← Book details Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 200 OF 211

Sashe 200

Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ita kam da kanta bata sanar da shi komai game da ita ba, bazata manta ba ranar yazo gidan su while ta tafi school Anty ce ka'dai a gida nan tayi masa iso suka zauna a parlour suka gaisa ya sanar da ita cewa shi ne me son Noor amma ta'ki bashi ha'din kai har yanzu.

Anty bata yi mamaki ba dan tasan dama Noor bata bawa kowa hankalin ta, nan ta fara yi masa bayanin wace Noor da kuma dalilin da yasa bata son kula kowa, Anty kam ma nuna masa tayi kamar har yanzun son Mu'een ke hanata kula wasu.

kuma tayi hakan ne dan bata son shima 'din ya cigaba da ra6ar Noor tafi son ta komawa Deen su 'karashe rayuwar tare, dan Anty Zainab tasha kamata tana kuka idan ta tambaye ta dalilin kukan kuma ta kance da ita bakomai wani sa'in bathroom take shigewa ta sha kukan ta son ranta sannan ta fito duk Anty Zee ta san hakan amma bata ta6a tanka mata ba..kuma ta fahimci duk akan rabuwar ta da mijin ta ne, daga baya ma sai ta daina bari Anty na ganin alamun kukan tattare da ita.
...A tunanin Anty ko idan Hakeem yaji cewa Noor 'din ta ta6a aure har da 'ya ko zai janye ne.

Amma ga mamakin ta Hakeem kam sai ma 'kara bada himma da yayi, gashi da 'dan banzan surutun da ko bakayi niyyan tanka shi ba ma dolen kane matu'kar kun zauna da shi.

Hakan yasa ya shiga jikin Noor sosai tun ma bata sakin jiki har zo ta saki jiki da shi, hatta sunan sa dake wayar ta ma da kansa yayi saving kayan sa, a yanzu idan tace bata 'kaunar sa to kuwa tayi 'karya sai dai har yanzun bai ko taka 'kafar 'kaunar da ta yiwa Yah Deen abaya ba.

*****
Lokacin da zazza6in ya sake shi ya fahimci cewa Anty Zainab tazo hankalin sa kasuwa yayi kashi-kashi, burin sa yaga Noor in sa tazo inda yake amma shiru, shi kuma bai tambayi kowa game da ita ba dan shi yanzu abu mai yi masa wahala shine magana, ya tsana sam.

Ko motsi yaji zaki ga ya dubi wurin da sauri da tunanin ko zai ganta, yana ji cikin ransa cewar wannan karon me raba shi da Noor koma waye shi to babban ma'kiyin sa ne.

Itama Antyn har yanzu bata ga wani sakin fuskar sa ba, dan ya sanya cikin zuciyar sa cewa itace ta raba shi da Noor 'din sa ta janye ta daga kusa da shi bacin tasan halin da yake ciki kuma ta share shi, da kansa ya sha rubuta mata abinda ke damun sa game da rashin Noor amma Anty Zainab bata ta6a tanka shi ba balle ta nuna masa alamun ta san inda Noor take, while tsawon lokacin tana nan tare da ita.

Washe gari Saif ya sake dawowa gidan Ummah dan sosai yake so su gana da Noor su fahimci juna.

Da Ummah suka gaisa dake harabar gidan tana 'yan aikace aikacen ta nan take tambayar sa jikin yayan nasa, tace taji da jimawa ance ya koma bakin aikin sa.

Saif Amsa ta yayi da fa'din" Erh Ummah ya koma amma yanzun haka ma yana gida jikin har yanzu babu da'di.."
Subhanallah..kai Allah dai ya sauwaka.."
Ameen Ummah"
Tace" A ini ban ma sani ba".
" Erh ai cikin kwanakin nan aka kawo shi shiyasa ba kowa ya sani ba.."
" Allah sarki..."

Ummah ta fa'di tana duban Hudah dake tsaye bakin 'kofa tana sauraran hirar ta su...kawar da kai tayi tamkar bata ga Ummah na kallon ta ba.

Iso ta yiwa Saif zuwa 'dakin nan ya cire takalman sa ya shiga.

Tana daga gefe jikin ta wata duguwar riga ce mai kyan gaske ta yane kanta da mayafin rigar, yayin da Saif ke zaune shima daga can gefe guda suna fuskantar juna.

Gaisuwa suka sake yi me 'dauke da kewar juna..." Yah Me jiki fa?"
Ta tambaya tana sunkuyar da idanu.

Sai da ya furzar da numfashi kafin yace" Jiki Alhamdulillahi da sau'ki...i thought zaki zo da safe ai ki duba shi shiyasa ma banzo da wuri ba.."
" Murmushi tayi tace da shi" Erh wallahi nayi niyyan zuwa kuma sai wani uzuri ya ri'ke ni..".
" Ke de kice baki damu da shi ba yanzu dan ba mijin ki bane shiyasa".
" Haba dai ya zaka ce haka kuma Saif? mutum ai mutum ne...balle jinin.Ammi kasan bazan ta6a wula'kantawa ba."

Kai ya girgiza tare da fa'din
" Kar ki wani yaudare ni da wannan kalmar dan sam bazan yadda da ke ba, alamun ki kwata-kwata basu nuna cewa kin damu da jinyar sa ba, ganki fa kyau ma kika yi abinki hadda 'kiba kamar ba me karatu ba..."

'Yar dariya tayi sannan tace " Hala so kake ka ganni na 'kwanjame na zama 'kashi ko?"
Ta karashe maganar tana murmushi.

Girgiza kai yayi yace ba nufi na kenan ba Noor...kawai wani sa'in ina mamaki ne, a dalilin ki fa Yaya kamar zai rasa ransa, wallahi tun rabuwar ku bai sake yin 1 week mai kyau cikin natsuwa ba, kullum shine a gadon asbiti kamar wani mai fama da ciwuka 'dari ta ya bazan tausaya masa ba...kowa ya kasa fahimtar sa hadda kema kika share sa da Ammi ka'dai kike waya itama kuma ta hana kowa damar da zai gana da ke...ban ta6a sanin ana rabuwa irin wannan ba sai akan ki Noor...wallahi koma miye Yayah ya miki zuwa yanzun ya kamata ace kun tausaya masa ke da su Ammi, ku duba halin da yake ciki fa, laifin sa tsakanin sa da mahalacci ne amma duk kun juya masa baya, nasan kema be kyauta miki ba amma Noor me yasa bazaki kalli abin matsayin 'kalubalen dake cikin rayuwar auren ki ba? kina da tabbacin ko wani daban kika aura zaki rayu babu wasu 'kalubalen ne?
Ba ina yi miki magana matsayin 'dan uwan Mu'een ka'dai bane Noor ina miki magana ne matsayin 'dan uwan ku gaba 'daya, dan Allah ki zauna kiyi tunani da kanki ki san abinda ya dace da ke, Allah ma kansa idan bawa yayi masa laifi ya kuma tuba tuba ta gaskiya Allah yana yafe mai ya kuma karrama shi balle mu 'yan Adam da dukkan mu ma muka kasance masu laifi, ki yafe masa dan Allah koma bazaki komawa auren sa ba Noor ki dubi girman Allah kije ki duba shi..? kar ki kasance mai son kanki wacce bata damu da damuwar wanin ta ba...rayuwa ko wani 6angare ha'kuri ake da ita balle shima Yayan na tabbata ko giyar wake yake ko wani sa'a bazai yadda ya sake maimata abinda ya wuce ba..dan Allah ki nutsu kiyi tunani kinji...?"

Kallon Saif take yi ta kasa fa'din komai gaba 'daya ya sanyatar mata da jiki...shi kam da gama fa'din hakan sai ya mi'ke tsaye bai jira jin ko kalma daga bakin ba cuz maganganun sa basu bu'katar amsa ko 'daya, tsaye ya mi'ke yana jin babu da'di cikin ransa.

Hanyar fita ya nufa yana fa'din " Ni na wuce sai anjima ko ince watarana..."
Bata tanka shi ba sai itama ta mi'ke tsaye tana duban bayan sa da raunannun idanun ta wanda tuni har sun fara tara ruwa...yana shirin 'daga labile ta 'kira sunan shi da sanyin muryar ta da baya ta6a canzawa.

Waigowa yayi ya dube ta take sai ta kawar da kanta gefe sannan a hankali tace..." Bayan Maghrib kazo ka kaini in duba shi...".
Cike da jin da'di yayi murmushi gami da jinjina mata kansa kafin ya 'karasa fita.

Ko bayan fitan sa ma zama tayi kawai ta 'kure wuri guda da idanu tunanin da zatayi takamamme ma kwata-kwata ta rasa shi, haka kawai take jin ta wata iri zuciyar ta duk ta dagule, abubuwa da da dama ke mata yawo cikin brain 'din ta amma ta rasa wanda ya kamata ta cafka.

Ana idar da sallar maghrib kuwa Saif yayi parking 'kofar gidan su, zuciyar sa wasai yake jin ta.

Da yake ta riga ta sanar da Ummah batun zuwa duba Mu'een in ya sanya tun da wuri Ummah ta uzzura mata ta gama shiryawa tana idar da Sallah kuwa sai gashi yazo da jin sallamar sa ta 'dauko mayafin ta fito suka wa Ummah sallama suka fita.

Ko cikin motar bata fa'din komai Saif ne ka'dai ke janta da hira..amma a ta'kaice take amsa shi, yanzun zuciyar ta bugawa take yi sosai tamkar wanda bata ta6a ganin sa bane a rayuwar ta sai a wannan lokacin.

Ko da suka isa gidan ma sai da ta zauna wurin su Ammi suka gaisa sannan ita da Saif suk shiga wurin Alhaji Baba nan ma suka gaishe da shi yake tambayar ta yaushe ne zata 'kare makarantar tace da shi" wata uku ya rage".
Cike da jin da'di yace" to Allah ya taimaka ya kuma bada sa'a 'ya ta."
Da " Ameen" ta amsa shi tana mai yin 'kasa da kanta.

Daga wurin sa sai suka wuce 6angaren Yah Deen...zuciyar ta har harbawa, duban 6angaren take yi kamar bata ta6a rayuwa a wurin ba, yanzu komai ya canza an canza sabo da ya ci 'kaniyar wanda ta sani a kyau.

Saif ne ya fara shiga bedroom 'din nasa, wanda ko sallamar da yayi ma bai amsa shi ba, gaban gadon yaje ya tsaya yayi masa sannu ya amsa shi ma be yi ba illah kansa da ya girgiza masa haka ya fito yana jin tsananin tausayin sa a zuciyar sa, sosai yake jinjinawa halin rayuwa, yau ga Yah Deen mai cike da Izzar nan mai kwarjini da haiba, mai nuna isa da tsananin jin kai amma yau gashi maganar da zai furta da bakin sa ma wahala take bashi..Allah kenan Sarki gwanin sarrafa al'amura a duk yadda ya so.

Ganin Saif ya fito ne ya sanya ta saurin fa'din" Bacci yake ko?"
" A a idanun sa biyu..ki shiga ina zuwa ya aike ni ne yanzun zan dawo".
Ya bata amsa yana mai nufar 'kofan da zata fitar da shi daga 6angaren.
Chapter 200 · 0% Book details