zai yi 'ko'karin ganin ya kame kansa daga aikata abinda yake yi.

Cuz idan har wannan yarinyar ta iya ganin abu makamanci wannan kuma ta iya 6oye wa yasan shima barin zina abu ne mai sau'ki a wurin sa...wannan abin ka'dai da ta aikata ya ja mata wani babban matsayi cikin zuciyar sa da shi kansa bazai iya misaltawa ba.

Bakin sa na son furta _kiyafe min_ amma harshen sa sai yayi masa nauyi wurin furta shi, sai ma yake jin gaba 'daya Noor 'din tayi masa kwarjini a idanun sa.

Tsaye ya mi'ke da niyyar tafiya...bai kuma niyyan sake furta komai ba, nima ban ko yi motsin kirki daga inda nake ba har ya isa bakin 'kofa zai bu'de sai a sannan nace da shi" Ammi tace in tambaye ka kayi min izni inje gida".
Take ya waigo yana fa'din
" Wani gida kuma?"
Inda yayi tambayar yana kallon bayana dan ko juyowa banyi ba, shi kansa yana mamakin wai 6eran yarinyar nan ce ke yi masa irin wannan abin...hmmm Allah mai sanadi...sai yayi 'dan ta'kaitaccen murmushi.

Amsa na bashi da fa'din" Gidan mu zani da wurin dangi na".

Wannan karan murmushin mai sauti yayi jin yanayin maganar tawa kamar da gaba....
Sai da ya juya yana bu'de 'kofan kafin yace" Toh ki je mana sai kin tamabaye ni ne?"

Shiru nayi ban ce masa komai ba...har ya sa kai zai fita kuma sai dakata sannan yace" Amma fa family kawai na miki izni ki ziyarta ban yarda da shiga ko'ina ba".

Ko yanzun ma shiru nayi sai dai bai damu ba cuz yasan sarai na jishi.. daga haka kuma ya fita daga 'dakin yana fa'din"  Sai da safe"...cuz daga masallaci wai bazai dawo gidan ba saboda yau 'din bai jin cin dinner shiyasa.

Comment
Vote
Share

*Salmerh ce* 😍

💕 *NOORUL* 💕
      (Haske nah)

By
*Salmerh MD*

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

🕌🌙 ~RAMADAN MUBARAKH~ 🕌🌙

_*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

🅿 *62*

Washe gari kuwa da safe ya koma Jigawa, wanda kafin tafiyar tasa sai da yazo gidan Ammi ya musu sallama ni kuma ya ciro ku'di ya ban masan nawa bane ya ajiye min yayi tafiyar sa, daga" na tafi" babu abinda ya sake ha'da ni da shi, kuma ko da yace ya min hakn ma baki n ta6e ban furta masa komai ba illah harara da na bi ku'din nasa da shi.

Ban ko saka 'dan yatsana na ta6a ku'din.ba na bar su nan inda ya ajiye su na cigaba da harkoki na.

Sai bayan tafiyar sane ne ma da 'dan jimawa kafin Ammi tazo ta ga ku'din da kanta sannan tactambaye ni sai nace mata" Yayah ne ya ajiye".
Ammi da ku'din a hannun ta tace
" Shine kuma kika bar su nan?" Inda tayi maganar tana kallo na.
'Dan marairaicecfuska nayi nace
" Ammi to ni ina zan kaisu? shine fa da kansa ya ajiye a wurin".

"Da ya ajiye 'din ce miki yayi ki ta kallon su ko kuma ki barshi a nan, i thought ke ya ajiye ko?"
A hankali nace" Ammi to ki ri'ke a gunki".

Kai ta girgiza kawai ta tafi ta bar ni a wurin.

  Nima ban jima ba bayan hakan na gama shiri na dan zuwa gidan mu wurin Ummah ta...lokacin da zan tafi Ammi sai ta ce in tafi da ku'din zan yi magana ta hanani...dole ta 'dauko tasamin cikin jakata tare da ha'da ni da tsaraba tace in kai wa Ummah ta.

Ranar Allah ka'dai ya san irin farin cikin da nake ciki musamman da naga Ummah ta...'kin zuwa ko'ina nayi saboda so nake na 'dan kwana biyu agidan Ummah ban san komawa can gidan a yau 'din.

Sosai naji da'din zuwa gidan kuwa inda nan take na sake cikin gidan mu walwalata duk tacdawo sabuwa har ma 'dan manta damuwar da ke ci na arai.

Ammi data ga dare yayi sai ta 'kira Umman mu awaya bayan sun gaisa tace ta ha'da mu...nan nayi mata bayanin ba yau zan dawo ba...Ammi bata damu ba haka bata ce dani komai ba illa sai da safe kawai da tai min.

Nan na sake sakan jiki na a gidan ganin Ammi bata hana ni ba.

Ko Ummah ta ma da na bata ku'din 'kin kar6a tayi abin sai ya bani haushi sosai, sai da ta ga na fara hawaye kafin ta kar6i 5k ta bar min 15k wai in ajiye a wuri na...nace mata Ammi ce fa tace in zo da shi..ni me ma zanyi da ku'din to?"

Ummah ta yi tayi tamkar bata jini ba, kukan da taga na dage da yi ne ma yasa ta ciran 5k 'din wanda ni kuwa kukan nawa har da tunowa da sirrin da na 6oyewa zuciya ta wanda ganin ku'din da ya bani da kansa a hannu na ne ya sani tunowa da shi da halayyar sa..ha'kika wani lokacin furta abu ma yakan sa ya yi ma sau'ki a zuciya yayin da ri'ke abu sam baida wani amfani inba yazama dole ba, nasan da ace na samu wanda zamu tattauna batun da shi na fahimta da zanji sau'ki cikin raina amma bazan ta6a iya yin hirar ga kowa ba, ciki kuwa harda mahaifiya ta...yanzu kam na fahimci akwai sirrin da 6oye shi ya fiye wa kowa alkhairi fiye da furta shi, balle ma ni da ya kasance sirrin mijina ne, ban manta garga'din da akayi min kan ri'ke sirri ba...nasan zan iya ri'ke shi har abada duk da na san bazan iya manta shi cikin raina ba.

Na bari dai akan sanin da nayi cewa rufin asiri ga wani tamkar ka rufa naka asirin ne...al'kawari 'daya da na 'daukan ma kaina game da Yah Deen shine zan nayi masa addu'ah ubangiji Allah ya shiryar da shi Allah yasa ya gane hakan da yake aikatawa babban laifi ne a wurin Ubangiji.

Sai washegeri muka je gidan su Addah ta saudah ni da Ummie, har  gidan Yaya Usman da sauran 'yan uwan mu dake kusa duk munje yayin da wasu daga cikin su ke min zolayar wai har na canza amarcin ya kar6e ni, ni dai kawai sai dai inyi murmushi cuz' ni ka 'dai na san damuwa zuciya ta.

Kamar yadda ya umarceni kuwa banje gidan kowa da yakansace ba ahali na ba, duk iya ziyarar da nayi ban 'ketare maganar sa ba, daga nan kuwa na dawo gidan Umma ta.

Kowa ya ganni sukan ce kyauna ya 'karu haka shiru-shiru na ma, hatta ma'kwabtan gidan mu sai da suka yabi tsari na...ni kam murmushi kawai nake yi ban bada amsar komai.

A duk lokaciin da na ke6e na a mafiya yawan lokauta na kan tsinci kaina ian mai zubda hawaye wanda duk baya rasa nasaba da Yah Deen, sam ban san dalilin damuwa ta akan rayuwar da na ga yake yi ba, kuma nayi-nayi in manta da lamarin amma na kasa a kullum yana nan sabo cikin zuciya ta.

Ban ta6a bari kuma Ummahn mu ta fahimci halin da nake ciki ba, sosai nayi 'ko'kari wajen 6oye mata, ni da kaina nasan nayi wannan 'ko'karin ko da wani bai fa'da ba.

Kwana na biyu sannan na koma gidan Ammi na cigaba da zama na,  hankali na a 'dan kwance saboda ko waya bama yi da shi, ina dai gaisawa da su Saif akai akai amma shi kam ban da shi, sai dai inji suna waya da Ammi lokuta da dama ina gefen ta amma ban ta6a ji ya ko gwada ambatan sunana ba balle yace a bani wayar.

'Bangarena nima hakn yafi min da'di dan idan akec zan yi magana da shi nasan kuka ne kawai zai rinjaye ni bazan iya maganar ba...in kuwa hakan yacfaru nasan zuciyar Ammi zai cika ne da tarin tambayoyi.

Ashe Ammi ma da kanta hakan da yake yi 'din na bata haushi, kawai ta 'kyale shi ne dan tana so taga iya gudun ruwan sa akaina.
Chapter 129 · 0% Book details